Sashe 12
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a gidan Hamma, wato kuka, shine ya dawo mata yanzu domin tasan tayi kuskure. Siddiqah sai ta kifa kai a saman tebur din daya raba tsakaninsu ta fara rera masa kuka babu gaira babu dalili, wani irin kuka na zallar shagwaba da ya nuna kuruciyarta a fili, kukan wanda yafi kamata a kirashi ‘na borin kunya’, a dalilin ganewa da tayi cewa Hamma Prince ya jita tsaf, a lokacin da take cewa tana jin wani iri a ranta da kasancewar sa ‘Bayerabe’ ga Ummanta mahaifiyarta. Shi kuma gani haka wato ganin guilt yayi mata yawa sai ya saki fuska sosai, daga dan dauretan da yayi, don baya son kukan mace a gabansa taba shi yakeyi sosai, Hamma ya koma magana cikin turanci, da dan murmushin bagararwa a fatar bakinsa, don ya kwantar da hankalinta. “Me akayi miki na kuka? Share hawayenki ki ai bakin alkalami ya riga ya bushe miki, ki shirya zama na har abada da Bayeraben miji, don wani abu muhimmi a al’adar gidanmu babu ‘sakin aure’. In akayi anyi kenan har abada, da so ko babu. Munada kishi mai tsanani akan iyalanmu, kishi irin mai lasting har gaban abada. The Akannis’ sun san ciwon matansu sosai. Bama taba auren mace mu hada irinmu da ita, daga baya mu barta wani ya aura. Ke ko ko bamu hada iri ba wato ko ba’a samu rabo a takani ba in dai mun aureta bama taba sakinta. A takaice sai ince miki Bayeraben mutum yafi bahaushe/bafullatani kishi da rukon aure da kyau. A wurin bahaushe ne kawai zaki ga ana saki da sake-saken aure anyhow. Nima biyayya na yiwa Dade na karbeki a gidannan as a Fulani girl, but I never planned it. Duk da ni bani da preference na matar aure daga kowacce kabila. But honestly what Hausa/fulanis are doing to Yoruba tribe is extremely bad. Islamically (a musulunce) mun san cewa Ubangiji yace “Inna akramakum indallahi Atqakum”, above all kuma kalmar shahada ta riga tayi binding us together. Then why the disgust? Idan aka duba ta fuskar kishin kasa ma, ya kamata a daina kabilanci gabadaya tsakanin kabilun Najeriya. Mu yarda cewa mu din duka WA-ZO-BIA ne. Idan muka yarda muka karbi hakan zamu zauna lafiya cikin girmama darajar kabilar juna". A cikin muryarsa akwai maturity na yawan shekaru, akwai amo (tone) mai nuna sanin ciwon kai, sannan at the same time a cikin muryar Prince din akwai lallashi, sabida kukan data soma yasa yaji tausayinta sosai. Domin ya fahimci kalar nata kabilancin kamar nature dinta ne, tanada kabilanci sosai da ya kasa boyuwa a ranta. “Ai kuwa in baki yimin shiru haka ba, ni kuma daga yau zan fara yi miki magana da Yarbanci kullum, har sai kin kware kin fini iyawa". Dan murmushi ya subucewa Siddiqa tasa bayan hannu ta share hawayen, taji dadin yadda bai dauki abin da zafi ba shi kamar Fatima. Kodayake dama hankalin namiji irin Hamma dana yarinya mace kamar Princess Fatima ai ba daya bane. Suna haka hankalinsa ya rabu biyu sakamakon ana ta kiransa a waya ya kasa dauka sabida Siddiqah taki daina matsar ido, mai kiran kuma bai fasa kira ba, da kyar ya daga wayar ya amsa sai yaga ashe Aunty Murjanatu-Taiwonsa ce. “Kehinde wai da gaske ne?” Abinda Aunty Taiwo ta fara tambayarsa kenan. Ya ce. “Menene fa?”. “Fatima ta gayamin su Dade sun turo maka yarinyar nan har Argentina?”. Yace “Exactly, gata nan ma a zaune a gefe na”. Taiwo kamar ta kundumo masa ashar shida wadda yace take kusa dashi din, sai ta tuna Dade da kansa aka ce ya tura ta, karewa ma shi yaje yasa ta a jirgin Argentina ta tafi ga Prince din. Taiwo ta rasa me ya samu iyayensu akan yarinyar nan. Duk girman Dade ace shi da kansa yaje ya saka ta a jirgi. Taiwo tayi shiru kamar zata yi kuka, can kuma tace. “Kehinde kuma ka yarda ta zauna a gidanka? Harda wani gata a gefenka, to uwar me take maka a gefen naka, wannan bakauyar yarinya haka? Kehinde kada kace min zaka iya kwanciyar aure da kucakar yarinyar nan?” Dariya sosai da kunya maganar Taiwo ta baiwa Prince Abdulrasheed. To in bai yarda ya karbeta a gidansa ba yaya zaiyi da ita? Bayan saida ta taso ma aka gaya masa ba shawarar sa ko amincewarsa aka nema ba? Prince yace da Taiwo “wace irin Magana kike haka? A matsayin Dade da Nenne garemu, kin ga ya kamata in sakota a jirgin da ya kawota ne in maido musu ita? Kigayamin tsakanin Dade da Nenne waye abokin sa'in'sa na?” Taiwo ta kasa magana na ‘yan dakikai, don ta san Kehinde ya fita gaskiya, amma in itace zata iya yin bore ta maidata din, saidai suyi hakuri su bi ra’ayinta, Kehinde yanada gudun zuciyar Dade da Nenne fiyeda kima shiyasa iyayen nasu ke samun damar takura masa. Ita da yake sun san halinta ba irin nasa bane wa yake shiga rayuwarta ko ace lallai ga abinda zata yi har a nemi tursasata alhalin tana cikin shekaru in her forties? Tsoron da take daya ne da zaman yarinyar nan kusa dashi a gida daya, tasan maza basu da hakuri akan sex, balle Kehinde da ya kusan fita shekarun kuruciya ba aure babu sabon Allah ta wannan fannin, tana da yaqinin cewa Kehinde baya neman mata a waje, duk yadda suke binsa kuwa as a celebrity, Taiwo tana cikin fargabar kada tsautsayi yasa Kehinde ya hada jiki da yarinyar bisa rashin kauda kai da matsuwa da rashin sanin darajar kai akan sex irinna maza, yaje haka kawai su yi masa surkullensu na Fulanin kauye da basu waye basu san komai ba sai kwadayi, don bazata yi jimilla a fulanin ba, su wadannan wato (Siddiqa da iyayenta) irinna kauye take kallon su, haka kawai taje a mallake mata dan uwa, don dai bata tashi taga bangaren su Nenne na surkulle ba, gashi kuma dai ance itama yarinyar daga Gombe ta fito. Kafin ayi haka Taiwo taji wani mikakken tsaki ya kwace daga bakinta, tace. “Kabi a sannu dai, wannan yarinyar kwatakwata ba ajinka bace Kehinde, class matters a lot in marriage, know how to relate with her don gaskiya da sake”. Ta kuma kashe wayarta cikin kunan rai. Kamar ita aka yiwa auren dolen, auren zubar da class ta bakinta. Yadda Prince ya dauki al’amarin da sauki, ba haka twin dinshi Taiwo ta daukeshi ba, gani kawai take an cutar da Kehinde dinta. Yau ba don tana tsoron iyayensu ba, ko kuwa da ace ba su suka auro masa Siddiqah da kansu ba, sai ta raba aurennan ko ta halin kaka. Dariya sosai Taiwo ta baiwa Prince da daukar dumar magaji da nishinta. Ya tambayi kansa dama ashe aure yanada class ne? Shi bai taba sanin haka ba. A saninsa Sarakuna har bayinsu da ‘ya’yan bayinsu suna aura suyi (sa-dakoki) dasu su haifi ‘ya’ya kuma tare dasu. Eh toh, ita Taiwo tana nufin yarinyar irin ‘ya’yan malam Shehu ce, tunda kuwa yaji ance yariyar ba ‘yar sarauta bace, ba kuma ‘yar masu arziki ba, irin wadanda ya kamata ya aura a matsayinsa na Prince of the Ilorin Emirate, amma a saninsa duk ba wannan ne ya hanashi aure tuntuni ba shi, tunda kuwa ta kowanne bangare tafi Haseenah da yayiwa hakikanin SO na soyayya akan radin kansa cikar martaba, asali, da kyakkywar nasaba. Ko babu komai ita duk sanda aka ga dama za'a je aga iyaye da danginta, koda basu da komai ya tabbata sunada asali, tunda har Nenne da kanta ta ga dacewar auro masa ita saboda kwadayin wata nagarta data gani a tareda mahaifiyarta. A kwana shidda kadai da zuwan Aisha tsarin kitchen da sitting room din Prince ya canza, komai ta maida shi yadda tafison ya kasance. Aisha ta canzawa kanta da kanta rayuwa a gidan Prince Abdulrasheed Kehinde. Kullum zaka sameta cikin tsafta da wanka da shiga mai kyau kuma ta mutunci. Taga cewa zaman me zata yi in bata motsa jikinta? Koda take son cikowa bata son irin kibar Fatima. Ta soma koyawa kanta gyaran sitting room din da kitchennette din, da kawar da duk abinda suka ci abinci ta wanke ta goge ta kife. Sannan ta fara sanyawa gidan turaren wuta masu tsananin dadin kamshi da Nenne ta hado mata. Ba'a jima ba ta gane yadda ake amfani da daukacin electronic appliances na gidan su dish washer, kunna dispenser, washing machine don wanke kayan ta data yi amfani dasu, ta hanyar karanta manuals dinsu. Cikin kwana na bakwai da zuwanta Aisha ta fahimci da yawan abubuwan amfanin gidan, ba tareda an koya mata ba, ta fara goge kauyancin data zo dashi kaso hamsin cikin dari, sai dan abinda ba’a rasa ba. Idan Aisha tayi girki ta kan tambayeshi idan ya fito ko zai ci? Sai yace yayi order. Don Prince ganin Aisha yake bazata iya wani girki da zai iya ci ba har guda nawa take? Siddiqah bata wai damu ba, sai ta dafa iya na cikinta ta kwashe a warmer tayi shigewarta daki da abinta. Prince ya zo Argentina ne domin ya huta, don haka zuwan Siddiqah na bagatatan dinnan baya ciki abubuwan da ya tsara a hutunnan nasa, don haka satin siddiqah biyu kenan amma abubuwa sunki yi masa normal, na farko ji yake tamkar a kansa take zaune tsabar ya kasa sabawa da zaman matar aure da motsinta a cikin gidansa. Duk da ita Siddiqah ba abinda ya dameta da Prince a cikin gidan, harkar gabanta kawai take yi tsakanin kitchen da falo da dakinta, sannan ta riga ta kirkirarwa kanta abubuwa na debe kewa da zasu lallasheta cikin wayar da Prince ya bata, social media plarforms ta sauke iri iri ba wanda bata shiga ta ga me duniya ke ciki, bayan girke girke da take yi wa kanta don ta burge kanta da kanta kullum. Yo ta burge kanta mana, sanin da tayi Prince bazai ci ba, musamman ganin komai na girkin available kuma a wadace yasa take dafa duk abinda ranta ya kwanta dashi. Daga baya idan ta girka ta kan ajiye bisa dining din da yake zama don cin abinci, ganin cewa da kudinsa ake yo cefanen koda bazai ci ba hakkinta ne ta bashi, musamman lokutan data ganshi a gida,