← Book details Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dai ta shige mata, sai ko shekara ta gaba. Prince yace yana mikewa tsaye, hannunwansa biyu zube cikin aljihu, “ina fatan gobe da safe zan samu breakfast daga hannun Ayshah? Tunda Kiki ta tafi kika daina bani, bayan kwana biyu kun shagwabani da kyawawan girke-girken nan naku”. Ya fada yana kokarin saka idanunsa cikin na Aisha, ita kuma tana kokarin sunkuyar da kai ga barin kallonsa. Prince ya kai bakin kofa yana cewa “Good night Ayshah!”. Amma kuma ya kasa ficewa daga dakin gabadaya, rabin jikinsa har lokacin yana cikin dakin. Wani bakon yanayi yana ziyartarsa. Da kyar da dakiya da jan kafa da karfafa giyar mulkinsa kada ta gudu ta barshi, da maintaining class dinsa kada ya bada kansa da yawa gaban little Aisha, Prince ya samu ya fidda gangar jikinsa data makale a dakin, amma har washegari zuciyarsa na reto tsakanin dakinsa zuwa na Aisha. Ji yake kamar ya dawo ya kwana a dakin tareda ita. A washegari kuma ya samu waya daga Ilorin cewa, Emir babu lafiya, ko fada baya iya fitowa, yau kwana uku yana kwance saidai a kwantas a tayar. Bai yi niyyar zuwa gida nan kusa ba, ko sake yin tafiya cikin hutunsa, amma sanin kowa ne sha’ani in ya hada da Kakansa Emir daban yake a gare shi, balle magana ake ta lafiyar Kakansa Maimartaba Sarki, ba zai iya kara wasu kwanaki bai je ya ganshi ba, a take Prince ya soma neman jirgi mafi kusa domin tafiya Ilorin. Ya tuna Siddiqah, yaya zai yi da ita idan ya tafi? Wancan lokacin da Kiki, wannan kuma babu. A karshe ya ga gara ta zauna ita kadai din maimakon ya dauke ta yanzu zuwa Ilorin, ya yi wuri ma ta je gida nan kusa, gara ma tun yanzu Aishah ta koyi zama ita kadai, don kuwa tafiye-tafiyensa ba masu karewa ba ne. Banda sauyukan dake faruwa dashi a ‘yan kwanakinnan a kanta, wato yanzu da ya fara sabawa da ita, ya kuma fara fuskantar dadin mu’amalar da yarinyar keda shi, da ba zai damu don ya tafi ya barta ita kadai cikin gidannan ba. Zuwa yanzu Prince da kansa ya fara tantama a kan cikar lafiyarsa, don duk da tabbacin da yake da shi na cewa Siddiqa matarsa ce, bai taba jin darsuwar wani abu game da ita a ransa ba da ya danganci ‘sexual urge’. Ya dai fara jinta a ransa, ta manne a zuciyarsa. Watakila kuma ko don ya riga da ya saba da yadda yake rayuwarsa ne tuntuni daga shi sai shi, sai ibadar addininsa, sai lafiyar Dawakansa sai kuma zuwa Polo tournament sai aikinsa na ‘Qatar Petroleum Refinery?’. Bai gaya wa Siddiqah maganar tafiyarsa Ilorin ba sai bayan ya gama duk wani shiri yayi (booking flight) dinsa na tafiyar, wato ana i-gobe zai tashi zuwa Ilorin. Siddiqah tana kitchennett tana tana dauraye kofin Mug din data sha tea, ta ji motsin Prince ya shigo inda take. Kai tsaye firij ya nufa, ya bude ya dauki gorar ruwa ya rufe. Ta gama wankin kofin tana kife shi a wurinsa taji motsinsa dab da gefenta. Siddiqa ta rusuna tana gaishe shi da irin gaisuwarsu ta ce, “Ekaaro Uncle” (wato ina kwana)”. Wannan Uncle da Siddiqah ke lanqaya masa ba ya son jin shi, har gara masa Hamma Abdul din da take kiransa dashi da fari kafin zuwan Kiki. A kan me za ta dinga ce masa Uncle sai ka ce wata Kiki? Uncle din nan da ta ke ce masa na sawa ya ji kansa tsoho sosai a kanta sosai. Amma wannan ba shi ne abin da ya kawo shi yanzu ba da yayi korafi, ya zo ne ya gaya mata batun tafiyarshi duba Emir gobe. Tun shekaranjiya rabon shi da ganin Siddiqah. Jiyan da shekaranjiyan duk bai karya kumallo a gidan ba, ya wuni ne a ‘Cathedral of Polo’, shi ya sa bai ga gilmawarta ba, don ko babu komai koda bazata saki jiki dashi yadda yakeso ba yanzu, yana son ganin gilmawarta a kitchen don dai ya tabbatar da lafiyarta. Murya a tausashe ya ce, “Siddiqah, in baki ganni ba ba kya nemana cikin gidannan ko? In ma mutuwa nayi cikin daki ko bani da lafiya duk ba damuwarki bane ba ko Ayshah?”. Kiran sunan nata da ya yi har sau biyu yasa ta bashi hankalinta, don yau ne karo na biyu da Prince ya ambaci sunanta. Ya kara matsowa dab da ita, ita kuma ta dan ja baya. Ya ce, "daina ja da baya ba rike ki zan yi ba Pretty, so nake na gaya miki zan je Ilorin, zan dubo jikin Kakana. Ba na fatan in wuce kwanaki bakwai ban dawo ba, ko akwai abubuwan da ki ke bukata?” Siddiqah kamar ta ce masa za ta bi shi, to amma ita ma tasan ya yi wuri su Nenne su ganta yanzu, duk da cewa ba abin da ke hada su cikin gidan ta san akwai mutum, idan yana nan. Don haka ta samu kanta da rashin jin dadin zancen tafiyarsa, haka ta daure ta ce, “Bana bukatar komai Uncle, ka saya mana komai, ina maka addu’a Allah ya kiyaye hanya ya bawa Emir lafiya, ina duba shi da jiki, in ka karasa wajen su Nenne, ina gaishe su bakidaya, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”. Prince ya ji kamar ya riko hannayenta ya sumbata, ganin damuwa karara a kyakkyawar bafullatar fuskarta. Ashe haka mutum yake ji idan iyalinsa sun masa addu’a? A zuciyarta kuwa hudubar Kiki ke ta mata aiki, na ta daina yarda yana tafiya yana barinta gadin gidan gona, to amma kwarjinin Hamma da girmansa da ta ke gani cikin idanunta ya sa kowanne hukunci ya yi ba ta da ja a kai, musamman a kan zuwansa Ilorin dinnan itama ta san ya yi wuri a ce ta bi shi yanzu. Ta kalle shi a raunane, shi ma kallonta din yake yi da wani sabon yanayi cikin idanun Hamma Abdulrasheed Prince, ya zuba dukkan hannayensa cikin aljihun wandonshi ya juya ya bar kitchen din, yana kokarin maida wani abu da ke neman fita daga bakinsa, wato kalmar ‘I will miss you’ da yake ganin bata dace ya furtawa Aisha ita ba. Amma tabbas zai yi kewar tata, gashi yana son ya zauna tare da Kakansa a wannan lokacin ya kula da shi da kansa. Prince ya tashi a washegarin ranar litinin Siddiqah ta tashi da azumin tadauwa’I a bakinta, wajejen karfe sha daya na rana ta kammala shiryawa ta fito zuwa falo. Ta kunna TV da taimakon remote tana kunnawa din kuma tashar Polo ta ‘PoloLine TV’ ce ta kama, ga dukkan alamu ita ce tashar da ya fi kalla. Ta tarar ana gudanar da wasan tseren Doki. Ta sha jin Nenne na ce mata Hamma yana polo, bata taba ganinsa a profession din ba sai yau, gashinan tsaf ya fito cikin kayansa na polo. A lokacin ana gudanar da wasan ‘Concacap World Polo Championship’. Kasancewar Helmet din kansa budaddiya ce ya bata damar gane fuskarshi sosai cikin mahaya dawakan. Dokin da yake kai wani farin kosasshen doki ne mai fatsi-fatsi, wanda a halin yanzu Prince baya wasan Polo da shi, tun wancan lokacin da suka fadi tare shi da dokin nasa. Siddiqah aka gyara zama ana kallon duk wani motsi na Prince Abdulrasheed Kehinde . Gudu yake da doki cikin kwarewa da iyawa, kamar zai yi fiffike ya tashi sama. “Wannan shi ne ake kira Polo kenan!” Inji Siddiqah. Kuma a koyaushe ta kalli wasan da aka nuno zata ga cewa kusan Prince shi ne jagaban wasan, wato shi ne a sahun gaba na wadanda ke neman isa goal. Abin ya burge Siddiqa matuka don kuwa a wannan daren kusan kwana ta yi tana mafarkin Prince Abdulrasheed a kan doki, yana mata murmushi da helmelt dinsa mai ban sha'awa a a kansa. Shi kuma Hamma tunda ya sauka a Ilorin bai samu sukunin da zai tuna kowa da komai bama don jikin Emir ya yi tsanani, ko wayarsa bai iya ya bude ba. A washegarin ranar ne Aisha ta fara fitowa ainahin kwaryar ‘Ranch house’ din, sabida kadaici daya dameta, kallo sosai Siddiqah take na dabbobi kala-kala masu daraja, harda wadanda ko a talabijin bata taba ganin irinsu ba. Tana tafe a sannu itace har wurin stable din dawakai. Daga ganin farin doki mai fatsi-fatsi “Saheeb” Siddiqah ta gane shi saboda irin kebewa da killacewar da aka yi masa. Wato an ware shi daga ragowar. Ba wanda ya isa ya je inda yake ba tare da Saheeb ya harbe shi ba, daga Prince sai Pareto. Amma daga nesa Pareto ya hango wani abin mamaki, wato Siddiqah ta isa har gaban Saheeb bai harbe ta ba. The beautiful royal horse “Saheeb”, duk ya fi sauran dawakan girma da mulmulallen jiki mai kyau. Ga tsafta ta kama jikinsa saboda kulawar Pareto. Farcensa kansa tsaf-tsaf yake, sannan yana zaune cikin korran ciyayi masu taushi da tsabta. Nan Siddiqah ta shashance har lokacin sallar azahar tare da doki Saheeb a stable dinsa. Pareto sai komawa ya yi da baya don ya ga tana jin dadin zaman wajen, sauran ma’aikatan gidan gona kuwa kowa yana bisa aikinsa babu wanda ya ba ta hankalinsa. Sai ya zamana daga ranar kullum da safe sai Siddiqah ta je stable din Saheeb, har dokin na Prince ya fara gane ta. Da ya ga tahowarta zai fara haniniya yana daga kafafu sama irin yadda yake yi idan ya ga Prince. Ba da sanin kowa ba cikin kwanaki hudu kacal da tafiyar Prince Ilorin Aisha da Saheeb suka yi developing good bond. Har wajen shanun Prince ta ke shiga inda ake tatsa (milking) mai kula da shanun yana mata bayanin madarar sayarwa kamfanonin sarrafa madara suke yi. Pareto ya sha mamakin sabon da ya ga ya shiga tsakanin Siddiqag da Saheeb cikin dan lokaci. Sosai abin ya burge shi. A rashin abin yi Siddiqah ta mayar da Ranch din dawakan wajen shakatawarta da debe kewa da shan iskarta. Wani zubin kuma ta tsaya kallon dramarsu shi da Pareto. Daga irin dramar da ake bugawa tsakanin Saheeb da Breeder din nasa Pareto Siddiqa ta ji doki Saheeb ya kara shiga ranta. Koyaushe ta zo gun Saheeb sukan gaisa da Pareto ta zauna a kujera a
Chapter 23 · 0% Book details