Sashe 5
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tasa daraja (a tunaninta). Kabilarta wato (Hausa/Fulani) babu ya ita a kabilun Najeriya wannan kadai idan ta tuna shi yake bata karfin gwiwa. Kenan ethnocentrism dinta har yanzu yana nan, bazai taba barin zuciya da kwakwalwar Siddiqah ba har abada wato perception dinta na (alfaharin kabila). Tana cikin passengers masu tafiyar dare, da suka tashi zuwa babban birnin (Beunos Aires) din Argentina, kai tsaye tun daga Lagos, tafiya ce suke yi mikakka ba tareda transit (dakatawa a wata madakata ba). Lokacin da jirgin su ya sauka a ‘Aeropuerto Ezeiza’, wato filin jirgin (Buenos Aires), saida kowa ya gama ficewa amma still har lokacin Siddiqah tana zaune a mazauninta kamar an kafe ta, ta rasa inda zata tsoma zuciyarta da rayuwarta taji daidai. Har saida ma’aikatan jirgin suka ankarar da ita cewa kowa ya fita ya barta. Sannan ne ta mike ta saba Jakarta, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta dinga jan kafa, jaye take da trollies dinta guda biyu da basu cika girma ba. Aisha sanye take da ruwan makubar Abayat da mayafinta kirar Taiwan, mai adon manyan stones da suka maida rigar mai dan nauyi, ba tareda Siddiqah ta san ina zata dosa ba kawai ta tasa kai a gabas take tafiya. Ita tasan ba wata shaida da take da ita da Hamma zai ganeta, kamar yadda Dade yake zaton itama zata iya gane shi, bata tsammanin ko kamannin fuskarta Prince ya sani. Kodayake Dade yace wai hotonta zai tura masa na jikin pasfo ko yaya dai? Itama kuma bazata iya tuna kamanninsa ba, don kallon shifcin gizo tayi masa a asibitin Lagoon lokacin da aka kwantar da Nenne, abunda zata iya tunawa game dashi guda daya ne zuwa biyu; na farko turarren tabon sallahr dake saman goshinsa, wanda ya ciza sosai ya nuna cewa Sajidi ne (mai yawan sujjadah). Na biyu kuma ingarman jikin sa murdadde da tsayayyun kafadunsa, wadannan ko ya juya baya ne ta gansu zata ganeshi dasu, don ba duk maza Allah yayiwa baiwar halittar da yayima Hamma ba. Ta cigaba da wuce mutane tana tafiya a ba tare da ta san ina zata dosa ba. Don haka ba jimawa Siddiqa taji wani marayan kuka ya zo mata, ba don ta rasa Uwa ko Uba ba, amma jin kanta take yau a marainiyar karfi da yaji, mara gatan kowa. Tana ta kokarin hadiye kukan da hawayen, tana gayawa kanta Allah na nan, kuma shi zai zama gatanta a nan inda bata da kowa. Hannayenta hagu da dama jaye da jakunkunanta ta wuce cikin terminal. Tana tafe idanu a rufe duk hawaye ya jika fuskarta, ba tareda ta san ina take jefa kafa ba saboda rudanin zuciya da kwakwalwa, Siddiqah tafiya kawai take kanta tsaye har ta kan kusa bige jikin mutanen dake wucewa ba tare ta kula ba, sabida idanunta sun rufe ruf! Da hawaye, sai ji tayi gab! Tayi wani uban karo da mutumin dake tahowa direct gabanta. Kawai sai ta samu kanta da dagowa a hankali, da bude ido jikakkun idanunta da suka kankance don kuka ta dubi mutumin, bata san sanda ta saki marikin jakunkunan hannunta kasa ba. Don kafin taga komai ta hango tabon sujjadar dake saman goshinsa, kafin ta sauko da rinannun idanunta akan faffadan kirjinsa wanda shine ya bashi suffar da za’a kira shi da INGARMA… A yawan hirar Kiki akan Kawunta, ta kan ce mata wai mazan duniya aji-aji ne su, a kamanni na halitta da kasaita, amma cikinsu da wuya a samu irin Uncle dinta…. Kiki tace “Uncle dinta zatinsa da kyawun surarsa ya zarta yadda duk zata misalta mata su ta gane baiwarsa mai yawa ce, ta dauka Kikin koda Ubannata kadai take yi a wancan lokacin, don ita bata ga komai da zata iya noticing har ta karar a tare dashi ba, a dan ganin data yi masa. Amma yau ta ga zahirin maganar Kiki-Ruqayyat, saboda ta yi masa kallo ne sak na rahma da salama, bana cikin halin taraddadi ba (ba irin wanda tayi masa a ganinta na farko dashi a asibiti ba). Ga cikar zati da kamala irin na jinin sarauta tsantsa da Allah ya yi masa, sannan kwarjinin fuskarsa a bayyane yake duk da a hade ta ke tamkar hadarin da ya nausa yayi gabas, sun nuna cikakken basarakensa, bayeraben usuli mai surki da ruwan jikin fulanin Gombe, wanda shine ya hadu ya maida shi tamkar ruwa biyun kasar Habasha, wato kamar dan kasar bakar fata ta Ethiopia, wannan kadai da kallon kyarr da ido da yake mata ne yasa ta gane cewa ba kowa bane a gabanta; HAMMA PRINCE ne…… Bata bukatar sai wani ya fada mata cewa ya ganeta, ko sai ya gabatar da kansa cewa shi dinne kafin ta yarda ta bishi. Shima kuma bai ce komai ba, sai kawai ya sunkuya yana daukar jakunkunan da ta saki a kasa …. Kafin Prince ya dago daga sunkuyon da yayi don daukar jakunkunanta, Aisha Siddiqah taji mararta ta cika taf! Da wani fitsarin razana da ke shirin balle mata daga yanzu zuwa kowanne lokaci, saboda tsabar kidima hade da rudewar da ta sameta lokacin da Prince ya dago manyan maganansa ya dubeta suka hada ido. Hamma ya wara manyan idanunsa a kanta, kallon da yake mata kamar yana son karanto dalilin wannan bewilderment din da ya gani a tare da ita. Ga hawaye na babu gaira babu dalili dake ta tsere a fuskarta wani na korar wani, Aisha ko damuwa bata yi data sharesu, ga jama’ar dake wucewa suna kallonta. Prince ya dan juya hagunsa da damansa a sace, kamar yana son ganin kota jawo masa hankalin mutane da wannan kukan nata, a dauka ko bata son binsa ne, ko batan hanya tayi. Sa’arsa daya sai yaga ba wanda ya basu hankalinsa wucewa kawai ake yi hagu da dama ba tareda an kula da ita da koke-kokenta ba. A cikin jikakkun idanunta kadai ya karanci cewa ta ganeshi, domin bayan rudewar ganinsa daya mamaye idanunta har da kallon sani dana bakunta a gareshi, da kuma kallon rashin sanin kalmar data dace ta furta masa mai nuna cewa ta gane shi din. Don duk wata kalma data kama a kan halshenta don furta masa, sai taga bata yi daidai ta furta masa itaba, har gara ma tayi shiru ta bishi da ido. Sai kawai taga ya juya dauke da jakukunan nata a hannunsa yayi gaba abinsa, ya kasa furta kalmar "biyoni" ko "follow me" don bai san yaren data ke ji sosai ba, tsakanin hausa da fillanci ko ingilishi, ya san dai Nenne tace daga Gombe ta ke, balle yayi mata tsammanin yarbanci. Kalarta da shigar jikinta da komai nata yafi nuna na ‘yan garinsu Nenne din, wato typical 'yan matan arewacin Najeriya. Aisha ta kasa cira kafa tabi bayan Hamma Prince tunda dai bai mata umarnin hakan ba, kada ta bishi ya zama ta zaqe, ita kuma a rayuwarta ta tsani zaqewa, kawai taga ya dau jakunkunanta ne yayi gaba. Ba tareda yace mata komai ba. Har sai da ya dan yi nisa ne ya ankara da cewa ashe bata biyoshi ba. A sannu ya juyo don ya tabbatar, sai ya ganta kuwa tsaye standstill a inda ya barta, bata ko cira kafa ba. Prince ya dakata yana tambayar kansa wannan wace irin yarinya ce kamar ‘yar goye Nenne ta kawo masa? Domin koda ya juyo gani yayi tana ta share ido bata taho ba din, tana jiran sai ya gaya mata me ya kamata tayi ita bata san facial expression ba? To idan kuma bai iya yaren data ke ji bafa, don shi ba wai ya kware da Hausa bane. Bayan dama cikin haushin an masa katsalandan da zuwanta gareshi ya wuni, alhalin yazo Argentina ne yin dogon hutun karshen shekara don ya samu ya huta, ya rage stress, yanzu ga rainon 'yar goye an kawo masa, yo raino mana! Don wannan a shekaru ai bata fice sa’ar Kikinsa ba. Budewar ido kawai Kiki ta fi ta. Ko Kiki fama yake da ita har gobe akan shirmen kuruciya, balle wannan mai ruwan ‘yan fulanin cikin garin Gombe. Dawowa yayi inda take tsaye yana kokarin hadiye fushinsa, don yasa a ransa cewa ba laifinta bane zuwan da tayi, umarnin iyayensa ta bi. Prince ya dan hade giran saman idonsa ya cure su, yace. “Are you waiting for my command? If yes, then follow me!”. (Kina jiran umarnina ne? In haka ne ki biyo ni toh). Aisha ba wai bata jin turanci bane ko yaya, tanada turancinta ba laifi tunda ‘yar makaranta ce, amma wannan karon kwakwalwarta ta kasa fassara turancin nasa, domin sak yake furta shi kamar na turawan yamma, wato accent din bata saba jin irinsa ba ko yaya ne dai ita dai bata gane me yace ba. Shikuma Prince sai bai kara cewa komai ba ya juya ya cigaba da tafiya, jinin mulkin ya motsa, yana cewa a ransa in bata biyoshi wannan karon ba baisan ya zaiyi da ita ba kuma. Don kuwa ya tabbata ta ji shi saidai in shakiyanci ne kuma abin nata, tunda ya tabbata ba kurma bace ai ya santa a zuwan da yayi Lagos tana gidansu. Tafiya yake a nitse akan marbles din wajen da jakunkunanta, bai kara waiwayota ba, ya barta a wurin tana zare jikakken idanunta ta rasa me zata yi takamaimai, don rudewa tasa ta kasa fassarawa kanta umarninsa ba rashin jin turanci ba. Kafin ta baiwa kanta shawarar kawai ta bi shi, shi ya fiye mata alkhairi fiyeda cigaba da tsayuwa a wajennan. Idan ya bace mata cikin mutanen da batasan kowa ba sai shi, tabbas zata gayawa aya zakinta. Sai kawai ta cira kafa da hanzari ta bi bayan Prince, harda hadawa da dan gudu-gudu, domin ya fara yi mata nisa. Prince sai jin motsin gudun-gudunta da sassarfarta yayi a bayansa, ya dan tsaya har ta cimmasa, kafin su jera tare zuwa parking lot na filin jirgin, yana gaya mata ta tafi a sannu akan santsin wurin, kada ya kada ita. Motar da Prince yake budewa Siddiqah ta bi da kallo domin da fari ta dauka ba mota bace wani abun ne daban, domin gani tayi murfin ya dage sama da kansa, wato kofar motar ta daga sama automatically, sannan samanta a yaye