Sashe 21
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni haushi dake, amma na tabbata Uncle ya fara kamuwa da sonki. Ko daga kishinki muraran da ya soma nunawa ba tare da ya san yana yi bama. Tunda nake Uncle bai taba yi min jan ido ba sai yau a kanki. Wanda ke nuna zuciyarsa ta fara sauyawa positively a kanki”. Aisha bata ce komai ba, rokon Kiki ta ke a kan ta kara kwanaki, Kiki na cewa lokacin komawa makarantarta ya yi. Zadai ta Kara kwana daya saboda gobe akwai wani surprise data keson yiwa Uncle AK. Tsabar fadan sa na yau yasa ya manta (tomorrow is his 43rd birthday). Washegari tunda safe Kiki ta soma shirye shiryenta a boye na shiryawa Hamma Candle Lit Dinner. Na farko ta bada order din birthday cake mai kyau da tsada ta kuma sa Chef a kusa dasu su shirya mata dinner na abinci da abin sha na alfarma, na iya mutum biyu zuwa uku, tun kafin karfe bakwai na magariba aka kawo mata komai. Ta sa Pareto ya kai mata karamin dining table na farar roba da kujerunsa zagaye dashi a wani bangare na korran ciyayi dake cikin Ranch din. Aisha na fitowa daga wanka Kiki ta zabo mata wata gown ta wani jan material da ratsin baki, budaddiya sosai daga kasa amma ta kama kirjinta sosai, cikin kayanta da tazo dasu daga Lagos, tace tayiwa Allah su zata saka yanzu, sannan ta zaunar da ita bisa stool din mudubi tanaso zata yi mata kwalliya. Kiki ta fara zizara mata sassanyar make-up, wato irin light make-up dinnan ba mai daukar ido ba. A isha dai tana kallon ikon Allah don Kiki bata gaya mata ko me take shiryawa ba. A can kuma Pareto ya gama shirya table din da kwalliya ta ban kaye bisa umarnin uwardakinsa Kiki-Ruqayyat. Ya shirya abincin da ya karbo order, ya aje katon cake a tsakiyar table din. A jikin cake din Kiki tasa an rubuta “Happy 43rd Birthday Uncle AK”. Kiki ta fara zuwa wajen ta tabbatar komai yayi yadda take so ya kuma tafi yadda ta tsara. Sai tasa Pareto ya kashe mata wutar harabar wajen gabadaya. Sai wata 'yar kankanuwar ‘dim light’ ya bari. Ta dawo daki tana cewa Aisha “Pretty biyo ni muje cikin Ranch, amma don Alah kada ki tambayeni komai”. “Kiki ho!” In ji Aisha, da alama dramomin Kiki ba masu karewa bane. Haka tabi bayan Kiki zuwa cikin gidan gonar. Kiki ta kama hannun Aisha ta zaunar da ita a kujera ta kuma karbe wayar Aisha ta rike don ma kada Aisha ta haska wajen da wayartata. Komawa tayi neman Uncle cikin gidan har dakinsa, acan ta samoshi idar da sallahr isha’insa kenan yaji knocking din Kiki. Saida ya kwashi mintuna kafin ya taso ya bude don yasan bazai wuce ita din ce ba. Casual wears dinsa ne a jikinsa kamar kullum wato shirt da dogon wandona Mark Jacobs. Harda farin karamin cazbaha a hannunsa. Yana bude kofar Kiki na kamo hannunsa. “Uncle don Allah biyo ni, amma kada ka tambayeni komai”. Inda sabo Prince ya saba da rigimar Kiki da dramarta kala-kala, haka ya yarda ya bi bayan Kiki zuwa bangaren data keso suje na gidan. Bai kuma tambayeta din ba har shima ta zaunar dashi a kusa da Aisha yana cewa, "me ya faru aka kashe wutar wajen nan haka? Ina Pareto?" Kiki tasa lighter tana kukkunna candles din cake din, sannan ta kunna fitilar wajen haske mai ni’ima ya wadata ya gauraye wajen. Kiki na dariya tana clapping hannayenta. Ta soma wakar. “Happy birthday Uncle AK!”. Sai lokacin duk suka fahimci me take nufi. Da abinda ta shirya. Wato sai lokacin ma Hamma ya tuna yaune zagayowar ranar haihuwarsa shekaru 43 a duniya. Excitement dinsa ya kasa boyuwa, domin ko ba komai Kiki ta bashi babban surprise din da ya sashi dariya, diyar nan tashi Ruqayyat tana matukar kaunarshi, ko bai haifi da ba a duniya ya godewaTaiwo data haifa masa Kiki. Kiki tana kula tana kuma sane da komai nasa, don shi ya manta ma. Duk da ba wai yana celebrating ranar haihuwarsa bane a baya a kowacce shekara, amma idan ranar ta zagayo, Nenne da Dade su kan kirashi suyi masa fatan alkhairi da addu’a, shikuma ya kan kara ninka sadaqarsa ga gidan marayu, a kowacce ranar birthday dinsa. To yau wayarsa tana kashe, domin ya baiwa kwakwalwarsa hutu. Ta cikin hasken candle lit din ya juya yana duban Aisha dake gefensa, sai ya ga ta koma masa tamkar furen fulawa don kyau. Kamar an kara wanketa an canza mata launin fata, sakamakon wannan sassanyar kwalliya mai tsari da Kiki tayi mata, serene make-up din ya amsheta sosai. At long last! Yau shi Abdulrasheed ya cika shekaru arba’in da uku tare da matar aure by his side (a gefensa). Auren da bai taba zaton yiwuwarsa gareshi a gidan duniya ba. Tabbas aure lokaci ne dashi ga kowanne dan adam, komin tsarin daka yi masa, idan lokacinsa ya zo daga Allah ko mutum yanaso ko baya so zai tabba dashi. Prince ya sakarwa Aisha kyakkyawan murmushinsa, wanda bai san lokacin da ya subuto masa daga zuciya zuwa fatar bakinsa ba, ganin itama kallon shi take yi yau da dukkan admiration na mace ga miji cikin idanunta. Ta kasa ce masa “happy birthday” din ita sabida kunya, amma a cikin zuciyarta ta fada ta kuma maimaita, har ta kara da cewa, “Allah ya karawa rayuwarka albarka the Great Prince of the Ilorin Emirate”. Kiki ta hau hure candles din dake bisa kan cake tana cewa. “Bari toh in huresu, a madadinka Uncle!”. Ta hure candles din duka. Tace sai Uncle AK ya yanka cake dinnan nasa da kansa. Nan ma dai Hamma dariya ce ta kama shi, da girmansa gemai-gemai za’a ce ya yanka cake! Yace Aisha ta yanka a madadinsa. “Lets the wife represents the husband”. Kunya ce sosai ta kama Aisha irin wadda bata taba ji ta Hamma Prince ba, a yau da ya dangantata da matarsa. A karshe sai Aisha da Kiki ne suka hada hannu suka yanka cake din tare. Aisha ta zaftaro katoto tayi bakin Kiki dashi, sai Kiki tayi kwana da hannun Aisha zuwa bakin Hamma Abdulrasheed (Prince). Ta kuma yi maza ta daukesu hoto. Aisha tayi dumu-dumu da bakin Hamma da cake. Daga Aisha har Prince kunya ce ta kamasu da wannan hoton da Kiki ta dauka don idonsa yana kan Aisha, babu irin wannan shaquwa da sakewar a tsakaninsu kafin zuwan Kiki. Don haka Kiki ta zama rahma ga auren ma’auratan nan. Kiki ta cigaba da waka a wurin tana musu hotuna tana wakar. “Happy Birthday Uncle Abdulrasheed Kehinde!”. Daga nan ta bubbude foil paper da aka rurrufe abincin dashi, ta zauna itama tana fuskantarsu suka soma cin dinner din tare. Suna ci suna hira gwani ban sha’awa, Kiki nata basu dariya da hirarrakinta na wauta, suna gamawa Prince ya kunna wayarsa ya zagayo hannunsa ta gaban Siddiqah, yace da Aisha, “dan matso nan Siddiqah muyi selfie nida ke, cikin wayata saboda tarihi!”. Ba karamar kunya ce ta lullube Aisha ba, lokacin da Hamma ya kashe kyawawan fuskokinsu shi da Aisha da flash din dalleliyar camarar wayarsa Idan da Kiki zata yi duba da duk abubuwan da ke faruwa yau, da wadanda suka faru tun zuwanta, sai ta godewa Allah, domin kuwa ta samu ladan wadannan ma’auratan. Zuwanta yayi riba. Tayi silar abubuwa na farin ciki da yawa a gare su, da cigaba cikin irin zaman da ta tarar suna yi. Don kafin zuwanta wani irin zama suke yi kamar na ‘jahiliyya period’. Don yafi gaban a kira shi na doya da manja don baza’a kira shi zaman aure ba. don kuwa alhakin juna suke dauka. Zuwan Kiki ya haska gidan. Ya hurawa zukatan ma’auratan ruhi. Sai mu ce madallah da Kiki-Ruqayyat, madallah da zuwanta gidan a wannan lokacin. Kiki zamewa tayi ta bar su a wurin da cewa zata je ta dawo. Ganin Prince duk hankalinsa na kan Aisha. Yau Prince da Aisha ne zaune dab da juna, har ya samu kansa da janta da hira. “Siddiqah bani labarinki mana? Tunda kikazo kin kunshe min baki, bansan kina walwala haka ba sai bayan kawarki tazo ko?” Aisha ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran ‘yan yatsunta tace “Uncle me kake son sani a kaina?” A takaice Prince ya ce da ita. “Komai! Tun daga labarin iyayenki, ‘yan gidanku, samarinki, kawayenki da makarantar ku. Yadda kika tsinci kanki a auren Bayerabe alhalin kina bafullatana mai kin yarbawa da sauransu. Kin ga ni na tabbata kinsan komai a kaina a gidanmu, amma ni har yau bansan da wa nake zaune ba, banda cewa ina tare da matar aure na kawai”. Aisha ta rufe fuska da zara-zaran yatsunta tana cewa cikin murmushi. “Hamma Abdul, banida labari ne ni, gidan mu ba kanne ba yayye, nikadai ce ‘ya a gidanmu. Nice yar kaina nice kanwar kaina. Samari kuma bana sauraron kowa sai Ishaq Nafada. Kawayena na makaranta kuwa sunada yawa, babbar aminiyata a cikinsu Amintako ce, sai Ramatu da Ruma, don ni dinnan da kake ganina shiru-shiru a gidan ka ‘gang leader’ ce dake shugabantar fitinannun yara a makaranta. Sunan makarantarmu FGC Billiri Gombe. Yadda nayi na samu kaina da auren bayeraben miji bazan iya cewa ba, illah ince wata addu’a ce ta Ummanka ta filin Arfah, ta fado a kaina ni Siddiqah, kamar yadda Ummata ta bani labari nima”. Prince ya soma dariya kamar bashi ba, bai zaci Aisha haka take da baki ba, yace “wato Nenne addu’a tayi akaina, sai ta fado a kanki ko Aishahh?” Ta sake rufe fuska tana dariya ta ce “exactly, sosai kuwa, wata irin zazzafar addu’a tayi a inda Allah baya juyarda addu’a, don Ummana ta ce da ta ji Nenne tana addu’ar nan a lokacin, a take a zuciyarta tace inama zata ganshi ko waye shi ta bashi PETEL dinta! Sai Allah yayi ta tsara abubuwan daki-daki yadda ya ga dama, suka yi ta faruwa subsequently (wani na bin wani). A rayuwata ban taba jin wani abu mai kyau game da kabilar Yarbawa ba, sai bayan da Nenne ta dauke ni zuwa gidanku a birnin Ikko. A nan ne Yarbawa iri-iri suka goge min hadda, tun daga kan ma’aikata da masu girkin