Sashe 6
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yake. (Sport Car, Toyota Supra) duk iyaka dauriyar Siddiqah da dakewarta na kada ta nuna kauyanci ta kasa karfafawa kanta gwiwar ta shiga motar nan, ba don komai ba sai don tsoron ganin cewa samanta a bude yake gabadaya. Idan iska ta daukota tayi wurgi da ita akan titi Ummanta kadai za'a yiwa asara. Shi a gatan da yake dashi a gobe za'a auro masa gomanta. Goman Siddiqah harda kwarori. Don haka shiga wannan motar ai tsautsayi ne da ganganci a ganin Siddiqah. Sai ta kara jin tausayin kanta na wannan rayuwar bakon wuri, da kasaitaccen basaraken bayeraben mijinta data samu kanta rana daya. Siddiqah ta kasa tsayar da hawayen ta sam. Prince bai lura da halin da take ciki ba ya sanya jakunkunan nata a bayan motar, sannan ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna, har zuwa lokacin tana tsaye kikam. Shi tunda yake bai taba sanya mace a gidan gaban mota ya tuka ta ba inka cire Fatima ko Firdausi ko Kiki. Amma haka ya daure ya mika hannu ya budewa Aisha kofar barinta ta hanyar danna wani madanni a jikin allon motar, yana lallashin kansa da kansa, yana gaya ma kansa yarinyar nan taci albarkar DADE dinsa da NENNE. Iyayen da bai hada alfarmar su data kowa. A komai ma zata cigaba da cin albarkacinsu, tunda sun zabeta gareshi sama da kowacce mace, har gobe sun kasa gane uzurinsa na bashi da gurbin adana kowacce ‘ya mace a ransa da cikin rayuwarsa. Amma Siddiqa ta ki shiga don kauyanci da rashin sabo na shiga gaban mota daga ita sai katon namiji, gani take motar babu sirri, kowa yana ganinsu, sannan yadda take babu nauyin nan iska zata iya daukota ta jefota waje in aka fara tafiya. Prince ya fara zama bored da kauyancin Aisha don kiri-kiri kana iya karantar tsoron motar take ji a kwayar idonta, bayan kasancewarta cikin takurar zuciya har a kan fuskarta, har ila yau, kana iya ganin kauyancinta baro-baro. Shi bai ga dalilin kukanta ba ko sau daya, tunda da yardarta akayi komai, koda yake ya kamata yayi ma kukan nata uzuri, rabuwa da kasar haihuwarka rana daya da iyayenka bakidaya da danginka zuwa inda baka san kowa ba baka taba zuwa ba ba wasa bane. Amma in banda haka ai ba’ayi wa bakunta kuka in ma bakunta ce. A ganin Prince shi ya dace ya dora hannuwa aka yayi ta rafsa ihu yau ba ita ba, shi da aka turo masa mace bagatatan, macen da ya riga ya rufe babinta aka sako yau cikin gidansa da rayuwarsa. Watakila kuma tana kuka ne kan an aura mata tsoho kamar shi, yarinyarta da ita danya sharaf, gata nan santaleliya son kowa kin wanda bai samu ba. Amma ya kamata ta duba cewa bai je inda take da kansa yace yana sonta ba, balle ta yi kukan auren dole dashi. Inda wanda zata tuhuma akan hakan to nata iyayen ne da suka yarjewa nasa iyayen, ba tareda sun ko gan shi ko a hoto ba balle a zahiri. Ya tuna abinda ya faru jiya. Yana zaman zaman sa Dade ya kira shi a waya. Inda cikin raha Dade din yace. “Kehinde, me kake yi daga yau zuwa gobe ne?” “Dade it's month end ai ka sani (kuma ya kama Asabar din karshen wata), so nafi zama a gida a duk rana irin wannan, Pareto yayimin lissafin abubuwan da suka kare a gidan, da abincin dabbobi da sauran bukatunsu, muna checking lafiyarsu kuma, sannan in biya ma'aikata albashinsu na wata, sannan muna yin lissafin abincin Horses da zamu ajiye na tsayin wata guda. So I will be busy the whole day, daga yau zuwa goben har in samu in kammala da duk wannan”. Cikin tsokana Dade yace "kawai kace min “The Prince and his ranch activities dai, to Allah ya taimaka, inaso yanzu ka ajiye komai ka sa a shiryawa Aisha-Siddiqah dakin da zaka sauketa, jirginsu ya taso zuwa Argentina yanzu daga Lagos, zasu sauka a (Ezieza International Airport Bueunos Aires) nan da awanni ashirin da biyu”. Saida ya baiwa kwakwalwarsa aiki na wucin gadi yana son gane me Dade ke magana akai, kuma wacece Aisha Siddiqa din, har saida ya ga cewa ya gaza wajen ganewar ya tambaya cikin girmamawa mai hade da mamaki. “Dade wacece Siddiqah kuma wajen wa zata zo?” Sai Dade ya juya harshe zuwa (native language) yana masa bayani don dai Prince ya yarda cewa seriously yake magana dashi yanzu. Cikin harshen Yarbanci yace ma Prince din. "Na gaji da jiran zuwanka na sako maka matarka Siddiqah a jirgi, ta taho, so nake ku rayu tare rayuwar sunnah a gidanka da duk inda zaka shiga, daga nan har karewar numfashi. Tunda naga alama baka san zuru ba, da irin sacrifice dinda iyayenta masu dattaku suka yi mana, suka baka aurenta ba tareda sun ko gan ka ba". Sai Prince ya tsaya sakatoto! Da waya a hannu, jin Dade ya kashe wayarsa ba tareda ya bashi damar kara yi masa tambaya ko neman karin bayani ba. Ya koma ya zauna a hankali bisa kujerar da ya mike daga kai lokacin da zai amsa kiran mahaifinsa. Prince bayan gama sauraron Dade sai ya kasa cigaba da aikin da yake yi, zufa sai yanko masa take yi daga goshi, ya koma ya zauna yayi tagumi da hannu bibbiyu, yana ji kamar yayi ihu. Domin wannan shine (hukunci mafi tsanani da tsauri da iyayensa suka taba yi masa). To amma ya kamata yaga laifinsu? Sun bi duk ta hanyar data dace don ya kawo mata da kansa, don yayi aure ya cika mutum a lokacin da ya dace, sun yi fadan sunyi lallashin, sunyi barazanar aura masa guda hudu daga danginsa, Nenne har kuka tayi a gabansa, akan zarge-zarge marassa dadi da ake masa, Emir ne kawai yake yi masa uzuri, har kauracewa Baffanninsa yayi akan suna so yayi aure don radin kansa da zabin kansa, ya cika tarbiyyar gidansu abu ya gagara, don haka kada yaga laifin kowa a kan zabin da suka yi masa yanzu wanda shine hukunci na karshe da ya biyo baya, na biyo shi da yarinyar har inda yake finally. Kamata yayi ya ga laifin kansa, bana yarinya ba, wadda aka katsewa rayuwar kuruciya itama aka turo ta aure inda bata da kowa ba da son ranta ba. Ko kusa bai kamata yaga laifin iyayensa ba. Sun bi duk hanyar daya kamata su bi donbashi hakkinsa a addinance da al'adance. Yarinya ita akafi cuta ma, kasancewar da kuruciyarta an hadata da tsohon tuzuru kamar sa. Nenne ta gaya masa maganar auren tunda jimawa amma ya gudu ba tareda ya damu ba, in zai iya tunawa daga lokacin bata kara yi masa zancen yarinyar ba, ta koma normal rayuwarta ita da shi. Ashe ba hakura suka yi ba dungu suka yi masa. Yau dai ga matar nan an biyo shi da ita hara Ajantina, ba kwabonsa babu darinsa, a wurinsu karshen gata sun gama yi masa, a wurinsa karshen katsalandan da takurawa an yi masa, in ba Dade din ba wa ya isa yayi masa wannan karan tsayen a rayuwa? Ko Akannis tara bazasu fara ba. Kai ko Emir ba zai masa hakan ba. Shi tunda ya koma Qatar bayan rashin lafiyar Nenne, lokaci-lokaci maganar yarinyar na fado masa, yakan tuna wai yanzu an masa aure, sai kace wani a zamanin da. Tabbas za'a gaji da ajiyar matar nan kuwa, a karshe a maidawa iyayenta don ba zai taba dauka ba. Sai kuma ya tuno kamannin yarinyar, wanda ko bai rike hakikanin kamannin ta a ransa ba, hakika ya rike kalar idanunta masu kama dana kwan zabo, wadanda suka nuna tsantsar damuwar rashin lafiyar Nenne cikinsu da wani irin innocence. Ya dade a zaune kafin ya yanke shawarar takamaimai me ya kamata yayi? Gashi an ce ta rigata taho. Ya bi bayan kiran Dade ne yace ta koma sai ya shirya ko yace bai shirya iya zama da iyali ba har yanzun a kara masa lokaci? Har zuwa sanda yake jin ya shirya? Ya riga ya saba da rayuwarsa ta kadaici ayyukan cigabansa, and his horses always makes him busy, baya maraba da duk wani abu da zai canza masa tsarin rayuwar nan da ya riga ya saba da ita. Kamar ya kira Taiwo, ya gaya mata abinda Dade ya kira shi yanzu ya gaya masa in yaso ya nemi shawararta kan abinda ya kamata yayi, don gaskiya Dade ya shammaceshi, sai kuma ya fasa kiran nata. Dalilin tunawa da yayi cewa Taiwo tun rana ta farko da tazo Lagos taga yarinyar ta yi masa korafin yarinyar da Nenne ta aura masa bata yi mata ba, because they are so much different from the grounds of age and social class. Bai taba tanka mata ba don shi bai dauki zancen ma da muhimmanci ba. So yanzu ya kirata yace an sako yarinyar a jirgi ta taho masa, bai san abinda Taiwo zata ce ba, banda ta sa shi ya maida ita. Ita dama ta saba rikici da iyayensu in sun yi hukuncin da baiyi mata daidai ba. Wata zuciyar tace to ko Kiki zai dauko daga Ilorin su zauna tare? Nan ma yaga hakan bazai yiwu ba musamman kasancewar Kiki na makaranta kuma watarana itama aure zata yi. Shi kam! Yayi duk iyaka tunaninsa bai ga ta yadda zai iya zama gida daya da mace da sunan partner ba. Bayan tsanar su da yayi, har gobe duk kallo iri daya yake yi musu, koda da wace niyyar alkhairi suka dumfaro shi. Uwarsa da ‘yan uwan sa na ciki daya kadai ya kebance daga cikisu. Gidan nasa babban ‘Ranch House’ ne hade da gidan gona (farm house), tsarin ginin flat ne aka gina a can tsakiyar ranch din. A cikin wannan flat din akayi babban (sitting room) dake kunshe da dakunan gidan, falon gidan (is kitchennette) wato hade yake da budadden kitchen na zamani da ake yayi yanzu da dining area. A cikin wannnan babban (sitting room) din ne masterbedroom din Prince Abdulrasheed yake. Sai wasu (two extra two bedrooms) din, kowanne da bathroom a cikinsa, wanda asali ya tanadi dakunan ne domin ‘ya uwansa mata da haularsa dake zuwa hutu wajensa akai-akai. Daga harabar wajen flat din nan ne Ranch