Sashe 22
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan, na fahimci cewa Yoruba kabila ce mai matukar daraja a Nigeria, kamar Hausa/Fulani. Dana zo Argentina na tadda Prince of the Ilorin Emirate, sai ya karasa wanke duk wata negative hadda dake cikin kaina akan Yarbawa, don na gane cewa Prince din Bayerabene na gaske, mai alfahari da kabilarsa. Da bakinsa ma ya fada min; he’s a proud Yoruba man. Don haka ni yanzu duk inda naga Yarbawa tsakanina dasu girmamawa ce da karya hula, sanadin kaunata dasu”. Prince ya lumshe ido cikin murmushi, kowacce kalma dake fita daga bakianaata tana masa dadi, ya budesu a kanta yana cewa. “Aisha frank kenan! Naji wannan, na kuma taya yarbawa bakidayansu murna da kika cire musu kabilanci daga dictionary dinki. Bayan wannan zan so in san wane irin so kike yiwa Ishaq? Ina nufin yaya kike jinsa a ranki kafin auren ki da Bayerabe da yanzu bayan auren?” Aisha ta hau ‘yar dariya tana cewa. “Uncle me yasa ka tambayeni wannan? Babu kyau binciken abinda yaa riga ya wuce”. Kai tsaye Hamma ya saka idonsa cikin na Aisha ya dan budesu cikin nata. yace “because I am extremely jealous of him!”. Aisha ta sunkuyar da kai tana jin wani irin dadi a zuciyarta, amma tana so ta baiwa Prince wannan amsar koda zai ji babu dadi. Ba don ta goge kishin da yace yana yi akan Ishaq ba, sai don ita ‘yar keke da keke ce tun asalinta, bata da rufa-rufa (frank). “Ina son shi sabida he is caring. Kullum muke tare sai ya gaya min how much he cares and loves me. Baya gajiya da gayamin muhimmancina cikin rayuwarsa duk da kankantar shekaruna. Na taso na san shi a matsayin fiancé dina shikadai na saba da shi na kuma shaku da shi. Rana daya aka ce an bada ni ga waninsa kuma Bayerabe da ban ko taba gani ba. Ka gayamin in kaine ni yaya zaka yi? Ai dole ka yi dan protest ko? Musamman daka gane cewa shi wannan da aka mallakaka gareshi din bai ma san da kai ba, bai damu da kai ba, bai san kana existing ba, kuma baka cikin lissafinsa a rayuwa”. Hawaye suka digo mata tace “it’s not easy, ina gaya maka Hamma, it’s not easy, don ma na roki Allah juriyane, da danganar karbar rayuwa a duk yadda ta riske ni”. Amma bayan nan ina dadewa ban tuna Ishaq ba, na yarda “he is my past, I don’t have a present”. Ba don komai nace haka ba Uncle sai don kasancewar Uncle AK da aka aurar dani gareshi rana daya bana cikin lissafinsa. Ya karbeni a gidansa ne kawai kan ba yadda zaiyi da umarnin mahaifinsa”. Hamma yace cikin karfafawa. “Prince Abdulrasheed yanada past mara dadi akan mata, kin zo rayuwarsa a lokacin da ya tsani mata, bashi da sauran hope akansu. Amma duk da haka Prince zai yi kokari ya komar da hannun agogo baya, wato ya yi kokarin manta past dinsa, ya karbeki a gidansa da rayuwarsa a matsayin present dinsa, don radin kansa ba don tursasawar iyayensa ba, hakan zai faru ne only ranar da kika daina yi masa kallon BABANKI!” Da sauri Aisha ta rufe ido da tafukanta cikin jin kunya daidai lokacin da Kiki ke tahowa garesu. Tana karasowa tace “Uncle AK zan dauki Uwata haka, lokacin barcinmu yayi, in ya so ka kawo kayan zance sai in barka zuwa tadi!” Hamma ya zaro ido yace “Kiki, kina maida ni Kakanki koh? Zan yi maganinki aure zan yi miki soon”. Koda suka koma cikin sitting room Aisha da Kiki kallo suka kunna a falon, suna kallon girke-girke a Netflix. Hamma dakinsa ya wuce cikin wani yanayi. Domin maganganun Aisha bakidaya na yau sun zame masa food for thought. Ya kasa barci a daren nan ya samu kansa da kallon selfie dinsu shi na birthday shida Aisha, da tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninsu. A daren yau Prince yayi abinda bai taba yi ba, wato yin rubutu a shafukansa na social media. Domin bayan ya kasa daina kallon selfie din, sai ya budo status dinsa na whatsapp, yayi wani rubutu mai matukar jan hankali da shikadai yasan ma’anar kayansa, a kasan hotonsu shi da Aisha, bayan yayi covering fuskar Aisha, amma gangar jikinta ta fita gaban candle lit cake. “Happenings at 43rd Birthday ….. !!! The wife that is slowly becoming the centre of my universe”. **** **** **** Wani ikon Allah Taiwo ce ta fara ganin status din brothernta. Ta sha mamaki ganin yau Kehinde ya dora status don baya yi sam. Don haka da doki da zaquwa ta bude don taga me Kehinde zai daura? Ta kuwa ci karo da wannan magana da hotonsa shida Aisha, da suka yi matukar daure mata kai. Me Kehinde ke nufi? Ya folawa wannan yarinyar ko yaya ne? Nan take tayi screenshot cike da takaici da tsegumi ta turawa Haseenah. Washegarin ranar Kiki tayi musu sallama ta wuce makaranta bayan Kawun nata ya cikata da duk abinda zata bukata, har ma da wanda yafi karfin bukatunta. Bayan wucewar Kiki Aisha duk ta canza wa rayuwar gidan, dan fitowa falo da take yi duk ta daina. Aisha ta maida kanta daddawar daka, gabadaya walwalar nan da ta ke yi sanda Kiki ta ke nan ta dauke daga fuskarta ta komar da kanta yadda suka saba zama ita da Hamma tun kafin zuwan Kiki. Duk inda miji yake sunansa miji, da soyayya ko babu, to hakan ce ta faru Prince Kehinde, bayan tafiyar Kiki da canzawar yanayin Aisha, duk sai ya ji ya damu. Ya shiga takura da canzawarta da rashin fitowarta falo yadda suka saba. Ko da ma can shi Aisha tausayi ta ke ba shi, balle yanzu daya fara sanin wacece AISHA-SIDDIQAH. Zaman Kiki ya haifar mata da walwala mai yawa, ya fara bankado masa asirin dake kunshe a zuciyar Aisha, ya ga excitement a tare da ita, irin wanda bai taba gani a tare da ita ba, kafin zuwan Kiki. Sai Hamma yaga cewa zai yi kokari ya maye mata gurbin Kiki, wato ya zame mata babban aboki kuma dan uwa, wanda zata iya yin dariya da walwala tare da shi idan har zata yarda da hakan. It’s not easy a rabo ka da iyaye, dangi, kasarka da kowa naka sannan a barka cikin damuwa. Yau kwanan Kiki hudu da wucewa, kuma tun lokacin ganinsa da Aisha sau daya ne tak! Ya zauna a falon har ba adadi domin ya ga gilmawarta ko don ya tabbatar da lafiyarta amma ko kamshinta bai ji ba. Aisha wadda ta koma daddawar daka tun bayan tafiyar Kiki Ruqayyyat, ko kiraye-kirayen waya data ke wuni tana yi da jama’ar gidansu dana gidan Nenne yanzu ta rage. Ta fi yin tilawar Alkur’ani da nafilfili a cikin dakinta, sai ta tabbatar Hamma ya fita ‘Ranch’ ta hanyar hango shi cikin stable din dawakansa ta tagar dakinta take fita kitchen ta dafa taliyar indomie da bakin ruwan tea, tayi maza ta juye a flask ta shige daki shikenan. Dama Kiki ce ta matsa suke cin abinci tare dashi. A rashin Kiki kuwa, sai ta maida musu rayuwarsu ta tun asali irin yadda suka fara ta. Duk iya juriyar Prince da dakewa da jin sarauta, ya kasa yin biris da wannan silence din na Aisha. Da canjin data kawo musu. Because it’s killing him inside. A can dakinta ita kuma a kwanakin nan guda hudu, Aisha babu abin da ta ke yi sai sauraron zuciyarta, tana ‘digesting’ maganganun Kiki na hankalin dana wautar. Tana daukar na hankalin, tana watsar da na shirmen. A ciki Kiki ta ce da ita kada ta kara yarda Hamma ya barta jiran gida. Ta dinga saka su lingeries a cikin gida da sauransu. Kiki ta manta duka wannan ana yi ne a inda akwai soyayya da kaunar juna. Ba ta haufin yau da a ce Ishaq ta aura za ta iya yin fin abubuwan da Kiki ke koyar da ita. Ita ba bagidajiya ba ce irin yadda kowa ke daukanta, ta san duk abin da ya kamata macen kwarai ta yi a dakin aurenta, uzurinta kawai shi ne Prince ba sonta yake ba, ita ma kuma haka, sannan ba ta hango musu wani canji a zamantakewarsu nan kusa ba, domin ita da shi duka danjuma ne da Danjummai. Wato babu wanda ya damu da wani abu wai soyayya, ita a kan Ishaq duk wani tsuntsun soyayyarta ya gama tashi. Tana wannan tunanin mara adadi a zuciyarta ta ji motsin ana knocking kofarta kadan-kadan. Kafin a shiga kwankwasawa sosai, a nitse Aisha ta tashi zaune daga kwanciyar da ta ke, ta isa ga kofar ta bude don ta san babu mai yi mata knocking har kofar dakin barci a gidannan a kuma daidai wannan lokacin da dare ya fara nisa in ba shi Hamma Prince din ba. Aisha ta taso ta bude wa Hamma kofa, ta rabe jikin kofar ta ba shi damar shigowa don alamu sun nuna shigowar yake so zai yi dakin. Sai da ya baza manyan idanunsa yana nazarin tsaftar dakin. Ba laifi Aisha ba ta watsar da shirgi, komai nata neat. Don haka ya zabi sofa-bed guda daya dake dakin ya zauna, kafin ya dago a hankali idanunshi a lumshe ya fuskanci inda take tsaye tana gaisheshi, bai amsa gaisuwar ba yace, “Are you alright? Kwana biyu bana ganin wulgawarki a sitting room, baki ko gaisheni, ina fatan dai lafiya?”. Kan Aisha a sadde ta bada amsa, “Wallahi lafiya kalau Uncle, kawai ina kewar Kiki-Rukayyat ne”. Prince ya yi murmushi ya ce, “Ni kuma da kika daina fitowa kinsan ya nayi kewar ki? Na ga alama jininki ya hadu da na Kiki, ga shi ba ki san ita yarinya ce mai kiriniya da rawar kai ba. Kawancenku ba zai yi daidai ba, considering cewa ke din Uwa ce a gare ta. Ba komai za ki dinga tattaunawa da Kiki ba akaina please, zan kai ki makaranta insha Allah idan nagama hutuna mun koma inda nake aiki a Qatar, domin ki samu abin debe kewa”. Godiya sosai Aisha ta hau yi, tana jin kamar Hamma ya mata bushara da kujerar makkah, kwarai ta ke son komawa makaranta, ta dauka karshen karatunta a rayuwa kenan sakandire, amma ta san wannan shekarar