Sashe 7
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na Dawakansa, suna cikin stable dinsu a jere abin gwanin ban sha’awa. Ko ka samesu sun watsu cikin korran ciyayi a ranch house din suna ci daga garesu, suna kuma sha daga ruwan dake tsiri sama yana sauka kasa (katon swimming na gidan gonar), inda anan ake kiwon fararen Agwagin ruwa, Dove, Babba da jaka, Kangaroos, Jimina, da Gada Mai tsalle, a can karshen gidan kuma wajen kiwon Shanu ne irin na turai masu yawan haihuwa akai-akai inda ake milking danyar Madara. Prince har ila yau yana kiwon tsuntsayen gida irin su kajin gidan gona jajaye, farare da bakaken tantabarun Ingila, Dawisu da Argentinian Parrots (Aku-kuturun Argentina) manya-manya masu magana. Duk a cikin wannan kasaitaccen ranch din. A can karshen gidan gonar ne sassan Pareto da sauran ma’aikatan gidan gonar yake, da babban (store house) na ajiye abincin Horses dana sauran dabbobin. Yana zaune still yanata tunani ya ankara lokaci na tafiya, ya dade a wannan halin na zama shiruuu, ya rasa ta ina zai fara. Cika umarnin mahaifinsa ko bin hukuncin zuciyarsa? Kararrawa ta gaya masa ana magana dashi a kofa, da kyar ya iya mikewa don kafafunsa sun masa nauyi, zuciyar sa ko tayi nauyi sosai, da kyar Prince ya isa ga kofar ya bude. Pareto ya gani tsaye rike da kayan sa da ya wanke ya goge, ya bashi hanya ya wuce ya ajiyesu akan daya daga cikin (three seaters) din (sitting room) din, don a ka'ida Pareto baya shiga (master bedroom) dinsa. Kawai sai Prince ya samu kansa yana ce ma yaron gidan nasa. “Bude daki daya cikin biyunnan ka gyara, ka karbo abincin da nayi order, ka ajiye a dakin, zan kawo baki daga gida Lagos anjima”. A gidan gonar Prince, Prince ruwan zafi kawai yake iya dafawa da kansa, duk abinda zai ci daga ‘African Cuisine Restaurant’ dake kusa da gidansa yake saka order ake kawo masa, kullum sau uku, in har yana Argentina kuma yana gida bai je tournaments ba, to 'El Buen Sabor Africano' su suke bashi abinci na al’adarsa wato (traditional Yoruba food). Pareto ya bi umarnin ubangidansa ya je ya fara gyara dakin wanda dama a gyare yake, sai abinda ba'a rasa ba don baya sati biyu bai gyarashi ba, ko su Fatima sun zo ko basu zo ba yana yawan sharewa ya goge, dama dai Taiwo ce tafi sauka a cikinsa don yafi girma, ko ita ko Nenne. Dayan twin Princesses da Kiki ne ke sauka cikinsa. Pareto Yana feshe dakin da room freshener bayan ya gama mopping, yana yi yana tunain ko su wa Boss zai kawo? Ya san da ba lokacin hutun kannensa bane ba, ko Twin Sis dinshi Mrs Taiwo. Da ya kammala ya fito sai ya samu Prince har lokacin a zaune inda ya barshi da alama yana cikin tunani. Ya kasa yankewa kansa shawarar zuwa Airport din ne don cika umarnin Dade ko a’ah? Saida ya rage bai fi mituna talatin jirgin ya sauka ba ya mike cikin zafin nama ya suri mukullin mota ya fita. Kuma yana isa wajen ya hango yarinyar tana tahowa kanta tsaye, duk da dai Dade ya kara da turo masa hotonta ta waya da ko budewa bai yi ba, yana ganin ta jikin sa ya bashi, zuciyarsa ta amsa, yayinda kwakwalwarsa da idanunsa kuma duk suka shaidata. **** **** **** Aisha nata tunanin shiga motar ne ko yaya zata yi? And the Prince is patiently waiting for her to decide, kamar yasan shawara take yi da zuciyarta tsakanin binsa ko a’ah. A ransa yace baida matsala kan duk abinda ta zaba. Shiga motarsa ko kin shiga zabinta ne, shi dama dan cika umarni ne kawai. Ya mika hannu ya bude mata kofa, wani privilege da bai taba yiwa wata mace ba bayan Nennensa, a iyaka saninsa tun tasowarsa sai dai shi a bude masa. Ya kunna injin motar wanda baya making any noise ko kadan, kasancewarta lafiyayyar motar tsere (Sport Car) ta zamani, sa’annan mai lafiyayyen sabon inji, Siddiqah ta gayawa kanta gaskiya idan Prince ya gaji ya tafi ya barta a wurin nan ina zata je a wurinnan da batasan kowa ba? Inda ko kallo kowa bai ishi kowa ba, kada ma taje Police su kamata a wurin a bisa tuhumar rashin yarda da ita, don gasunan birjik cikin fararen kayansu suna ta shawagin tsaro a filin wurin. Ko me ya bata tsoro? Prince sai gani yayi bakuwarsa tayi kundumbala ta shigo motar da sauri. The way and manner da Siddiqah ta sako kai ta shigo motar ma kamar mai shiga daki ya saka Prince yamutsa fuska, domin ba ta haka ake shiga motar ba. Ya dan kalleta kawai ta gefen ido yana so yace ta rufo kofar, mulkinsa na gaya masa yayi mata banza, ita bata san ya kamata ba? Komai sai an gaya mata zatayi? Shi baya son yawan magana a nature dinsa, don sai ya wuni bai yiwa kowa magana ba in ba SAHEEB ba, ko zai baiwa Pareto da ma’aikatansa umarni ba kullum bane. Amma wannna bakauyar yarinyar ya ga alama a komai tana jira a bata command ne, in kuma an bata din ba kasafai take ganewa ba. Sai kawai ya mika hannu ta gabanta ya rufo kofar da kansa, a hankali ya hau kwalta suka soma tafiya, nanma ya ga bata da niyyar daura belt, haka kawai zata jawo masa attention din road safety. Da wata murya kamar yayi kuka don tausayin kansa, na aikinda Dade ya hadashi dashi Prince yace da ita. “Please, fasten your belt!”. Siddiqah ta dago tana duban Hamma Prince da ‘yar rudewa, cikin alamu na son ya fassara mata, don har ga Allah wannan karon ma bata gane me Hamma yace ba. Don haushin data bashi Prince bai kara maimaitawa ba, sai kawai yasa hannu daya yayinda yake tuki da dayan yana daura mata belt din a bayan kwibinta, saida Aisha ta janye numfashinta sama kadan, sakamakon kakkarfan kamshin masculine turaren Prince “Boss Intense” daya bakunceta. Don da farko bata fahimci me yake kokarin manna mataa kugu ba, wanda hakan ya sata ‘yar karamar kidimewa, don haka har Prince ya gama zura mata, ya cigaba da tukinsa numfashin Siddiqah ya ki komawa daidai yadda yake, sakamakon tsoro da kidimar data shiga kafin ta gane belt ne Hamma ya saka mata. Ko irin kalle-kallennan na bakin hanya na bakunta da bako ke yi in ya zo bakon wuri, banda Aisha-Siddiqah. Titi kawai ta kurawa ido ba abinda yake burgeta duk kyau da kyatuwar birnin. Hankalinta da tsinkayenta duk basa jikinta a yanzu, suna ga irin rayuwar data tunkarota, a kasar Polo ta Ajantina, amma ta san ko babu komai tana da Allah, tana kuma da albarkar iyayenta tareda ita. Kuma Umma da Malam suna sane suka kawo ta don ta rayu da dan Nenne, sabida darajar iyayensa, amma ko me yasa ba ruwan kowa da feelings dinta akansa wane iri ne? Shima din kuma yana sonta ko a'ah? All they care for shine dansu yayi aure da mace mai tarbiyyah yar masu dattaku, ya samu ya cika martabarsa da tasu. Ummanta da Abbanta kuma damuwarsu akan ta samu iyayen miji na kwarai ne, Nenne da Dade kuwa sun hada wannan, burin nata iyayen shine suyi mata aure cikin lokaci, sannan su kaita inda za’a rike musu ita da daraja. A ganin Aisha Siddiqa lamarin is far beyond this only, ya kamata ayi la'akari da zuciyarshi a kanta, ita tata mai sauki ce tunda ta rasa Ishaq, to bata da sauran zabi akan mijin aure. Ishaq kadai takeso. Don haka a rashinsa kowa aka zaba mata sunansa Umma ta gaida Aisha, wato sammakal, don bata da ja akai. Tun Daga kallon data yi masa suka hada ido a filin jirgi bata kara yarda ta dube shi ba balle ta kalli cikin idanunsa masu tsananin kwarjini. Ta kan dai dan saci kallon gefensa yana tukin. Tafiyar mintuna kusan talatin ce ta kawo su gidan Prince tsakiyar garin Buenos Aires (capital of Argentina). Tausayin yarinyar ya dada kamashi ganin ta kifa kai a jikin allon motar tana sauke ajiyar zuciya ita kadai bayan tayi kukan ta gaji. Ya kashe motar yace da ita cikin sassauta sa “mun zo. Ko zaki iya shigowa ciki?” Da sassaukan turanci ya fada. Wannan karon bata isa tace bata gane ba, domin kuwa Prince yayi lowering accent dinsa da voice tone dinsa sosai. Pareto ne ya iso da hanzari ya budewa ubangidansa kofa kafin ya zagayo ya budewa Aisha. Ya umarceshi da ya shigar da jakunkunan ta ciki. Yana fatan kuma ya karbo mata abincin da yace ya karbo mata. "Master abincin tun kafin fitarka na karbo shi, na shirya shi a dakin". Aisha ta fito tana zare kyawawan idanunta a gidan gonar Prince Abdulrasheed (Kehinde). Wani babban ranch house ne wanda tun daga nesa zaka hango daidaikun Dawakai na alfarma farare da jajaye da bakake, sun watsu jefi-jefi suna cin korran grass, wani abun sha'awa da ko a talbijin bata taba gani ba sai yau a zahiri. Prince ya wuce gaba, Aisha ta hadiye kauyancin ta da tsoronta ta bishi a baya zuwa ainahin (sitting room) din dake cikin ‘ranch house’ din. Da suka shigo tsakiyar falon, Prince sai ya maida kofar ya rufe yayi gaba ya barta a wurin. Siddiqah ta cira kai a hankali tana kallon wannan kayataccen muhalli wanda saidai taga kwatankwacinsa a finafinan larabawa dana turawa, shigifa ce ta alfarma mai hade da karamin madafi na zamani da akeyi a cikin falo (kitchennett). Girman falon da fadinsa yasa kujeru kala-kala saiti uku kosassu na musamman yaci, batare da kowacce ta san da zaman ‘yar uwarta ba. Dole tsarin komai na sitting room din Hamma Prince ya burge bako, har dai in wanda ya san kimar muhalli mai daraja ne, ba kamar Aisha-Siddiqah ba, wadda iyakacinta Gombe da Billiri. Sai ko yanzu data dan samu 'yar gogewa a zaman ta na gidansu Prince a Lagos tareda Nenne. Ita kyawun falon da dukiyar da aka zuba a cikinsa firgitata yayi, maimakon ya bata sh’awa, ya kara kidima 'yar nutsuwar da ta fara samu. Tsayawa tayi a tsakiyar falon harde da hannuwa a kirji, tana jiran ya bata umarnin zama, ko ya nuna mata kujerar data dace ta zauna. Ta kwaso gajiya ba