Sashe 1
Aisha Siddiqa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
AISHAH-SIDDIQAH
3
SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga mambobin TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aishatu Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.
(INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
Takorinku
April, 2024
AISHAH - SIDDIQAH 3
A
isha-Siddiqah na cikin farin ciki mai yawa a yau, kasancewar yau ne ta zana paper dinta ta karshe a sakandire lafiya. Kuma ga dukkan alamu mahaifan Abdulrasheed basu yi asarar makudan kudadedn da suka kashewa Aisha ta jona karatunta na sakandire ba a makaranta mai tsada da yaransu ke yi, har yau da Allah yasa ta kammala cikin kudurarsa.
Lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa, ta fara shirye shiryen tafiya, wannan karon tareda Nanin Gombe zasu tafi Hajjin bana, wato mahaifiyarta Hajiya Oummana, don haka za’a dauko Nanin daga Gombe, zuwa Lagos, sai su hadu su tashi ta Lagos State Pilgrims.
Sun yi waya da Haj. Zainab ta gaya mata batun tafiyar tata, nan Umman Siddiqah take gaya mata suma acan Gombe suna shirin tasowa, kuma cikin ikon Allah wannan shekarar ma har da ita Umman, ta kara samun kujera daga ofishin su Malam Yunus. Nenne tayi murna sosai da sake haduwarsu a Saudi, karo na biyu, har take cewa cikin tsokanar Umman.
“Abin Allah sai kiga wata shekarar kuma war haka, saimu sake haduwa a masarautar Ilorin, muyi wankan jegon Petel dinki”.
Dariya Haj Zainab tayi cikin jin kunya, na Nenne tace “to ta share dakin Petel, tayi wake da da shinkafa da salad da yajin maraba, Petel zata zo musu sallama, don itama wajen mijinta zata koma kafin tashin nasu aikin Hajj, tunda ta gama makaranta.
Da wannan Nenne da Umman Siddiqa suka yi sallama cike da kaunar juna.
Haj. Zainab ta gayawa Malam Yunus maganar zuwan Petel ganin gida da sallama, wai zata koma inda mijinta yake zaune. Malam Yunus ba karamin dadin hakan yaji ba, a take ya ce maza Sunusi almajirin dake zama da Umma tun bayan auren Siddiqah, ya gyara dakin Petel ya share ya goge.
Lokacin da za'a taho daukan Nani Ummana sai Nenne ta gayawa Siddiqa ta shirya zasu wuce Gombe tare, ta gaya mata zata kaita ganin gida ta gaida su Ummanta, in yaso ta yi kwana uku, suyi sallama da su Ummanta saboda sunaso zata bi bayan mijinta (Hamma) cikin watannan, wato lokaci yayi da zata tare a gidanta.
Duk da Nenne ta yi mata wannan bayanin na dalilin da zata je sallama gida Gombe, Siddiqah bata damu ba, murnar zuwa ganin gidan ya take fargabar maganar tarewar, wato sawun Giwa ne ya take na Rakumi, ta hau murna da giringidishin shirin tafiya gida baji ba gani, kamar ta sume don dadi.
Yaushe rabonta da Umma da Abbanta? Ji take kamar ta shekara Goma rabonta da gida da iyayenta.
Nenne dai bata yi mata bayanin yadda tarewar tata zata kasance kai tsaye ba, ta barwa Haj. Zainab, don ta san Haj. Zainab zata fita iya lallashinta da convincing dinta ta tafi cikin dadin rai ba tareda ta daga hankalin ta ba.
Kuma tun farko Haj Zainab taso daman a barta ta shirya Siddiqah tun kafin zuwanta Lagos wato tayi mata gyaran aure amma basu bata damar yin hakan ba a lokacin. Nenne tana ganin yanzu in taje gida kome Haj. Zainab takeso sai tayi mata yanzu ne yafi dacewa.
Tsaraba sosai tasa Seun da Firdausi suka hadowa Siddiqah, wanda zata tafi dashi gida, turamen atamfofi da lesika na Ummanta da kannen Babanta mata dake Kumo, da shaddoji da yadikan Maza masu daraja da turare na Babanta da Yayansa madaurin aurenta Baba Barau. Itada Nenne da Firdausi suka taho Gombe ranar Asabar.
Da suka shigo gari kuma tun kafin su tafi masarautar Gombe saida suka fara sauke Siddiqa a gidansu dake Jeka da Fari.
Umman Siddiqah dama ta san da zuwansu, tuni ta shirya musu karba ta girma yadda ta saba yima bakinta na musamman, Umma akwai karrama bako balle suruka irin Haj. Sappah, ta tarbesu da abinci mai tsari da abin sha mai sanyi. Saida su Nenne sukayi kat, sukayi sallah suka huta, suka kuma sha hira sannan suka fara shirin wucewa fadar Gombe.
Umma na tsokanar Princess Firdausi da cewa, "yau dai gata ga Gimbiyar tagwaye kuma auta sannan shalelen Nenne". Princess tayi murmushi tana sadda kai tace “Umma ai tuni Siddiqah ta kwace min wannan fadar”.