← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Gombe kowa ya san masu wadatar zuci ne, masu sana’ar da zasu dogaro da Allah da kuma kansu”. Ran bafillacen ya baci, yana fulatanci yana gamutsawa da Hausa. Umma dai kasa magana ta yi, don ta tsorata sosai da yadda Malam Yunus ya fusata, ya sa Petel a gaban motarsa nan take suka dauki hanyar gidan Baba Barau suka bar Hajiya Zainab ta rasa abinda ke mata dadi. Ba ta so a ce Petel dinta ta zama bazawara, at a very tender age ko a kirata sauta ga wawa, kuma bata so ya zama su Mallam Yunus sun yanke hukunci kawai daga bakin Petel gabanin jiran Dade da Nenne, da shi kansa Abdulrasheed din yace zai zo gobe. Sun samu Baba Barau a gidansa a turakarsa yana cin abinci, ya yi mamakin ganin Aisha. Amma fuskarsu kadai ya kalla ya san ba zuwan ziyara ta yi ba, ba kuma na dadin rai ba. sai ya ture kwanukan abincinsa gefe yana cewa “Indon Legas saukar yaushe?” Wajen zama ya bai wa kaninsa, sannan Aisha ta tsugunna gabansa ta gaida shi, ya ce, “In ce ko lafiya na ga Indo kamar daga sama? Ba ance min kun bar kasar ba zuwa turai?” “Yanzu dai Petel ki fada masa komai da bakinki ya ji”. Aisha ta maimaita wa Baba Barau kalaman Murjanatu kakaf. Da yadda ta tada bori sai ta taho. Baba Barau ya sunkuyar da kai na ‘yan dakikai, kafin ya dago ya ce, “Na ji, kuma sun yi da dan halak. Kin haifu Indo, daya tamkar da dubu ga iyayenta, kuma mun gode da wannan karramawa da kika yi mana. Allah yayi miki albarka tunda arziki, mulki da daular da kika samu kanki ciki rana daya basu sa kin sarayar da mutunci da martabar mu ba. Ni kuma na yi miki alkawarin yadda na hada wannan auren haka zan tsaya in kwato miki martabarki. Taiwo ta ke ko Tuwo, sai ta san ba’a cin zarafin bafillace a kwana lafiya don ko sune Qaruna da Fir’auna don mulki da dukiya kin gama auren dan su”. Ya ce, “Kuma a gidana za ki ci gaba da zama, don Zainaba tsaf kawarta za ta kalallameta ta zugeta su maida ki. Tunda uwarsa da ubansa kadai ke son auren. Shi dinma nataba ganin kafarsa a gidannanya zo gaishemu? Kullum saidai ace baya nan kamar wani tsuntsu. Don Zaynaba kam sanyin halinta bazai bari ta kwato miki ‘yanci ba, kuma kin san kawancennan nasu itada Sappa sai Allah”. Farin-cikin goyon bayan da ta samu kadai daga iyayenta dattawan kwarai ya wanke mata zuciya ta saki numfashi na samun kwanciyar hakali. Ta san da wasu iyayen ne cewa zasuyi zasu maida ta kada sarauta da mulki ta wuce ta kansu. Baba Barau ya sa murya ya kira matarsa Furera, ta shigo ya ce, “Maza Furera share wa Aisha dakin can na kusa da naki, ki kuma kama kaji a yanka ki mata farfesu yanzun nan. In kuma gashi take so sai a kaiwa Ayuba ya gasa mata. Ko me ta ke son ci a yi mata (baba Barau na kiwon kajin gidan gona masu yawan gaske a wani bangare na gidansa)”. Sai bayan fitar Baba Furera ya tambayi Aisha, “bani wayarki kada ma ya kiraki. Shin kina da iddarsa a kanki??” Kunya sosai ta kama Aisha. Ta sunkuyar da kai ta kasa amsawa. Baba Barau ya ce, “Magana nake yi da ke Indo”. Aisha ta girgiza kai a hankali, wato babu iddar Prince akanta. Wayarta kuma tace ai a wurin ta aje masa abarsa. Ba waya a hannunta yanzu. Baba Barau ya kara fusata ninkin ta baya, yayi kuta ya ce, “Allah ne shaidata, ni ban yi la’akari da komai nasu ba na yarda na ba su aurenki, amma in suna ganin akwai wata manufa daga gare mu, ko in hankali bai kwanta ba gara da suka maido ki gabanmu da wurwuri. Amma miji ya jingine mace mai lafiya har watanni tara babu sunna, kuma da sunan aure, sannan suna tare a gida daya ai wannan auren ma da alamar gurbacewarsa. Babu inda zaki koma kin zo gida kenan inyaso su biyo ki da takardarki ni za’ayiwa iya shege da wulakanci?. Idan kuma sun ki, na rantse ko da shari’a sai na raba auren nan. Mu za a wulakanta? Mu ake wa kallon kwadayayyu matsiyata?” Baba Barau har ya fi Malam Yunus daukar zafi. Nan ya tafi ya bar Aisha a gidan Baba Barau yana ta ja wa Furera kunne kan lallai kullum ta kama kaza da zabuwa ta yi wa Aisha farfesunsu da suya ko gashi. Nenne ta kira mahifiyarta ta ta gaya mata Aisha ta taho Gombe, sakamakon abinda Taiwo ta yi mata, da abinda ya biyo baya, wato tahowar Aisha gida. Nenne ta nuna ma Oummana damuwarta sosai kan abinda ya faru a bikin na Princesses dinta, ga jama’a sun gayyato daga ko’ina ba damar ta barsu ta taho, sai an kai amare, shi ne Nani Oummana ta tace ta kwantar da hankalinta su gama bikin twins lafiya. **** **** ****
Chapter 8 · 0% Book details