← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 25

Sashe 5

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana fadin. “Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!”. Hamma yace “I don’t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa? Wannan ai mugunta ne Aisha. Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki”. Aisha tayi wani murmushi kawai ta kalleshi “ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji” ya sake mata kiss a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana murmushi. Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin, shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu’ar arba’in kuma a dauro auren a fadar Ilorin. Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a gidan, kamar ‘ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar wanda za’a bawa sarauta a cikin ‘ya’yan Emir. Idris Akanni y ace a’ah, ko dama Emir ya dade yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha’anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra’ayin sarauta ko kankani, don haka ya barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin. Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu’a arba’in din za’a zarce da bikin nadin sarautar da daurin aure. Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam. “Nenne keda surukar taki daki daya zakuyi sharing ne? Ai ba’a yin haka a gidannan, ta tashi ta koma cikin matan ‘ya’ya, haba Nenne don Allah ki dinga jan ajinki akan yarinyar nan”. Nenne tayi sakatoto tana duban ‘yarta Taiwo kafin ta samu abin cewa Aunty Taiwo tace da wata baiwa dake gefe ta dauko kayan Aisha ta kai dakin da ta sauka. Jin tace a kai dakin da take yasa Nenne tayi shiru bata tanka ba, koba komai zata so a samu shakuwa da fahimta tsakanin Murjantu da Aisha, bata son yadda Taiwo ke treating matar kanin nata. Taiwo tace Aisha ta biyo ta, kamar kada ta mike don ba tun yau ba jikinta ya gama bata Aunty Taiwo bata sonta ko kowa bai gaya mata ba. Amma jin Nenne bata ce a’ah ba, kuma Taiwo dinnan diyar Nenne ne da bata da maraba da Hamma, sannan Maman Kikinta sai kawai ta zari hand bag din ta da mayafinta tabi ta nata dakin. Babban bedroom ne a wani sashe na cikin gidan sarautar, dakuna ne a jere wasu na fuskantar juna duk iri daya, yawanci matan Uncles din Abdulrasheed da matan ‘ya’yansu in suka zo sha’ani duk anan suke sauka, dakin da suka shiga da Aunty Taiwo ya ji kayan alatun rayuwa na gargajiyar sarauta dana zamani, ga iya kwandishin mai ni’ma nata aiki, akwai tafkeken gado da wardrove, Aunty Bola matar wani Cousin dinsu da Aunty Iyabo matar Turaki da Fatima da Firdausi ne a dakin suna hira lokacin da suka shiga dakin. Jikin Aisha a sanyaye matuka don yarbanci kawai kake ji yana tashi a gidan da sauran dakunan, koda suka shigo ma duk ta tsangwami kanta duk da Firdausi na tsokanarta da fulatanci tana cewa duk ta wani takure, tafi son koyaushe gta like da Nenne, tace ta saki jikinta nan duk iyayen Hamma ne sai su kannensa. Fatima ta Harari Firdausi tace da turanci don kowa yaji “in taga dama ta daure jikin don Allah, kinsan bata son shiga cikin yarbawa kada su cinyeta, ba abin raini a wurin yarinyar nan irin Bayerabe. I wonder yadda na jita shiru kamar an aiki bawa garinsu tun isarta gidan Hamma kuma”. Ifedayo ta zaro ido tace “kamar yaya bata son yarbawa? Ewoo! Bata son kabila ta auri dan su, dan ma babban jikan sarkin Ilorin da muke fatan ta zama uwa ga kowa namu watarana?” Aunty Bola tace “ke ko Ifedayo! Ai ‘yammatan hausawa ba don so suke aure ba, kwadayin su ba inda baya kaisu. Balle taji sarauta zam, taji Prince na kasashen turai ai nan ‘yammatan hausawa dana fulani suka fi kauri. Sai an yi auren kiga ba soyayyar da zata dauwamar da farin ciki a cikinsa”. Kamar an yiwa Aunty Taiwo kunni, ko kuwa allura akan gyambon ta, ta dubi Aisha ta kyabe baki, tace “ku bar ganin laifinta, iyayenta ne manyan kwadayayyu da basu san darajar kansu ba balle na abinda suka haifa, amma ba ita ba, tunda ita batama san shi ba ko kafin a auro ta, su da suka dauki wannnan teenager suka aurawa Kehinde wanda a haife ya haifeta sune suka fiddo kwadayinsu da zalamarsu fili, ta yaya zaka aurawa danka wanda baka ko taba gani a zahiri ko a hoto ba? Sai kawai don jin su waye iyayensa. Wai daga haduwar kan hanya aka baiwa Nenne sadaqarta ta aurawa danta saboda an ga mamora a jikinta. Ni tunda nake ban taba jin aure na rashin mutunci irin haka ba, ban taba ganin auren rashin sanin darajar Da irin naki ba, ai a al’adarku ana lefe, ana yiwa amarya kayan hana gori, amma ke ko lefen bana jin an yi miki, ke suturar da zaki saka ma a gidanmu mu muka yi miki, da tsummokara kikazo, ko wanka babu, aka bi aka asirce mana uwa, bata zance sai naki, amma ku duba kuga daga shan jar miyar Ewedu har ta fara washewa, ku kuke kayan daki amma ke haka aka daukoki zikau! Aka kawo mana. Mun miki komai domin mu suturtaki, mai nuna sadaqarki suka baima Nenne ta likawa Kehinde ta karfi da yaji. Kuma shi ba so yake ba, ya fada ya kara bashi da lokacin soyayyah, bazai taba son ki ba saboda ya dade da gama soyayya tun a kuruciyarsa, akwai wadda yayi shekara da shekaru yana so tun samartakarsa har girmansa bai aureta ba. kuma har gobe ita zuciyarsa ke so. Ni nasan Kehinde wallahi, babu kuma wanda zai gaya min waye Kehinde, ko a kafa aka daura masa ke nan gaba kadan zai kwance ya yar. Kawai kun ga arziki da sarauta kun nace, watakila ma kuna tunanin Kehinde zai yi sarauta ne, to in gaya miki gaskiya inma wanan kukewa keda iyayenki to kije ki gaya musu Kehinde bazai yi ba. Da aka aura masa ke aka kawoki guidanmu saida ya jingineki kusan shekara guda, saida su Nenne suka gaji da ajiyarki a daki ne suka tattara ki suka danna masa ganin wankin hula zai kaisu dare. Da zuwanki gidansa na fahimci kun soma juya masa kai, iyayenki nata surkulle ga dukkan alamu, har wani dora ki yayi a status baya ko jin faduwa a ganshi dake a matsayin mata. Nayi rantsuwa ni Taiwo abokiyar tagwaitakarsa, inma asirinku ne ya fara cinsa ko zan daina barci sai na warwareshi da karfin addu’a, in asiri kuke shiga jeji kuna jefa masa mu addu’a muke kwana yi, yadda kuka ganshi haka zaku kyaleshi. Kakan kakanmu Shehu Alimi, ya dade da tofe zuri’ar shi da kul’aquzai, daga duk wani sharri na masu nufin Kehinde da wani surkulle na magauta da irinku makwadaita”. Duk maganar nan Taiwo na yinta ne cikin sassaukan turanci da fulatanci ziryan, don ma Aisha ta fahimta sosai. Siddiqah dai tana zaune banda kallon bakin Taiwo ba abinda take yi. Kirjinta yana harbawa zuciyarta na matsewa. Fuskarta na rinewa daga yellow zuwa jazir. Saida Aunty Taiwo ta gama cin mutuncinta tas, su kansu su Fatima da Firdausi wadannan maganganu na Yayarsu Taiwo sun san firgitasu domin sunji sun yi zafi da tsauri sosai. Firdausi jikinta rawa ya fara yi ta soma cewa “haba-haba Aunty Taiwo? Haba ke kuwa don Allah Maman Kiki? Wannanba girmanki bane”. Ganin yanayin da Aisha ta shiga ya firgitasu. Babu ko digon hawaye a fuskarta amma tsigar jikinta duk ta tashi yarr, tsokar fatar bakin ta har raurawa takeyi amma ba kuka ba. Taiwo zata wuce toilet ta bar su a wurin suka ga gabadaya jikin Aisha ya dauki kyarma, idon nan ya koma kamar garwashin wuta ya kada yayi jazur… Ga dukkan mamakinsu Aisha ta mike da hanzari ta sha gaban Aunty Taiwo dake neman wucewa toilet wato ta gama zagin banza, ta sha lafiya zata wuce harkokin gabanta. Aisha ta tsaya gaban Aunty Taiwo, gabadaya ta koma Aisha-Siddiqarta fitinanniya, masifaffiya, ta Billiri ikon Allah! Gang leader mara tsoron kowa, sannan mara kara wato mai keke - da kekenta da kowa ya sani, ta kalli Aunty Taiwo cikin ido ta soma magana cikin sarkewar numfashi. “Na rantse yau kinci albarkacin haihuwa, kin ci albarkacin Kiki a wajeana, kinci albarkacin dimbin qaunar da ‘yar ki ta nuna min.Sannan kinci albarkacin
Chapter 5 · 0% Book details