← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da kyar Hamma yakai bakin mota, su Nenne dai tuni sun bude sun shige basu kara bi ta kanshi ba.
Bayan fitar Hammah Siddiqah ta yi unpacking ta fada wanka ko ta samu karfin jikinta daga gajiyar data kwaso, ta sille jikinnan tas ta zuba sassanyan turaren humra na “turarewutashop” (crème de la crème), tana gamawa ta dauko ‘lounge wear’ dinta wando da riga ta saka, sai ta dora hijab ta fito falon, tana fitowa taga wayam, Zaid har ya gama tattare wajen ya kunna bakhoor burner ya kwashe kayan abincin da wadanda aka bata, ya bar musu flasks na coffee da tea a dining din, da mugs da desserts harda da dan cup cakes ya tafi, ta kashe turaren don ya kare, sannan ta cire hijabinta ta kunna kallo.
Daman Hammah ya mata connecting wifi kafin ya tafi mayar dasu Nenne. Sai kawai ta kira Ummanta ta whatsapp vedio call, suka danyi hira akan saukarsu lafiya sannan Siddiqah ta haska mata wani sashe na gidan ta gani, tace “Umma kinga gidan” Umma tace “na gani Petel” ta sa albarka, bayan sun yi sallama da Umma ta kishingida a three seater din falon tana kallo, daga nan ne barcin gajiya ya dauketa. Kuma ko a cikin barcin nata duk mafarkanta Hamma Prince ne.
Saida su Nenne suka wuce priority lounge zasuyi jiran one hour kafin tashinsu Hamma ya juyo gida.
Yana tafe a hanya ya kira Zaid, yace kada ya zo masa gobe da safe sai ya neme shi da kansa. They will take care of themselves. A lokacin yana adana motar a muhallinta, ya dauko abubuwan da yake bukata ya fito ya rufe motar. Yasa mukulli ya bude kofar shiga falon.
Shiruuu baka jin komai sai hucin AC. Kafin ya ankara da Aisha a three seater tayi dai-dai akan kujerar tana sharar barcinta sadidan. Prince har da sakin ajiyar zuciya don ji yayi tamkar komai na rayuwa yanzu ya gama yi masa daidai (with his wife Siddiqah by his side). Hamma bai tasheta ba don ya ga alama tana jin dadin baccin, dakinsa ya wuce ya fada wanka.
Har Prince ya fito yayi sallah yayi changing zuwa kayansa na barci wasu ruwan tokar pajamas Aisha bata farka ba, a hankali Prince ya sunkuya yasa hannunsa biyu ya dauki Aisha, ya soma tafiya da ita a hannunsa, yana sumbatar kasan wuyanta da saman lips dinta softly, jinta dauke a hannun Hammah da wannan sumba da yake mata (soft and light kiss) Aisha ta bude idonta ba shiri, idanun ta suka fada cikin na Hamma Abdulrasheed (Prince).
Aisha tace “Hammah…” cikin magagin barci shi kuma yace “shhhh, cigaba da barcinki ban so kika tashi ba Baby”.
Sai Aisha ta mayar dasu ta sake lumshewa, ta kuma sunne fuskarta cikin kirjinsa don kunya, katuwa da ita an mata daukar jarirai. Prince ko a jikinsa don bata fice baby din ba a idanunsa.
A takiyar dakin Prince ya sauke Aisha, kasancewar ya kashe wutar dakin ga barci a idonta sai bata fahimci a inda suke ba, har sai da Prince ya kunna wutar dakin haske ya gauraye ko’ina ta gane masterbedroom dinsa na.
Aisha ta fara bude idonta a hankali cikin nutsuwa tana kallon yadda Prince ya shirya mata ‘special welcome’.
Chapter 23 · 0% Book details