← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 25

Sashe 17

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dan haka suka ce ta kawar da maganar Taiwo daga ranta ta fuskanci aurenta da mijinta da iyayen mijinta. Ta kyautata musu ta kuma rike su da kyau.
Baba Barau yace “tunda naga ya matsa ma Indo ko zaki hakura ki bar jamb din ne? Ban ga amfaninta ba tunda kasar zaku bari fa.” Tace “Baba gara inyi, ko ba komi dole zan koma makaranta, ina so in cigaba”.
Baba Barau yace “toh bakomi”.
Addar Kumo tace “gara dai ki kara satin kema, sai ayi miki shirin amarya, kamar yadda akayi ma ‘yar uwarki Maryam. Yanzu ne za mu kai diya, dan wancan kaiwar daman dai yin sa kawai akayi”.
Ummanta tace “nima zanfi son haka”. Aka ce “toh shikenan. Allah ya masu albarka”.
Toh dazu bayan azhar tana tsakar gida sai ga Baban ta ya shigo yace Hamma ya kira shi yace zai zo anjima ya musu sallama sabida gobe daga Litinin ze wuce Lagos, jibi zai tafi Argentina. Aisha tace “toh” tayi ciki.

Ta ma rasa me take ji. She is happy, kuma har ranta abin da ya faru ya wuce, amma kuma sai tana jin haushin Hamma yace zai tafi. Wato bai ma damu ba, da tace baza ta bishi ba. Hmmm! Da Haseena ce kila kuka zai yi tayi…mtsw…..
Satin nan da tayi a gida, quite sure tasan Hamma bashi da laifi, amman kawai dukansu taji sun bata haushi daga Taiwo din har shi. But daga baya tana dan missing dinshi.
Amman jiya yadda taji Baba Barau yana bata labarin nacin da yayi tayi akanta, ya dawo Gombe ma gabadaya duk sai ta ji tausayin shi da so me girma.
(She always want to be loved) sosai irin haka, toh gashi itama dai kamar Prince ya fara sonta.
Amman wannan cewa da yayi zai koma be matsa su tafi tare ba, ya bata haushi. Ta sake kwana a gidan Baba Barau dai, ta dawo gidansu tayi kwance har akai magrib.
Daman tun yau da safe aka fara mata gyaran jiki itama. Ummanta tasa an mata halawa dazu dasu dilka, tace baza a qara ba.
Toh yanzu ana ida magrib Umma ta miqa mata diye tace taje ta durje jikinta dashi ta hada mata lalle da khumra kuma tace ta dauraye jikin dashi. Aisha tace “toh”. Ta shige toilet tayi ta gama ta fito. gaba daya dakin har waje kamshi ke tashi. Tace “Umma nidai mura zanyi in kullum zan wannan wankan”. Haj Zainab bata tanka ta ba dai, tace “yi ki shirya ko Hamma yau zai zo zance” tace “kai Umma, ina tsoho ina zance” Umma tace Patel kenan, ana so ana kaiwa kasuwa. Ni je ki shirya kyaji da gulmar ki”. Ta wuce ta barta a wurin.
She is so nervous, a haka ta tashi tai sallahr isha. sai ta dauki kulaccen da Ummanta ta bata ta shafa, da tasa undies dinta black ta ma rasa kayan da zata sa, akwai wata abaya da Ummanta tazo mata dashi daga Hajj bata taba sakata ba daman suka tafi Lagos da Nenne. Ita ta dauka tasa, white and silver haka kuma cif-cif jikinta. Sai ya kwanta lubb! A jikinta, kugun nan nata ya fito masha Allah.
Tace ta san dai tayi kiba saboda abayan kamar yanaso ya matse ta, karin kibar nata har haka ne? data gama ta dauko ‘yan hannun gold din da Nenne ta bata na Makkah ta saka su, tasa ‘yan kananan ‘yan kunne na gold suma ba sarka. Tayi parking kitson ta tayi gammo da gashi. Sai ta dau gyalen abayar ta yafa. Tana zaune taji ana gaisuwa a tsakar gida, gaban ta ya fadi….
Shi kuma Prince tun da akai magrib ya dau wanka. Ya dai ma kasa cin abinci. Yayi sallah yana zaune da jallabiya har akayi isha, sannan ya shigo cikin sassan Oummana, Nenne tace yazo yaci abinci yace a koshe yake. Bari ya shirya zashi gidansu Aisha zai masu sallama tace “toh” ya shiga ciki ya dauko kananan kaya sai kuma ya mayar, yace gidan surukai ne. Sai ya dauko wata baqar (voile lace) na maza. tana da shara shara haka sai daukan ido kyallin ta yake. Wando da riga irin iya cinya dinnan cip jikin sa dinkin. Sai karamin hannu haka ba dogo ba iya gwiwar hannu. Haka Hamma ya shirya tsab, ya dauko hular sa Tonak ya saka baka itama, da design din silver a jikinta, ya zuba turaren ‘Tomford Oudwood’ ya kuma dauko ‘Francis Kurkdjian Baccarat Rouge’ ya fesa.
Wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikin Prince ya dauko ‘black hermes’ ya saka ya daura ‘rolex’ dinsa ya fito.
Ai yana fitowa sai Taiwo tasa guda har ma dai yaji kunya, su Nenne duk suka juyo, yace “meye haka Taiwo?”, tace ko dai mu dauko mayafi mu bika naga daukar amarya zaka yau” yace “kash!” Ya wuce.
Nenne da tayi murmushi dan tun bai fito ba suke jin kamshi. Lallai Aisha Siddiqa ta ciri tuta. yau Kehinde ke ta wannan rawar kafar haka zai je zance. “Alhamdulillah” Nenne ta gode ma Allah.
Yace musu se ya dawo ya fita. ya dau mallam Buhari suka wuce.
Prince ya yi sallama gidan su Aisha, Mallam Yunus yana tsakar gida suna zaune da Umma, ya amsa ya ce “shigo mana Abdulrashid”. Ya shigo ya gaishe su. Sun burge shi. Domin sun shimfida katuwar dadduma ga abinci nan a gefe, ga sallayar Umman Aisha da hijabinta akai. Nan tayi sallah kenan.
Tana gefen Mal. Yunus suna hira tana dama fura. Shikuma ya kishingida haka kan tuntu. They look so simple and very in love. Masha Allah kawai yace a ransa, ya karaso suka gaisa yace Oummana na gaishe su. Mal. Yunus yace suna amsawa ina Dade? Yace ai ya koma Lagos tun dazu. su Nenne suma jirgin safe zasu bi gobe. Suka ce “toh Allah ya kai su lafiya”. Akayi shiru, Umma tace “shiga palo Hammansu, bari in kira Petel”.

“Petel!!!!”
Umma ta kwada mata kira, ta amsa daga cikin dakinta tace “na’am” tace ga “Hammanku yazo, ki debo ruwa da abinci ki kai masa. Hammansu akul kayi min fulako” yayi dariya yace “Umma ai daga gida nake, furar kawai zan sha”. Tace “toh bari ta kawo maka” yace “toh”.
Ta nuna masa kofar falo ya shiga, ya zauna yana jiran gimbiyar tasa.
Chapter 17 · 0% Book details