← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

girma da shekaru. Sannan kinci albarkacin Nenne, mafi girma kuma kinci albarkacin tarbiyar da iyaye na suka bani akan wanda ya girmeni!!! Kinci zarafin dattako da tarbiya da kamalar da Nenne take dashi kuma ta baku ku ‘ya’yanta, kin ci amanar tarbiyyar data baki!!! Aunty Taiwo ta saki baki galala! Tana kallon yarinya karama haka kamar diyarta Kiki, ta tsaya a gabanta tana maida mata da martani, yarinyar da bata wuce second born dinta Kiki ba, duka mutanen dakin ma su Ifedayo da Aunty Bola sun sha mamaki domin basu zaci zata iya tankawa Taiwo ba sam, da yake cikin turanci take maida mata martanin duk suna ji, kallonta suke, shock duk ya kamasu. Firdausi ta soma bata hakuri daman tunda Taiwo ta fara zuba rashin mutuncin Firdausi tana ta cewa “haba aunty Taiwo, ki bari bai kamata ba” Taiwo ta ce mata “shut up malama! Kada ki kara saka min baki in ina magana”. Ganin haka gudun kada akai ga duka sai Princess Firdausi ta dauki wayarta jikinta nata kyarma ta yiwa Hamma text, tace maza ya bar duk abinda yake yi yazo don Allah ga Aunty Taiwo na cin mutuncin Aisha tana neman wulakantata a gaban dangi”. A take Hamma ya kira Firdausi immediately, ai kuwa Firdausi ta saka masa a handsfree, yana iya jin muryar Taiwo na karasa wassafa ma Aisha… “ki dake ni mana ‘yar Mallam Shehu! Shine zan san kinyi fushi na zagi makwadaitan iyayenki da suka yi miki auren sadaqah. An zagi iyayen naki, wata tsiya ne su? Ko zaki rama eh? Ke a karan kanki da dan hankalinki kinga dacewar ki auri Kehinde? Banda kankanba irin ta talakawa da kai kai inda Allah bai kai ka ba, ina ke ina zuri’ar Akanni? Ai da kin tafi kin auri mai kora shanu a kauye shine daidai ke…. Amma ba dan Sarki babban jikan Sarki ba…”. Hamma be kashe wayar ba a haka ya karaso hankalin sa a matukar tashe. Aisha ta wuce ta gaban Taiwo a zuciye, ko ganin gabanta bata yi. Wani irin tafasa zuciyarta keyi. Babu kuka ko digo a idonta zuciyarta ta bushe. Bata so ta kara wata kalma bayan wannan don zuciyarta na iya bugawa a lokacin. Firdausi ta kula da hakan ta taso ta biyo bayanta da sauri tana Siddiqah tsaya don Allah…. ko jinta batayi ba ta bude kofa, sai karaf! Tayi karo da mutum tsaye a bakin kofar. Data daga kai ta kalle shi da idanunta kamar gauta sai ta kawar da kai, ta sake juyowa tana kallon Taiwo data biyo bayanta…. ganin Kehinde yasa Taiwo tsayawa standstill. Wani irin bayyanannen bacın rai ne a fuskar sa, zata iya rantsewa tunda take da shi bata ta a ganin wannan yanayin a tare dashi ba. Ya bude baki zai yi magana sai jin Aisha yayi ta juya tana cewa da Auty Taiwo…. “Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye….”. Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga Prince ya bi bayanta yana “Aishah Please wait…Don Allah tsaya…” ko kallonsa Aisha bata yi ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana “please listen to me Aisha….”. Yayi sa’ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace “cikani, daga yau na gama wannan auren”. A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne suka sauka, inda tace. “na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada baa auren!” Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi. Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince da hanzari ya rufa musu baya. Nenne na jin irin numfarfashi da ajiyar zuciyar da Siddiqah ke sassaukewa a jejjere, ta durkushe a gabanta, ta hada hannayenta wuri guda cikin roko tace. “Nenne ke uwace mai adalci a wurina, babu abinda zaki sani in ki yi, amma don Allah ki barni naje gun Ummata. Nayi rantsuwa a gidanmu zan kwana yau. Kar kisa nayi kaffara. Ni Nenne wallahi Allah tun ranar da kika kawoni Lagos da niyyar zaki kaini asibiti, har aka kai ga maganar aure, aka yi aka dawo, duk da banaso har raina, ban taba jin zan iya yi muku gardama ba. kuma na karbi kaddarar auren a haka, nima ai da wanda yake so na din nake kuma son shi aka raba mu amma ban yi bore ba. Amma Nenne yau Maman Kiki ta tabo martabar wadanda ba’a iya taba su in hakura, inna hakura ma ji zan yi kamar nayi gagarumin laifi ga iyayena, don haka Nenne don Allah zan tafi, na rantse bazan kwana garin nan ba”. Jikin Nenne yayi sanyi kalau, at the same time she is so proud of Aisha, domin ta haifu, ta cika diya. Prince na kallon Nenne da dukkan hope na cewa zata lallashi Aisha ta shawo masa kanta ta saurareshi. Shi meye laifinsa a ciki? Amma sai gani yayi Nenne ta dauki wayarta tayi kira. Bai dai san wa ta kira ba yaji tana “lallai-lallai a nemo jirgin zuwa Gombe yanzu, idan ma babu direct a nemi na Abuja daga nan sai ta kara shiga wani”. Sai Prince ya dubi Nenne a firgice, yace “Nenne me kike nufi? Gidan zata tafi da gaske? Ta gama auren fa tace, ni kuma fa Nenne?” Gabadayansa a daburce yake, kansa da duk wani lissafinsa ya kwance, duk wani azanci da tsinkaye da kunyar idanun mahaifiyar tasa sun kwace daga hannunsa. Nenne bata ko bashi amsa ba tace “Aisha dauki kayanki kinji, muje driver da Dade suna waje suna jira zasu saka ki a jirgin Gombe”. Dadi sosai ya kama Aisha sai lokacin ta samu hawaye suka zubo, tafe da wata sassanyar ajiyar zuciya, tace “nagode da uzuriki, amma ni Nenne yadda nazo haka zan koma Gombe, ko tsinke bazan dauka ba”. Ta dauko wayarsa da ya bata daga jakarta ta russuna ta ajiye a gabansa ba tare data kalli yanayinsa ba. Saura kadan Prince yayi hauka a cikin kansa, musamman ganin Nenne tasa hijab ta kama hannunta suka fice suka barshi tsaye a wurin. Sai kawai ya fito daga dakin shima a matukar fusace, ya san yayi kadan ya dakatar da Nenne yanzu, a yadda yaga fushinta da bacin ranta irin wanda bai taba gani ba, to balle kuma Dade mijin tace din Nenne, wanda sai abinda Nenne tace yake amfani dashi. Don haka maimakon yabi bayansu, dakin su Taiwo ya nufa. Yana tafe da sassarfa yana tambayar ransa me zai yiwa Taiwo ya huce? Ance ba’a raba hanta da jini, ance blood is thicker than water… wai ba’a batawa da ‘yan uwa saboda mace, komin son da ake yi mata. Amma shi yadda yake jin matukar bacin rai da soyayyar Aisha data bijiro masa yanzunnan, mai raba shi da Taiwo dinsa yau sai Allah. **** **** **** Tun kafin su Nenne su karaso jikin motar daya daga cikin direbobin Emirate da Dade ya kira ya bude musu kofar gidan bayan wata jibgegiyar mota baka wuluk suka shiga har Aisha wadda hannunta ke cikin na Nenne. Direban ya ja motar cikin nutsuwa suka bar fada. Har sai da suka dauki hanyar airport din Ilorin sosai, suka yi nisa fintinkau da masarautar ta Ilorin, sannan ne Aisha ta ji ta (at ease) kuma bugun kirjinta ya soma lafawa, Aisha ta yi ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali, saboda abinda take so Nenne ta yi mata nan take, Nenne ta dubi halarci, kauna da amana ta yi mata kan ta rufe baki. Me za ta ce da Nenne Sappa? Ban da Allah ya ja kwananta? Tana jin Nenne da Dade suna magana amma da harshen Yoruba suke yi, (which means) ba su so ta fahimta sosai, don kuwa yarbancin mai zafi da sauri da sauri sosai suke yi. Amma a cikin dan abinda take tsinta yanzu a harshen ta fahimci kamar Dade na rokon Nenne ne akan ta bari a yi komai a hankali kada ta biyewa fushin Siddiqah, ta bata hakuri su wuce Lagos don yana so ya fahimci meye matsalarta data sa aka taso tafiya Gombe haka bagatatan, suna tsaka da sabgar biki, kuma daga ina matsalar take?” Sai taji Nenne na cewa, “A’ah Dade, yi hakuri ka barta ta tafi, ni a wurina tafiyar Siddiqah Gombe yau ba makawa sai wani babban ikon Allah mai karfi da ya gagari iyawata, matsalar daga Taiwo take, zaka fahimci komai daga baya don ba yau matsalar Maman Kiki ta fara akan Siddiqah ba, na yau din na fahimci yayi tsamari ne tunda har kaga Siddiqah tayi fushi, amma a halin yanzu bazan iya yarda da komai ba banda cikawa Siddiqah burinta”. Ta Lawanti International Airport. Dade ya yi ma Siddiqa tikiti, babu ko waya a hannunta haka ta shiga jirgin, Nenne ta gaya mata tana sauka Malam Buhari direban Nani Oummana zai zo ya dauke ta daga gidan Sarki. Ya kaita har zuwa nasu gidan. In kaga idanun Siddiqah a lokacin a soye suke kamar gyada marau-marau, babu ko kyallin hawaye a cikinsu. Na Nenne ne fal kwalla, suka yi sallama ta shiga jirgin Mangal. Dade dai yana gefe yana kallonsu ya rasa abin da ke masa dadi, don Nenne har zuwa lokacin ba ta yi masa wani cikakken bayani da zai gamsu da tafiyar Siddiqah Gombe kuma ita kadai ba, don ta ce ita ma ba ta gama fahimtar matsalar ba kawai ta yi wa Siddiqah abin da ta ke so ne kada hawan jini ya kama yarinyar, a yanayin da ta ganta kamar mai tashin iskokai sanda ta ke rokonta ta maida ta gida. Hakika Nenne ta tsorata, kuma ta dauki laifin duka ta dora a kan Abdulrasheed, duk da a hargitsatstsen bayanin Aisha ta fahimci ita dasu Taiwo ne. Siddiqah na sauka a Gombe ta tarar da direban Nani Oummana watau Buhari ya dade
Chapter 6 · 0% Book details