← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

raba ku lafiya”. Ai jin ciki sai Aisha ta yanke da kakkaifar wukar hannunta bata sani ba, tayi maza ta jefar da wukar, tsabar firgici, shima Hammah yace “ciki kuma Nenne?” tace “eh mana. Ba shine ba?” Sai yayiwa Aisha wani kallo, ya kece da dariya. Yace “Nenne yaushe tace miki ciki ne da ita?” Sai Nenne tayi shiru, sai kawai Hamma ya sake fashewa da dariya ya kashe wayar. Aisha itama abin ya dan bata dariya, ta dan dara ba shiri, ta kalli Hamma yana kara kyalkyacewa (he looks amazing), kamar bai ma san kalar kyan da far’a take yi masa ba. A wannan dan dakikan da take kallon Hamma Prince, sai taji (her whole world feels complete). Wannan din mijinta ne da ya hada komai da dan adam ke burin samu, kyau da nagarta, nasaba, ilmi da arziki da kuma kyan hali. Sai kawai zuciyarta ta hasaso mata haka yayi rayuwar soyayya da Haseenah, ita to da aka cusa masa ma ya sake yanzu yake kula da it aba karamin dadi take ji ba, to wannan wane irin dadi Haseenah tayi ta ji a ranta sanda suke tare suke soyayyah yana kula da ita? Sai kawai far’arta ta koma, Siddiqah ta mayar da annurin fuskarta ta sake dinkewa tsaf. Ganin haka sai ya kashe gass din data kunna, ya kama hannunta suka wuce (sitting room). A tare suka zauna a two seater, Hamma yace “Aishah, bana son mu gina rayuwarmu akan zargi da rashin communication. Ko me nayi miki banso kina fushi dani, just tell me. Kina ji na?” Aisha tace “yes” don taga ya kawar da wasa, he is serious now. Yace “menene yake damunki tun ranar can kike ta attitudes?” tace “babu komai” “ko ki fada min ko in kira Nenne, ita in ta tambaya na tabbatar zaki gaya mata” tayi shiru dai, da ya matsa sai tace “Uncle ko ka kira Nenne ni ba abinda kayi min, hakannan dai kawai ban jin surutu”. Hamma yayi shiru, daga bisani ya sunkuyar da kai, yace “kan zuwan Haseenah ne ko?” Sai Aisha ta mike tace “bari in karasa girki na”. Sai kawai ya janyota ta fado cinyarsa duk ta daburce tana kokarin tashi kawai sai taji yayi hugging dinta ta baya gabadaya. “Don Allah Uncle ka sake ni….” yai shiru, jin baida niyya itama ta share tayi shiru, baka jin komai sai bugun zuciyoyinsu. Can kuma Hamma yace (in a cool tone). “Yes, Haseenah was my girlfriend, naso aurenta, amma (she did something bad) da ya raba mu. The worst thing da kika sani za’a yiwa masoyin gaskiya. Kuma a kanta ne na rufe babin mata a rayuwata, wanda hakan yasa I feel Kaman duka daya suke, dalilin ma kenan da yasa ban kuma neman wata ba, kuma ko an bani cikin ‘ya’yan ‘yan uwana a family sai ince banaso…. Toh Aisha har saida Nenne ta nemomin aurenki da kanta, aka yi ban sani ba, don ta san inna sani bazan yarda ba, amma tun ranar dana je asibiti duba Nenne, na ganki, na yaba dake a raina Aisha, har na gayawa Nenne, nace wacece wannan yarinyar mai hankali haka…. Kinga dai kudin goro na yiwa mata, but you stood out, I was impressed with you”. Long story short, tun a lokacinma da bansan ke matata bace, naji kin burgeni da attributes dinki, kuma zama dake da nayi na dan lokaci na sake ganin me Nenne ta ganin min. Aisha naga meyasa iyayena suka nemo min aurenki suka aura min. Kamar yadda kikace addu’ar Nenne a filin Arfah ce ta fado a kanki wannan haka ne. don haka ke zabin Allah ce a gare ni. You are a light in my life and I am telling you you are shining so bright. Kinga duk ciwon dana ji na rashin Haseenah? To yanzu godiya nakewa Allah da nayi wannan rashin nata, don I wouldn’t have met you… So don Allah ki cire maganar Haseenah a kanki, babu abun fushi a wurin, You my Dear kin zama ‘ife mi, orun mi, iyawo mi’ kinji Aisha?” Sai ta daga kai. A zuciyarta wani sanyi na zuba, ashe haka ake ji in mijinka ya fifita ka kan kowa? That’s the Yoruba husband in action. Sai taji haushinnan yanata tsiyayewa… yana bin rariya, ta gyara zata tashi ya kara riketa, yace, “kin fahimceni yanzu?” Tace “yes Uncle” yace “Uncle ya dawo dai? Don Allah ya koma. Ni ina murna kina ce min Hamma, daga nan in zama honey, watarana in dawo Sweetie, shine kuma za’a koma Uncle dinnan, haba babyn Nenne da Dade”. Sai kawai Aisha ta saki murmushi. Tace “naji Ya Hamma” yace “ko kefa?” Sai tace “me kace dazu da yarbanci?” Sai yace “ashe kina ji? To ki koya ki fassara mana”. Aisha tayi dariya, sai lokacin Hamma yaji sanyi a zuciyarshi har da ajiyar zuciya. Bakinsa daidai saitin kunnenta yace “Babyn Nenne da Dade kuma Babyn Hamma ko?” Prince ya fada yana jin wani cool feelings for her, sai ta tashi da karfi zata wuce kitchen don kunya sosai ta lullubeta, tana ‘yar dariya. Hamma yayi maza ya dawo da ita jikinsa. Yaji dadin yadda yana mata bayani ta sauka, kuma da gani har ranta abin ya wuce. She’s a very understanding person. Sai Prince ya sake rungumeta sosai ta bayanta, yayinda take zaune a kan cinyar sa. Itama Siddiqah sai tayi mukus…. Hamma ya kwantar da kansa bisa masangalin wuyanta… yana sunsunar kasan wuyanta, duk sunyi shiruuuu na wani lokaci, kamar ruwa ya cinyesu. Bugun zuciyoyinsu kawai kake ji wadanda ke bugawa a lokaci guda. Murya a sanyaye Aisha tace "Hamma, thank you for the explanation, nasan ba dole bane kayi min bayaninnan, amman naji dadi da kayi min din, domin ya wanke min zuciya. In sha Allahu kuma nima bazan qara fushi ba kan maganar nan". Prince yayi murmushi, voice dinta yana caressing din sa, gabadaya wata kasala ce ma ta sauko masa, yana ta kokarin dannewa. Ya dai kasa magana yai shiru, ya rufe ido, listening to her soft sound, tana masa wannan maganar cikin lumana da gamsuwa da abinda yace mata, and the softness of her skin dake kwance a jikinsa yana kara tasiri a tare dashi. Sai Hamma ya samu kansa da dan murza hannunta …. jin shirunsa yayi yawa bai amsa ta ba, sai Aisha ta juyo kadan haka ta dubeshi. Sai ta ga Hamma da ido a lumshe, kamar mai jin barci. A tsanake tayi kokarin tashi daga cinyarsa, ya kuwa rike ta gam, ya dan bude idon yace "ina zaki?" Aisha tace "abincin zan qarasa" yace "kashe gass din, we will eat out today, just stay here…". Aisha tayi shiru, ta koma jikin Prince ta kwanta tayi lamoo! Yace "please Aisha..... muje outing din?" Tace "toh ai bacci kake ji naga", Hamma yace "bacci? Did i say so?" Ta ce. "To ai Hamma idonka rufe yake fa tun dazu, ina ta maka magana bakaji ba, gashi ma muryar bacci kake yimin". Prince bai san sanda wani kasaitaccen murmushi ya kufce masa ba, he so much loves her naivety. And she is observant, but totally ignorant ga halin da yake ciki. Yes, yanayin sa gaba daya ya canza, wata muguwar sha’awa ce ta saukar mashi. It seems with every word she says kara yayyafa ma wutarsa petrol take, amman babyn Nennen bata gane ba. Wannan childishness dinnata yana kara burge shi. Hamma yace "Ayshaaaaa…" tace "na'am Hamma" yace "ba bacci nake ba, I am just in a mood!" Ya fada yana mata wata kallo, mai shiga rai da sanya kasala. Har sai da Aisha ta tsargu don ya kara jawo ta jikin sa sosai, this time around juyo da ita yayi tana facing dinsa gabagadi. Aisha tayi shiru, yace "baza ki tambayeni what mood ba?" Tace "toh Hamma bacci kake ji, kuma ka kafe kai baka ji" ta dan turo bakin ta gaba, tana fada cikin shagwaba 'yar gaske. Ai kuwa Prince ya sa ido yana kallon bakin da take turowa so soft and luscious, bai san sanda yace "I really really want to kiss you saddiqa… "ya matso dab da fuskar ta, har suna jin numfashin juna, ya kalle ta, cikin idonsa kadai ta ga tsantsar al'amuran dake cin zuciyarsa da gangar jikinsa. An yi sa’a itama ta juyo kenan sai kawai Hamma ya hade bakinsu wurin guda ya soma kissing Aisha-Siddiqah in a serious tone and passionate manner. Da kyar Aisha ta samu ta zame daga Hammah, ta mike jikinta yana rawa a daburce tayi hanyar kitchenette. Hamma da kyar ya iya mikewa yanakokarinsaita kansa. Yabi bayanta yana cewa cikin basarwa, “you know what? Jeki shirya kawai ki bar girkinnan, we are going out, ma ci a waje”. Tace “toh”, sai ga Nenne ta sake kira. Tace “ni Hammansu dazu maganar bikinsu Princesses na kira zan maka na manta, an saka rana, kwanaki goma masu zuwa. Don Allah ka taho da Aisha, kuma kuzo da wuri. Asabar ne daurin aure wato ranar addu’ar arba’in din Sarki”. Prince ya ce “toh Nenne, in sha Allah”. Itama Aisha sai murna lokacin da Hamma ya gaya mata zasu tafi gida Lagos sati mai zuwa, tace “bikinsu Firdausi za’a yi?” Yace “eh, za’a hada da addu’ar arba’in na Emir. Shine babban burinsa kafin rasuwarsa wato auren twins din gidanmu”. Siddiqah tayi ta murna har ‘yar rawa ta shiga takawa a wajen, ta manta shaf a gabansa take, irin murnar zata gida dinnan, after a long while. Hutun Prince ya dade da karewa, zuwan Siddiqah ne yasa ya kai har wannan lokacin a Argentina. Sun fita a daren sun shakata, suka ci abincin dare a wani Arabian Cuisine sannan suka dawo gida. Aisha ta nufi dakinta tayi wanka ta sha rigar barci mai dan kauri purple ta fesa turarukanta masu dadin kamshi ta nufi dakin Prince. Nan ta tadda shi daga shi sai short nicker akan sofa yana shan ‘chamomile tea’ kafin ya kwanta. Ta na shiga Hamma ya dago yana dubanta da wani kallo da bai taba yi mata ba, domin sha'awar matarsa ce zallah yau cikin idanunsa da duk abinda yake yi. Aisha ta juya da sauri zata koma ganin ba suttura a jikin Hamma sai gajeren wando, ga kunya data kamata sai
Chapter 3 · 0% Book details