← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka ɗauki kusan 20m kafin su fito daga room ɗin. Da sauri ya miƙe ya na ƙarasawa dan jin me yake faruwa dafa kafaɗarsa Dr yayi kafin ya ce "Muje office sir" babu musu ya bisa suka shiga office ɗin nasa zama yayi akan kujera yana nuna masa shima kujera babu musu ya zauna, cire farin glass ɗin dake fuskarsa yayi ya na duban Suhail "Bakomai ne ya haifarma da wannan shiga yanayi da ba tashiga ɗinmuwa ne kasan a wasu lokuta mutum idan bai saba da abuba toh aduk lokacin da abun ya faru da shi ya na shiga gigici da ɗimuwa kuma ita yarinya ce qarama, dole ne sai an dunga kiyaye wasu abubuwa sir "Insha Allah za'a na kiyayewa, yanzu zan iya ganinta?" "why not yanzu haka tana ɗakin hutu zaka iya zuwa, zuwa anjima idan ta tashi zaku iya tafiya" godiya ya masa ya miƙe ya fita

A cikin company kuwa kowa ya ya fito a office ɗinsa sun tsa-tsaya sai mai da magana ake ita dai Suhailat tana gefe ta haɗa hannuwa ta biyu a fuska babu abun da ke zuba daga idanunta sai hawaye, gashi babu damar ta bi su Mdee hospital ɗin. Yana shiga cikin ɗakin ya tarar da ita kwance tana bacci karasawa yayi gaban gadon ya zauna ya na kallonta "Am sorry Ayrah ni ne naja miki kiyi haƙuri bazan ƙaraba kinji", ya faɗa Kamar ta na jinsa hannuta ya ruke cikin nasa kiran dad ɗinsa ne ya shigo cikin waya da sauri ya ɗaga a ɗaya ɓangaren kuma dad ya masa "Hallo son kana lafiya" "Lafiya qlau dad" "Masha Allah karka manta da taron yau fa ka san taren na da matuƙar muhimmanci ko?" shiru yayi dan shi gaba ɗaya ma ya manta da wata maganar taro 'Ko baka jinane?" "Ina jinka dad insha Allah bazan manta ba" "Toh Allah yasa muma munan muna shiri"

Yana katse kiran ya kira h.o.d cikin Company "Ku shirya komai da za'a bukata na taro, karku damu sai na zo no kuyi komai yadda ya kamata" "Okay sir Insha Allah za'a yi hakan" katse wayar yayi ya na duban Ayrah da ta ke bacci abunta 2hours later
A hankali ta ke buɗe idanunta ganin Kamar mutum a zaune a inda ta ke yasa ta saurin karasa buɗe idanunta murmushi ya sakar mata dauke kanta tayi daga kallon nasa "Sannu ya jikin" banza tayi masa tana tuna abun da ya faru wani sabon kuka ta fara "ya ilahi ki yi shiru Please ki daina kuka nan dan Allah" "Ni ka kaini wajan Mamana bana son zama anan" "Naji zan kai ki amma sai kin yi shiru" mai makon ma tayi shiru sai ta cigaba da kukanta tashi yayi har ya kai bakin ƙofa ya ce "Taso muje ai da sauri ta duro akan bed ɗin ta bisa a baya dr suka gani na ƙoƙarin shigowa murmushi yayi "Sir kace har kun fito" "Eh" ya bashi amsa a taƙaice su na isa haraba hospital ɗin drive ya ta so da sauri "Ka koma Company ni zan kaita gida" "Okay sir" ya faɗa yana buɗe masa motar zagayawa yayi ya buɗewa Ayarh ta shiga da gudu ya ja motar dai-dai wani ɗan ƙaramin stor ya tsaya ya siya mata abun da zata iya ci tare da kayan tea

Dawowa yayi cikin motar yaja suka tafi, suna isa ƙofar gidan da sauri ta buɗe zata fita ruƙe mata hannu yayi yana girgiza mata kai kwaɓe fuska tayi zatai kuka "Shiit ni bacewa na yi kimin kuka ba," ya faɗa ya na miƙe mata leda "Idan kin shiga gida ki gaida min da Mama sananan ki bari sai kinji sauƙi kya dawo aikin kin ji? Allah ya baki lpy kuma kiyi haƙuri nasan nine naja miki" "Babu komai nagode" ta faɗa ta na fita daga motar kwanta da kansa yayi a jikin kujera ya na murmushi shi kaɗai ya san abun da yake ji akan yarinya ganin har ta daɗe da shiga gida ya sa ya ja motarsa yayi gaba

Kai tsaye gida ya nufa dan baijin zai iya komawa Company a wannan yanayi ya na isa ya nufi falon ya nasa

Tana shiga Mama ta ta so tana tambayarta lafiya fashewa tayi da kuka tana rungumeta, ruƙeta tayi suka nufi cikin ɗakin suna shiga ta kwanta akan tabarma "Wai Ayrah menene ya faru?" "Kai nane fa ya ke ciwo" ta faɗa a shagwaɓɓe "Amma ke kam wai yaushe zaki daina kukan ciwon kai ni Allah na zata ma ko wani abune ya faru tashi toh ki ci abunci kisha magani" "A'a Mama ni na ƙoshi ta" faɗa tana miƙa mata ledar da Mdee ya bata "Ita kuma wannan ledar menene a ciki?" "Mdee ne ya siyamin kuma ma ya ce na gaidaki" "Toh Ina amsawa mungode sosai da ɗauwai niyar da ya ke" ita dai Ayrah bata sa ke cewa komai ba ta rufe idanunta

Da da dare suna zaune Ayrah ta dubi Mama "Wai Mama mu Shikenan haka zamu cigaba da rayuwa mu kaɗai?" shiru Mama tayi bata ce komai tabbas itama a koda yaushe tana wannan tunani shin idan rayuwa ta ciga da tafiya haka watara na fa zata mutum alokaci sai dai yar'tata ta yi itama rayuwa ita kaɗai, ganin hawaye na zuba akan fuskarta ya sa ai Ayarh saurin nufo in da ta ke "Dan Allah Mama kiyi haƙuri idan magana ta bata miki daɗi ba" murmushi kawai tayi tana rungumeta adaran dai haka suka kwana cikin tunani rayuwarsu

Washegari da wuri ya tashi ya shirya yana fitowa security ya buɗe masa motar ya shi, su na isa ya shiga office, Suhailat da dama zuwansa ta ke jira, ta tashi da sauri ta nufi office ɗinsa kanta aƙasa ta shiga da salama amsawa yayi ya ɗago ya na kallonta "Good morning sir" "Morning how are you" "fine" "Dama sir tambayarka zanyi ya jikin Ayrah" "Jikinta da sauƙi tana gida, sai bayan ta ƙara samu sauƙi zata dawo aiki" ya faɗa yana danna lapton ɗin dake gabansa "Okay Allah ya bata lafiya" "Ameen ya rabbi" godiya ta masa tana fita daga office ɗin

Tana fita p.a ta tare ta "Am me Mdee ya ce akan yarinya, har yanzu tana asibiti" wani kallo Suhailat ta mata tana wucewa abunta "Mtss kada Allah ya sa ki faɗa yar raini hankali, daga gani yarinya shikenan kunbi ku liƙe mata Allah shiƙara wallahi ni na so ma ace ta mutu muga ƙarshen iskanci"
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

A WANI COMPANY

BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

fallow my account

Arewabook@hauwauomar05

Page_12_13

Yau kusan kwanan Ayrah uku agida bata zuwa aiki. Gaba ɗaya baya jin daɗin aikin ji yake Kamar akwai wani abu da yayi giɓi cikin aikin na sa. A hankali ta mike da ga kwance da ta ke ta na kallon Mama meƙewa tayi ta shiga toilet dan yin wanka, ta na fitowa ta nufi cikin ɗakin ta shirya tsaf cikin doguwa riga ta atamfa hajjab ta zura Masha Allah ta yi kyau sosai fitowa tayi ta na wa Mama bye bye ta fita sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta samu mai napeep ɗin da zai kaita zuwa Company tana isa ta shiga ciki office ɗin Suhailat ta shiga ta na ganinta ta miƙe da sauri ta rungume ta "Oyoyo sister yau kinzo kenan?" murmushi tayi tana gyaɗa mata kai "ya jikin naki?" "da sauƙi Aunty Suhailat"ta ce" Masha Allah Mdee ya san kinzo ne?" "a'a yanzu na zo ai" ta ce"Okay maza kije zuwa anjima kya dawo kinji" fita tayi ta nufi office ɗin Mdee ɗago kai p.a tayi ta na kallonta dan ita gaba ɗaya ma ta manta da ita wuce wa tayi zuwa ciki yana ganinta ya ya yi murmushi, Murmushi ita ma tayi tana zama akan kujera ya ce" ya jikin na ki?" "da sauƙi" ta bashi amsa.

Kasa tashi tayi ta haɗa masa coffee dan tana gudu abunda ya faru ranan ya sake faruwa jita yi ya ce "coffee" jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi wajan haɗa coffee ɗin tana haɗa masa ta zo kan table ta ajiye zama tayi akan kujera tana wasa da yatsun hannunta sai da ya gama tsaf kafin ya miƙe kallonsa tayi nufar ɗakin hutunsa yayi ita dai tanan zaune har ya shige kuma bai mata magana ba ta kai kusan 20munith kafin ya fito cikin cuz brown Masha Allah yayi kyau sosai.

hanyar fita yayi juyowa yayi yana kallonta ganin ba shi take kallo ba yasa ya ce "muje ko" ɗagowa tayi ta na kallonsa dan bata gane inda maganarsa ta dosaba "cewa nayi ki taso muje" babu musu ta miƙe ta bi bayansa p.a na ganinsa ta miƙe karasawa yayi "bani file ɗinnan" miƙa masa tayi har yayi gaba tace "am sir ko nazo muje tare ne?" "ban nemaki ba idan da ina da bukatar hakan da zan faɗamiki" shiru tayi bata sake cewa komai ba har suka fita zuwa waje

Shiga yayi cikin motar itama ta shiga suna isa drive ya fito ya na buɗe musu ƙofa tana ganin inda suka zo ta haɗe rai haka kurum a bar mutum shi kaɗai har ya gaji murmushi yayi ya na juyowa ya kalleta dan ya ji abunda ta ce ganin ya na murmushi ya sa tayi shiru suna isa ya nuna mata wajan zama karasawa yayi wajan meeting ɗin
Chapter 9 · 0% Book details