← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ta kama asabar kasan cewar babu aiki yau zaune ta ke cikin ɗakin hannuta ruƙe da beskit tanaci, Mama ce tashigo cikin ɗakin ta na kallonta "Hajiya shan zaƙi yau ansamu abunda ake so" sun kuyar da fuskarta ta yi ta na dariya "Ma za ki tashi muje gidan alh hadi, tin ɗazu ya aiko mu zo kina bacci" murmushi ta yi ta miƙa ta na gyara zaman riga dake jikinta hijjab ta saka na riga su ka fita suna tafe suna hira har suka isa gidan. a parlor su ka samu hajiya da sauri Ayrah ta ƙarasa wajan Hajiya sarai ta na murmushi ita ma murmushi tayi "A'a yau ma'aikata ne a gidan namu? sannu da zuwa lale marhabu da daughter" karasawa ta yi ta na rungumeta habib da shigowarsa kenan cikin parlor ya yi gyaran murya "Nifa na fahimci Momy kamar kinfi son Ayrah akaina Allah" ya faɗa ya na turo baki gaba kamar wani karamin yaro. tin tsirewa Ayrah ta yi da dariya ta na nunasa wollah ya habib da ka yi shagwaɓɓa ka yi kyau sosai" murmushi kawai ya yi, ya na karasa shiga cikin parlon

Gyaran murya alh hadi yayi ya fara basu labarin yadda sukayi da Suhail fashewa Ayrah ta yi da kuka "Yanzu Daddy idan ka tafi ni yaya zanyi kuma dawa zan dinga tafiya"?karki damu daughter Mdee ya ce za'a san yadda za'a yi insha Allah komai zaizo da sauƙi" Allah ya sa" anan alh hadi ke faɗa musu Insha Allah ranar Monday za su wuce Austiralia kuma shi da iyalinsa za su tafi, ba karamin damuwa su ka shigaba jin haka amma babu yadda za su iya "Shikenan alh Allah ya kaiku lafiya" Ameen ya ce ya na miƙewa dan yana son ya je wani waje Saboda shirin tafiyarsu

Suna isowa gidan kai tsaye Ayrah ta nufi É—akin, ta na shiga ta kwanta gaba É—aya sai tajima aikin ya fita kanta.

Zaune ya ke akan sujerun da ke garding ɗin hannusa ruƙe da cup ɗin juice ya na sha jin gidana ya yi da kujera ya na lumshe idanunsa ji ya ke ina ma yau ba ta zo a sturdy ba, gaba ɗaya zaman gidan ya ishe shi gashi babu wani wanda ya sani bare yaje in da yake. Ayrah shine abunda zuciyarsa ta faɗa masa tabbas gidan su Ayrah ya kamata ya je har ya miƙa kuma wani tunanin ya zo masa shin idan yaje gidansu ya ce mata me? kai ina bazaije ba gaskiya, gwara ya yi zamansa shi kaɗai. tashi ya yi ya nufi cikin gidan ya na shiga ya janyo lapton ɗinsa dan kiran Daddy ɗinsa.

Da fara'a dad ya ɗaga wayar murmushi ya yi ya na kallon mahaifinnasa "Allah dad ni na fara gaji da ƙasarnan, idan fa babu aiki sai dai na yi ta zama a gida kamar wani mara gata, ya faɗa cikin shagwaɓɓa" murmushi Daddy ya yi dan yasan rigima Suhail ce ta motsa "Ka yi shiru dad, yaji murya Suhail ta katse ma sa tunanin da ya tafi "Haƙuri zakayi son tinda kaga tunda ka dawo Nigeria ba'a kara samun wa ta ɓannaba, na san kana ƙokari kuma nima ina matukar kewarka. amma Insha Allah inan zanzo na kawo maka ziyara da zarar na gama da aikin dakenan" murmushi jindaɗi ya yi "Promise dad" "I promise you son"

cigaba sukai da wayar ta su cikin farin ciki da kaunar juna su na gama wayar ya kashe lapton É—in ya na lumshe idanunsa tabbas ya na natukar son mahaifansa baya iya haÉ—asa da komai

Tashi ya yi ya nufi ciki dan ya samu yayi bacci.

Cire kayan da ke jikinta ta yi ta nufi bayin na su ta watsa ruwa ta na fitowa ta tsaya a gaban wadrop ɗin ta su ta na kare mata kallo tinani kayan da za ta saka ta ke, ganin har kusan takwas ta yi ba ta fito ba ya sa Mama ta tashi ta shiga ɗakin tsaye ta ganta a jikin wadrop ɗin ta zu ba mata idanu murmushi ta yi kawai ta karasa ta na taɓata, da sauri ta dawo da kallonta kan Mama "Ke kuma lafiya? ki ke ta kallon wadrop Kamar kinga sabon abu" turo baki ta yi kamar zatayi kuka kafin ta ce "Ni to ba rasa kayan da zansa na yi ba" "Tofa yau nabanu wai Ayrah yaushe zaki daina wannan halayyar taki? ace kullum mutum in ya yi wanka sai ya ta ruwan ido, kafin ya sa kaya" Mama ta faɗa ta na janyo wata marron ɗin abaya cikin abayoyin da Mdee ya siyamata "Ingo wananan ki sa ka" karɓa ta yi ta na murmushi zura riga ta yi a jikinta wow Masha Allah yanda kasan dan ita aka yi riga, ba karamin kyau ta mataba ƙarasawa wajan mero ta yi ta shafa tirare da leps glows a bakinta kama kanta ta yi dan ɗaurewa tin ta na yi ta na ganin za ta iya harta fashe da wani irin kuka mai cin rai. ƙarasowa Mama ta yi ta kama kan ta na ɗaure mata da wani white ribom mai kyau, hula riga ta sa ka white sai belt na riga shima white ta yi rolling dashi, takalmi ta zura plat. ba ƙaramin kyau Ayrah ta yi ba yadda kasan yar turai. fitowata yi ta na ɗagawa Mama hannu. Fita ta yi waje ta na tunani ta yadda zata tari abun hawa ya kaita Company. Turus taja ta tsaya ganin wata arniyar mota kirar pontic gto(1964). Tsayawa ta yi ta na kallon motar a hankali ya sauke glass ɗin ya na sakar mata murmushi, murmushi itama ta yi ta na nufar wajan motar. Da sauri drive ya buɗe mata tashiga, godiya ta masa ta zauna "Good Morning sir" "Morning" "how are you today" "fine" ta bashi amsa a taƙaice
Su na isa cikin Company ta buɗe murfin, "Ba kiji ba"ya faɗa a hankali juyowa ta yi ta na kallonsa, ganin idansa har yanzu a lunshe kamar bashi yayi magana ba "Kinyi Kyau sosai" "Thank you very much" ta faɗa ta na fita a motar shima fitar ya yi ya nufi hanyar da za ta sadashi da left, sai murmushi ya ke shi kaɗai kamar wanda akaiwa bushara 😂

Ya na shiga ya nufi office ɗinsa da fara p.a ta gaidasa ko kallon inda ta ke baiba bare ta sa ran zai amsa mata. Jiki a sanyaye ta karasa kan kujerata ta zauna hawaye ne ya fara zarya akan kuncinta. Turo kofar ta yi ta shiga bakinta ɗauke da salama da sauri ta goge hawayenta ta na gallawa Ayrah harara, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tai gaba abunta ta na shiga ta nufi wajan haɗa coffee dan ta san zai bukacesa zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta ke komai cikin nutsuwa samun kansa yayi da sakin wani murmushi wanda shi kansa bai son manufar yinsa ba

"Sir" "Sir" gaba ɗaya ya faɗa duniyar tunanin baima san ta na masa magana ba sai da ta bibuga table ɗin sannan ya dawo hayyacinsa karɓa ya yi ya na kaiwa baki ƙara lumshe idanunsa ya yi ya na kai kofin bakinsa sai da yasha sosai kafin ya ɗago ya kalleta. "Yau baki tawo da abinci Mama ba?" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar eh "Dama ina son na maka godiya da kayanan nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Mama ma ta ce na maka godiya" "Babu komai na yi dan Allah so dan haka ni aganina ba abun godiya bane." "Sannan daga yau duk abunda da na baki ba na son godiya kinji" ya faɗa ya na kafeta da idanunsa ma su matukar kwarjini saurin sunkuyar da kanta ƙasa ta yi dan bazata iya jurar kallonsa ba.

Da salama ta shiga ciki office ɗin wanda baida wani girma samunsa ta yi zaune ya haɗa hannusa biyu akan fuskarsa da alama wani abun yake tunani. Murmushi ta yi ta na karasawa ciki, hura masa iskar da ke bakinta ta yi "Lafiya kai kuma ka ke ta fama tunani?" murmushi kawai ya yi ya na cije leɓansa na ƙasa "Hmm wallahi har yau na kasa mantawa da abunda Mdee ya min akan yarinyar nan" "Kaima kenan daba wani abu ya maka ba" "Ni tozartani ya yi agabanta😥 "Ni da na ke matsayin p.a ɗinsa amma ko ta ni bayayi, sai wata ƙaramar yarinya" tsaki ta yi mai sauti dan a duk lokacin da ta tuna wa ta irin wutar tsanar Ayrah ke karuwa tabbas ta yi alƙawarin sai ta wahala da yarinya wahala wadda ko aljan sai yaji tausayinta bare mutum. "Wai me ki ke tunani ne? ina miki magana kin min banza kin san fa ba na ɗaukar wulakanci ko" Abdul ya faɗa a hasale "Kaifa daɗina da kai rashin haƙuri ina tunani yadda zan wahala da yarinya ne, da yadda zan rama abunda tamin" wa ta irin dariya ya sheƙe da ita ya na kallonta "Ina jinki me kike tunani kenan?" murmushi ta yi ta na gyra zamanta akan kujera. Matsawa ta yi dab da shi ta raɗa masa wani abu akune wata irin dariya su ka sheƙe da ita su duka, su na tafawa "Sai yanzu na kara yadda da ke wace" "Kai dai kawai ka kasance cikin shiri dan a koda yaushe zakajini na nemaka" "Angama shugaabar mugaye duniya" wata dariya ta karayi ta na fita a office ɗin

rungumeta Hajiya ta yi su na kuka "Idan Ayrah ta dawo kice ma ta mun tafi" gyaÉ—a kai Mama Ayrah ta yi har sun shiga mota Habib ya fito "Aunty idan Ayrah ta dawo kice zan yi kewarta sosai, ki gayama zanzo na É—auketa mu koma Australia tare" murmushi Mama ta yi ta na goge hawayen da ke fuskanta..
Chapter 6 · 0% Book details