Sashe 13
A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da sauri ta ƙarasa shiga cikin ɗauki idanunta na zubda hawaye, jijigata tafara yi ta na kuka. Buɗe idanunta ta yi da ƙyar wanda su ka ma ta wani irin nauyi. kallonta Mama ta yi, menene ya faru da ke Mama? dan Allah ki tashi shine kawai abinda ta ke faɗa idanunta na tsiyaya da ruwa kama hannu ta yi tana matsewa a nata "Fatima" ta kirata cikin Normal sunanta "Ki yi haƙuri da rayuwa Fatima ki kula da rayuwarki ko ba na raye, kimin alƙawarin kare mutuncinki Fatima ina matukar ƙaunarki, ina jin kamar bazan tashi ba sai dai a kullum ina kuka rashin iyayena dan da na son in da su ke da komai zaizo mana da sauƙi ina matukar ƙaunarki Zarah" ta faɗa tana lumshe idanu "Mama dan Allah ki daina faɗar haka Insha Allah zaki tashi" murmushi kawai Mama ta yi da dugu ta shiga cikin ɗakin ta ɗako ledar magani ruwa ta ɗibo ta zo ta na bata gyaramata kwanciya ta yi bacci ne ya ɗauketa da sauri ta miƙe ta nufi bayi dan ɗauro alwala sallah t ayi raka'a biyu ɗa ga hannuta ta yi sama ta na kuka da roƙan Allah ya bawa Mamata lafiya
Ta na idarwa ta kwanta a gefan Mama bacci ne ya dauke ta
Washegari Alhmdllh Mama ta ɗan fara samun sauƙi Ayrah shara gidan ta yi tass kunu ta dama mu su bayan sun gama sha Mama ta kalleta "Ayrah ya kama ta ace kinje aiki" girgiza ma ta kai ta yi "Ki daure kije kinji insha Allah babu abunda zai faru da ni" babu yadda ta iya miƙewa ta yi ta nufi ciki ɗakin dan shiryawa ta na gamawa ta fito da hajjab har ƙasa murmushi Mama ta ma ta "Allah ya tsaremin ke a duk inda ki ke" "Ameen Mamana" ta faɗa ta na sumbatarta a kumatu tsaye ta ganshi a jikin motar da alama kuma dama ita ya ke jira tuntuni, tunda ta fito ya ke binta da kallo wani irin kallo ya kemata Wanda bai taɓa ma ta shiba dube-dube ta fara yi a jikinta dan ganin ko wani abune da sauri ya kawar da kansa ya na shiga cikin motar shiga itama tabyi yaja su ka tafi su na isa ya fito ya yi ciki ko left yau bai hauba ya nufi stap..
Shiga ya yi cikin office ɗin, dafe kansa ya yi ya na furza da wani wahalala numfashi shi kaɗai ya san abun da ke damunsa tabbas yau ce rana da ya kamata ya aiwatar da abunda zuciyarsa keson ya aiwatar ɗin. Da Salama ta shiga cikin office ɗin ɗaga kai ya yi ya kalle ta, nufar gurin haɗa Coffee ta yi da sauri ya dakatar da ita "Kije kawai bana bukata" ba ta damu ba ta nufi hanyar fita daga office ɗin ƙasa ta sauka wajan Aunty Suhailat ƙarasawa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi
"Ke Jiddah Jiddah ki tashi fa na ce" turo baki ta yi gaba tana jin haushin tashin da'a kamata wai Ammi sai ina bacci ki ta tashina" banza Ammi ta mata ta nufi kofa tai fucewarta
a hankali ya ke sakowa daga bene Ammi ce ta tsaya ta na kallonsa murmushi ya yi lokacin da ya ƙaraso guri "Ammi kallon fa?" "Ai dole na kalle ka son yau na ga abun da ban taɓa gani ba, kai ne wai yau ka sa ka manya kaya? kuma ba karamin kyau su ka maka ba" dariya ya yi sosai wadda ta kara masa kyau Ammi dai kice sokike ki ce bana sa wa" "Da toh sawar ka ke ne" murmushi kawai ya yi "Anya babana ba wajan wa ta zaka ba?" haɗe rai ya yi kamar bai taɓa dariya ba dan in da abun da ya tsana a rayuwarsa toh bai wuce amasa maganar mata ba shi ya yi soyayya ma ya ce ya yi me shifa gaskiya har yau baiga wace ta isa ya sota ba, ganin ya haɗe rai kamar baya dariya ya sa Ammi cewa "Allah dai ya shiryaka Babana wai ni kam kai kullum idan aka maka zance budurwa sai ka sauya fuska shikenan sai kayi ta zama ba kai aure ba, kai kasani yanzu ka yi duba da Sa'a nin ka duk sunyi aure wasuma har ya'ya gare su" "Ammi su su kaga zasu iya wahala" ya faɗa ya na wucewa murmushi kawai Ammi ta yi tai gaba abunta dan yau ne Abieey zai dawo Nigeria
Momy ce zaune a cikin bedroom ɗinta ta na waya sheƙewa ta yi da wata dariya "Ke dai bari kawai kawata ai komai na shirya shi yanda ya kamata yoh Allah na tuba taya zanyi sanya da wannan aiki idan kika ga ban aiwatar ba toh kice ni zainab an buneni ne a rami kinga a lokacin ai babu abunda zan iya" ta faɗa tana ƙara sakin shu'umin murmushi Yusra da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin duk taji abun da mahaifiyartata ta faɗa hawaye taji na zuba a fuskarta shin yaushe ne Momy za ta gane ta dai na irin wannan abubuwan? da sauri ta bar bakin ƙofar gudun karta fito ta ganta..
Cikin murna Fahad ya fito ya na murmushi ganin abokin na sa dan baitaɓa tunani da gaske zaizo gidan na saba kama hannusa ya yi su ka shiga cikin parlon zaunar da shi ya yi akan kujera ya nufi cikin bedroom ɗin ya na kiran Samha fitowa ta yi da fara'a "Badai har babban baƙon namu yazo ba?" "wallahi kin ga ko ya karaso' murmushi ta yi tana fita a ɗakin drinks ta ɗako da sincks ta nufi kan centar table ɗin ta ajiye ma sa "Ina yini brother" murmushi ya yi ya na kallonta "Lafiya qlau Samha ya gida" "Alhamdulillah yau dai Allah yayi munganka a gidan mu" "Ai kuwa dai" ya faɗa a taƙaice zuba ma sa juice ɗin ta yi ta na miƙe ma sa godiya ya ma ta ya na karɓa
Suhailat ce ta dubeta "Kinga Ayrah bari naje office É—in H.o.d na kaimasa wannan file kinji, yanzu zan dawo" "Toh aunty Suhailat sai kin dawo" fita ta yi ta barta a office É—in haÉ—e hannuta biyu ta yi akan kuncita tun É—azu babu abinda ta ke tunawa sai Mamata ko wane hali ta ke ciki yanzu
lumshe idanunsa ya yi ya na jin wani irin ya na yi a jikinsa gaba daya jijiyoyin kansa sun tashi, p.a ce ta turo kofar tashigo sai da ta ambaci sunansa sau uku bai É—ago ya kalleta ba hakan ya sa ta ajiye file É—in da ke hannuta ta yi ta fita ta na tunani ko menene ya faru da Mdee zama ta yi akan kujera da ta kasance mallakinta
Shin kodai taje ta faɗawa Mdee tana son zuwa gida Saboda Mamata bata da lafiya? a'a gasky bazata iya ba tashi ta yi ta fita dan zuwa cikin lambu da ke Company, tana zuwa ta zauna kan fararen kujerin da ke gun lumshe idanunta ta yi ta na jin wani irin ya na yi shiba damuwa ba shi ba farin ciki ba "Ya Allah ka sa Mama ta na cikin ƙoshin lafiya" ta furta hawaye na bin gefan fuskarta "Ameen" taji an ambata a bayanta da sauri ta buɗe idanunta wanda su ke kawo ruwa Oga Abdul ta gani tsaye ya haɗe hannusa biyu akan ƙirji murmushi ya sakar Ma ta ya na zama akan kujera da ke gefanta fine girl ya faɗa ya na murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa kawar da kanta ta yi da sauri kuma ta miƙe ta nufi hanya fizgota ya yi ta faɗa jikinsa, ƙoƙarin kwacewa ta ke amma ina gaba ɗaya ya ruke ta cizo ta gartsa masa da sauri ya saketa ya na dafe gun da gudu ta fita a wajan ta na haki dafe ƙirjinta ta yi ta na ambata sunan Allah
Office ɗin Suhailat ta shiga ganin har lokacin bata dawo ba ya sa ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi zama tayi akan kujera shin wananan wane kalar bala'i ne