← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom ɗinta dan shiryawa ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa" Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun bashi ciwon kai.

Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni kawai ji nayi ina cikin nishaɗi" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin ɗakin na su kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin ɗakin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako. Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi sha'awar cinta😁 bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi "Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daɗi sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci

Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar jan luck ɗin ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buɗe ta kasa drive ta ce ya buɗe ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buɗe ma ta ko hmm" shiru ya yi ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buɗemin ba" dariya Jiddah ta yi ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buɗe ma ta, da sauri ta shiga ta na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida da sauri Yusra ta fita ta yi apartment ɗinsu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faɗawa kan makeken gadon ta yi ta na sauke numfashi

Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta

Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta "Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daɗe dan anjima akwai inda zamu" "Thank you sir" ta faɗa tana murmushi

Da sauri ta ke sauka daga kan stap É—in ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta "Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faÉ—a cikin hasala tana isa ta sameta zaune ta na dube dube a laptop.
Zama tayi a kusa da ita murmushi Suhailat ta yi "Jiya ina ki ka shiga ban ganki ba" "Da wuri mu ka tafine shiyasa" "Ohk wai ni kam na tambaye ki man" "Eh ina jinki" "Kina zuwa sloon kuwa?" girgiza ma ta kai ta yi alamar a'a "Gaskiya toh ya kamata yau na kai ki saloon naga idan angyara miki gashi ya zaiyi" murmushi ta yi kawai mikewa ta yi tana kama hannuta "Zo muje kinga mu tambayi Mdee ko zai bari" tashi ta yi tabita su ka fita, su na isa Suhail ya É—ago ya na kallonsu "Sir dan Allah idan ba damuwa zamu fita da Ayrah" wani irin kallo ya ma ta da sauri ta sunkuyar da kanta "Idan kunfita kuje ina" taji ya ambata "Saloon" ta bashi amsa shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Shikenan muje na kaiku murmushi jindaÉ—i su ka yi su na kallon juna

Baya suka buɗe za su shiga su duka "Ni ɗin drive ku ne da zaku shiga baya" "Sorry sir" "Ayrah ki shiga gaban kinji" "A'a Aunty Suhailat ke ki shiga" wani kallota ma ta wanda ya sa ta saurin buɗe gaban ta shiga, murmushi gefan baki ya yi dan dama hakan ya ke da buƙata beauty saloon su ka isa da ke garin abuja babban gurine na musamman wanda ya kayatu, akwai wajan saloon da lalle, wajan make up duk agun, fitowa su ka yi su ka nufi wajan saloon ɗin zama ya yi a gurin su kuma su ka karasa cikin wani glass "Madam gulo ce ta fito ta na tambayarsa abun da ya ke so nuna ma ta su Ayrah ya yi dake zaune cikin glass "Ki tambayesu" ya faɗa ya na ɗora kansa a jikin kujera lumshe idanunsa ya yi wani irin bacci ke fusgarsa
Suhailat ce ta basu umarnin su yiwa Ayrah saloon mai kyau sannan ida sun gama su ma ta kalba kanana zaro idanu ta yi ta na turo baki "Allah ni Aunty Suhailat kar'amin kitso kedai kam anyi raguwa wallahi" "Dan Allah Aunty Suhailat" ta faɗa cikin shagwaɓɓa "Allah fa ke daina marairaice wa dan sai an miki" shiru ta yi kawai ɗago idanunsa ya yi dai-dai lokacin da ake warware mata kai masha Allah ya ambata cikin cool voice ɗinsa, cikin muntina da ba su wuce 30 ba aka gama mata komai bakaramin kyau kalba ta ma ta ba zubawa kan nata idanu ya yi tabbas yarinya Allah ya yi mata baiwa kala- kala "Sir" da sauri ya kalleta ya na mamakin yaushe ta iso nan? mikewa ya yi su ka nufi ƙofar fita su na shiga kai tsaye su ka sauke Suhailat a gida kallon Ayrah ya yi "Kin yi kyau sosai da wannan kitso" murmushi ta yi tana mamakin yaushe yaga kitson na ta "Kina mamakin yadda nagani ko?" ɗaga ma sa kai ta yi dan har ga Allah ta yi mamaki

Buɗe murfin ta yi ta shiga ɗa ga ma ta hannu ya yi ya na murmushi, ta na shiga gida ta ga babu kowa a tsakar gida karasawa cikin ta yi Inna lilahi wainna ilayi rajiƙun
Mai ta ke gani haka

Ina ma'abota sun littfin a wani Company na ce ko kinsan har yanzu ba'a fara wasan ba ko kinsa cewa yanzu ne ƙadarorin Ayrah za su fara ohh ya rabbi ki hanzarta biya danjin yadda zata kaya
Idan kinyi shirin biya
9165855674
Hauwau Umar Abdullahi opay.
Ki turomin evidence ta wannan Number
09165855674
Karki bari a baki labari yar uwata.. littfina ₦300 ne babu tsada
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

A WANI COMPANY

BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

fallow my account
Arewabook@hauwauomar05

Mikiya writer's Allah ya cigaba da haÉ—a kanmu sharin mutum da Aljan Allah ka tsaremu tabbas farin jini jama'a Allah ne ya bamu kuma muna alfahari da haka domin mu masoyan mu akullum sune mu mune su masoyan mu abun alfaharin mu.

Page_14_15

"Good morning Ammi good morning ya Abrad" "Morning dear" Ammi ta faɗa. Ta na gamawa ta miƙe da sauri tana sumbatar Ammi fita tayi waje, samun Yusra ta yi tsaye ta na jiranta hararata ta yi "Wai ke kullum sai mutum ya ta jiranki?" "Sorry sisna ta faɗa ta na kama hannuta, drive na isa ta fito da sauri ko jiran Yusra batai ba.

Tana gama shiryawa tafita. A ƙofar gidan ta ga motar Mdee da sauri ta buɗe ta shiga murmushi yayi yana kallonta suna isa ya fito zuwa cikin Company

A hankali yake ziro santala-santalan ƙafa funsa daga kan makeken bed ɗin sanye ya ke cikin fararan sleep dress white masu matukar kyau da shaƙi badroom ya nufa dan watsa ruwa.

Yana fitowa ya nufi wajan mero tabbas Abrad kyakyawa ne farine tass ƙwayar idanunsa blue sai bakinsa da ya kasance ƙarami pink color girarsa ta haɗe da sajen fuskarsa, yana da fafaɗan ƙirji jikinsa a murɗe Kamar mai gym lotion ya ɗako masu kyau da ƙanshi shi kansa salon shafa man abun kallone a wajan Abrad. Ya na gamawa ya taje kansa White ribom ya ɗako ya haɗe kansa dashi

Yana gama shiryawa ya fito kai tsaye part ɗin Ammi ya isa tana ganinsa ta saki murmushi da sauri ya ƙarasa ya na kwanciya akan cinyarta wata irin nutsuwa yaji
tana ratsasa shafa kansa Ammi tayi "Son ya kamata kaje wajan Momy ku ka gaidata" shuru yayi kamar bai jiba "Da kaifa na ke" "Please Ammi nifa bason shiga sabgar matarcen nake ba" "Naji ni dai nace kaje idan kuma bazaka jeba kai kasani ta faÉ—a tana turesa" "Sorry Ammina Insha Allah idan na fita zanje" murmushi tayi "Yawwa ko kaifa"

Company
Chapter 11 · 0% Book details