← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mrss Afif ne ya dubesa ya ce" muna bukatar gine mai kyau na zamani mun yi la'akari da kaf Company babu kamar wannan shiyasa muka kawo kwangila mu nan" haka suka cigaba da tattaunawa tun tana sa ran zai taho su tafi har ta gaji meƙewa tayi ta fita ganin ta fita ya sa hankalisa ya dawo kanta ko ina zata sai ya ji ya kagu su tashi daga meeting ɗin tana fita kai tsaye wani lambu mai kyau ta karasa lambu cike ya ke da bishiyoyi daban daban Kamar su mangoro, gwaiba, dabino banana, da dai sauransu ai ta na ganin bishiyar mangaro ta karasa da sauri ta na murmushi dan ta na matukar kaunar mangoro wani dutse ta gani agun da sauri ta karasa ta na jefawa ganin ya ƙi faɗowa gashi ta gaji ya sa ta zauna agun tana haɗe rai Suhail da fitowarsa kenan ya na nemanta security ne ya ce masa ya ganta ta shiga lambun cen nufar gun yayi ya na zuwa ya ga ta haɗe hannu biyu a kumatu ta na hawaye da sauri ya ƙasa ya na tambayarta abunda ya faru nuna masa mangoro tayi kuma har lokacin ta na hawaye murmushi yayi kawai ya kira wani security bashi umarni yayi akan ya ciro masa mangoro da yawa ya kai masa mota ai ta na jin haka ta miƙe ta na murmushi jindaɗi "toh taso muje ko" babu musu ta bisa suka fita a lambu suna shiga cikin motar ta zauna lokaci zuwa lokacin sai ta leƙa ganin har yanzu security bai tahoba ya sa ta ƙara turo baki "menene kuma toh?" ta ce" bashine har yanzu bai tahoba" "ke kuma rashin haƙuri" juyar da fusakarta tayi ta na ƙara turo baki murmushi kawai yayi security na zuwa ya buɗe boot ya saka musu zagayowa yayi "sir an saka a boot" okay ya bashi amsa drive ya ja suka fita kai tsaye gida ya kaita suna isa ya sa aka ɗako mata ledar mangoro mai uban yawa sai murmushi take kamawa tayi ta na shiga cikin gidan sakin baki Mama tayi tana kallonta ganinta ruƙe da uwar leda ta ce "ke ko Menene acikin wannan ledar?" "mangoro ne" ta bata amsa tana murmushi "wato kefa na fahimci ma ba aiki kike ba a Company wallahi kawai shirma kike" turo baki tayi ta na shiga ɗaki da abunta tashi Mama tayi tana bunta a baya zama tayi akan tabarma ta na buɗe ledar "kuma fa walloh Mama ya nuna mangoro" "eh gashinan ai nagani sai ki bada himma kisha" ɗauka tai zata kai baki "amma ai kya wanke ko?" dafe kai tayi ta na dariya "wollah ni nama manta ana wani wankewa" ta ce" dama ya za'a yi ki tuna tunda yau ala ya haɗaki da mutumnin ki"

Suhailat ganin har yanzu Ayrah bata zoba kuma gashi lokacin ta shi ya kusa ya sa ta miƙe dan shirin tafiya gida ta na fitowa taga p.a ta sako daga saman "amma yawa Ayrah fa?" kallon sama da ƙasa tayi mata kafin tace "wacece kuma haka?" shiru Suhailat tayi bata sake cewa komai ba dan ta fahimci p.a bata da mutunci ko kaɗan kama hanya tayi tai wuce warta

"Ayrah!! Ayrah!! ki tashi daga bacci nan kin san fa babu kyau bacci yamma ko tun da kika dawo kike ta bacci ko abinci baki nema ba" buÉ—e idanunta tayi ta na kallon mahaifiyata

A hankali ya ke sauka daga matata kalar bene sanye ya ke cikin white cuz ya haɗe gashinsa guri ɗaya farin ne tass gashinsa ya sauka har gadon bayansa da wani irin sauri security suka nufosa suna isowa gun gaba ɗaya suka rusuna ɗago kai yayi yana kallon su ya salam kyau iya Kyau kyakyawa ajin ƙarshe sanye yake da farin glass a fuskarsa gefan sa wata mata tace wadda aƙala zata haura shekaru (45) itama fare tass kamar dai shi sanye take cikin Black abaya mai duwatsu tayi rolling da belt na abayar hannuta ruƙe ya ke cikin na haka suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa suna isa bakin motar aka buɗe musu suka shiga kai tsaye kata faran gida dake maitama hills estate ya salam gidane iya gida girman gidan ya zarce misali gaba ɗaya gidan zagaye yake da security ta ko ina mai gadi ne ya buɗe get ɗin da jerewa motocin suka yi zuwa cikin gidan tun kafin su gama parking ta fito da gudu ta na ihu duk da tsakanin cikin gidan da pearking lot da nisa amma hakan bai sata ta howa da gudu ba ta na murna "Oyoyo Ammina Oyoyo ya Abrad" shine kawai abun da take furtawa ta na gudu murmushi yayi kawai ya kalli Ammi itama kallon na sa tayi da sauri ta faɗa jikin Ammin ta na murmushi cen kuma hawaye ya fara zuba akan fuskarta "Ammi shine kuka tafi kuka barni ni kaɗai ko?" "ohh Jiddah toh yanzu kuma menene abun kuka ai gashi mun dawo ko?" gyaɗa kai tayi ta na kallon Abrad jan hanci ta yayi ya na cewa "rigimama Ammi" murmushi tayi ta na turo baki "nifa fushi na ke da kai" "kaina bisa wuya na idan kikai fushi da ni ina zan kama" ya faɗa ya na yin gaba abunsa dan shi bai cika yawan magana ba wananan ɗin ma yayi ta ne kawai wani haɗaɗan falo ya shiga mai tsanani kyau irin falon nane da ko gidan shugaban ƙasa ba a samunsa a hankali ya zauna a kan kujera da ke gun ya na lumshe idanunsa wani irin sanyi ne ke ratsa masa zuci yau dai gashi ya dawo Nigeria duk da badan Ammai taje ta tawo dashi bana babu abun da zai dawo da shi

Ammi kama hannu Jiddah tayi suka shiga na su apartment É—in sai surutu ta ke kamar redio dan Jiddah badai magana ba

Ayrah fitowa tayi cikin ƙanan kaya masu kyau da shaƙi kallonta Mama tayi tai murmushi "kin yi kyau sosai" murmushi tayi ta na zama akan tabarma "wallahi Mama na ƙagu gobe tayi naje aiki saboda za'a bani salary na" murmushi Mama tayi "waya ga su Ayrah da salary" wata dariya tayi mai cike da nuna zallar farin ciki ta

Tashi yayi ya haura sama ohh ya rabbi ashe ba komai na gani a ƙasa ba dankareren falone shima na alfarama bedroom ya shiga dan watsa ruwa

Ɗaure ya fito cikin white towel iya gwiwa hannusa na ruƙe da karami wanda ya ke tsane kansa da shi

Wani irin taunar cingom take mai bada sauti kallon wata ƙarama yarinya tayi wadda baza ta fi Sa'ar Jiddah ba "kinji na gaya miki wallahi kika sa ke kikaje wajan mutsiya tan cen ranki sai ya bacci sakara kawai" "rabi da ita Momy ita yarinya wallahi na fahimci tafi son Ammi" "eh ɗin nafi sonsu kuma ni wallahi duk abinda zakuce sai dai muce haka kuri ni dai wallahi Momy akullum ba zan daina faɗaminki kiji tsoran Allah ba kuma kisan zaki mutu" da sauri Momy ta bige mata baki "zaki rufemin baki ko kuwa sakarar yarinya sai anyi magana ki farawa mutane wa'azi angaya miki mu bamu san abunda ya dace ba ne?" tashi tayi ta haura sama tana ƙunƙuni
"Na fahimci yarinya nan sai na shiga dukanta zata dawo hankalin ta" "kema ce Momy tutuni nagaya miki ki kaita wajan durfus kawai ya rufe miki bakinta wallahi idan ba haka ba duk wani shirinki sai ta tarwatsa sa yanzu gashi su ya Abrad sun dawo Nigeria kuma da kince ance miki ba zai taɓa dawowa ba" shiru Momy tayi ba tace komai ba dan itama al'amarin duk ya ɗaure mata kai

Niko nace Allah kenan babu wani wanda ya isa yayi abunda Allah bai ba hajiyata[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

A WANI COMPANY

BY.
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT.

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

Fallow my account.
Arewabook@hauwauomar

Page_16_17

Be ce mata komai ba ya buÉ—e idanunsa "Kin É—auka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faÉ—a ta na fita dan zuwa office É—in Suhailat

Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana kallonsa ganin da marron ɗin cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke zuwa Company? ta faɗa ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh insha Allah zan faɗamata"

Tsaye ya ke ajikin window apartment ɗinsa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai kyau haɗe gashinsa ya yi ya ɗaure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaɗi yanayi ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin bedroom ɗin ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta biyo ni zata dakeni ba dan na ɗauka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma ka ke min faɗa ko ya Abrad" ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a ɗakin ta na kuka
Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta "Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faÉ—a" "Da ya miki faÉ—a ke me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa"
Chapter 10 · 0% Book details