← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afusace ya ke maganar wanda kana gani kasan ransa ya ɓaci sosai da sauri kuma kamar wanda aka tsikara ya miƙe yana gyara zaman cuz din dake jikinsa fita yayi cikin sauri security dake wajan suka rufa masa baya daga musu hannu yayi dan baya buƙatar kowa yanzu a kusa da shi wani haɗaɗan ɗaki ya shiga mai tsananin kyau cire rigar dake jikinsa yayi ya kwanta a kan katafaran royal bed ɗin dake shimfiɗe a ɗakin gaba ɗaya kansa ya ɗau zafi ya ma rasa me ya kamata yayi shin idan haka ta kasance menene makomarsa kenan? anya zai yarda ya tafi wani guri No ya faɗa yana girgiza kansa gaba ɗaya ɗimuwa da tashin hankali sun wanzu akan fuskarsa
Da sauri ya tashi yana nufar badroom, ya na shiga ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi dan-danan kuma wata nutsuwa tafara saukar masa, lumshe idanunsa yayi a hankali ya na sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

# SQUAD 2024

A WANI COMPANY

BY

HAUWAU OMAR
...CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

fallow my account Arewabooks

Arewabooks@hauwauomar05

Page 4,

"Ayrah" "Ayrah wai me kike har yanzu baki fito ba kin san dai ba tsayawa jiranki za'a yi ba ko" da sauri ta fito daga ɗakin tana gyara zaman zumbulele hijjab ɗin ta da ya sauka har ƙasa tayi matiƙar kyau. "Mazaki wuce kije gidan alh hadi yana cen yana jiranki tun ɗazu" da sauri ta kama hanya ta tafi har tayi gaba ta dawa tana kiss ɗin Mamanta akumatu murmushi Mama tayi tana ɗaga mata hannu "Allah ya tsaremin ke dear" "ameen Mamana"

Tafiya take cikin sauri duk da ba wani sauri ta'iya ba tayi tafiya sosai kafin ta karasa gidan tana shiga taga habib da'alama shima fita zai yi da sauri ya karaso wajanta yana murmushi "a yau Ayrah ce a gidan na mu?" "eh wllh ya habib kwana biyu" "kin guje muba" ya faɗa yana dariya murmushi tayi tana sun kuyar da kanta ƙasa "ki maza ki shiga ciki dad yanan yana jiranki tin ɗazu" da sauri ta nufi cikin falon tana shiga tagasu zaune kan kujerin falon tsugunawa tayi har ƙasa tana gaidasu amasawa suka yi da fara'a "sai mu wuce ko kar muyi late dan yanzu Mdee da aka sauya baya da sauƙi kwata-kwata"

Kama hanya sukayi zuwa wajan parking space shiga cikin motar yayi hajiya da kanta ta buÉ—ewa Ayarh motar ta shiga..
Suna isa ta tsaya tana karanta sunan Company

* JULIUE BERGER NIGERIA PLC*

Company Juliue Berger Nigeria Plc yana hedikwata a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Company ya kasan ce wani kamfanin gine-gine da ke aiki a fannoni daban-daban na gine-gine, musamman a fannin gine-ginen tituna,

Akwai kamfanoni da dama a Najeriya da ke da alaka da kamfanoni a kasashen waje, ciki har da kamfanin Juliue Berger Nigeria Plc. Kamfanin ya kasance yana aiki tare da kamfanoni daban-daban a duniya, ciki har da na Austiralia, don gudanar da ayyukan gine-gine da kuma bayar da kayayyaki.

Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su isa left zaro ido tayi tana kallon alh hadi dan ita tun da uwarta ta haifeta bata taɓa ganin irin wannan abun ba murmushi yayi yana nuna mata gurin "shiga muje kinji daughter babu abunda zai miki" shiga tayi a tsorace jin sunyi sama ya sa tayi saurin rintsa idanunta tana ambatar sunan Allah
Dai-dai left na biyar suka isa fita yayi tana biye da shi nocking yayi a jikin wani office mai kyan gaske, asama an rubuta General Mdee Suhail . P.a din dake zaune a Office din farko ce ta basu umarnin shiga shiga suka yi bakinsu dauke da salama zama alh hadi yayi akan kujera da sauri p.a ta miƙe tana gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska wani banza kallo ta watsawa Ayrah duk da bata santa ba amma gani farko taji ta tsani yarinya da sauri Ayrah ta sun kuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta

Tashi yayi yana ruke da hannuta suka shiga cikin katafaren office ɗin wani mugun sanyine ya daketa da sauri ta kan-ƙame jikinta suna shiga ya nuna mata wajen zama da kecen nesa karasawa yayi wajan Suhail da fara'a ya miƙawa masa hannu shima cikin girmamawa ya basa hannu sukai musabaha dan Suhail duk wulaƙancisa yana matukar girmama manya bayan sun gaisa ne yake faɗa masa ga yarinya da yace zai kawo murmushi yayi yana kallon yarinya wani irin faɗiwar gaba yaji da sauri ya kautar da idanunsa daka kanta .

"Shikenan babu komai ka koma bakin aikinka zan mata inter biyu" godiya ya masa ya nufi ƙofar dan fita tashi tayi da sauri tabi bayansa "kije wacen kujera ki zauna daughter shine zai miki inter biyu" "tom Daddy" ta faɗa tana bin inda ya gaya mata zama tayi akan kujera har lokacin kuma bai dago ya kalleta ba sai da ya gama abun da yake kafin cikin wata sanyayiyar muryasa ya ce ya sunanki

"Fatima Mahir"
ta bashi masa itama a taƙaice

Menene matakin karatunki
Secondary

"It's also an opportunity for job seekers, we are hiring young people here"

Ya faɗa a tsawace sunkuyar da kanta tayi ƙasa dan-danan hawaye ya fara ambaliya a fusakarta

Miƙa hannu yayi ya karɓi takardun hannu nata yana dubawa murmushi yayi abun ba karamin mamaki ya bataba ganin yanzu ya gama mata tsawa amma kuma ya koma murmushi "shikenan zan daukeki aiki amma kin san wane aiki zaki yi?" girgiza kai tayi alamar a'a "coffee" Zaki zama mai kawomin coffee ko da yaushe kuma ban yarda ki kaiwa wani acikin Company coffee ba in bani ba kina jina" ɗaga kai tayi alamar eh ita dai koma me zai bata ya bata in dai zata samu kuɗin da zata na siya musu abinci kuma Mamanta ta daina wankau wata takarda ya ɗauka yayi rubutu "gashinan zuwa gobe sai kizo dan fara aikinki sanan idan kin fita kicewa p.a ɗin dake zaune a Office na farko ta rakaki wajan alh hadi ki kai masa takarda" ɗaga kai tayi tana masa godiya, da sauri kuma ta fita daga Office ɗin

tana fitowa p.a taimata wani irin kallo sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana magana "dama cewa yayi kirakani wajan wanda mukazo dashi ɗazu" wani kallon banza tamata kafin tace "ke bana son iskanci da ni na shigo dake da zakice narakaki wawuya kawai" ita dai bata ce mata komai ba kuma bata ɗaga kai ta kalleta ba duk abunda suke yana kallonsu jin telephone ɗin dake kan table din nata yayi kara yasa tayi saurin ɗagawa hlo sir cikin wata irin murya mai amo ya ke bata umarni gaba ɗaya ta rikice dan bata taɓa jinsa da irin murya ba "am sorry sir Insha Allah hakan bazai kara faruwa ba" ajiye wayar yayi yana dora kansa ajikin kujera a hankali kuma ya ke lumshe idanunsa

Fita tayi ita batace mata komai ba da sauri ta bita abaya sai da suka hau left ya kai su bene na 3, in da office din alh hadi yake wanda ya kasance Office ɗin da duk wani taransaction ya ke shiga "Ga office ɗin nan zaki iya shiga" ta faɗa tana juyawa abunta hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/Ilta4xHroxoHpDTtpEW4H9

#SQUAD 2024

A WANI COMPANY

BY

HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

Fallow my account Arewabooks

Arewabooks@hauwauomar05

Page 3.

A hankali yake sauka daga matata kalar jirgin sanye yake cikin cuz maroon da sauri security suka nufesa gaba ɗaya suka gaidasa ɗaga musu hannu kawai yayi yana miƙa musu back ɗinsa gaba yayi suna binsa a baya har suka ƙarasa wajan motocin motoci ne yan uban su wanda babu mai hawa irinsu sai ɗan wane da wane yana shiga suka tashi motoci a hankali suke tafiya har suka isa cikin Sarah estate dage abuja haɗaɗan estate mai matiƙar kyau da girma dai dai gaban wani gida sukai horn wanda kaf estate ɗin babu kamarsa da sauri mai gadi ya wangale musu katafaren get ɗin suka shiga ya Salam tabbas wannan gidan abun a kallane gidane na gani na faɗa irin gidanan da ake kira da aljanna duniya gidane mai matikar girma.

Suna yin parking ko jira security su buɗe masa baiba ya buɗe ya nufi ciki da sauri wani security a cikinsu ya ƙarasa dan nuna masa komai dake gidan suna shiga cikin katafare falon wanda aƙala yayi wani gidan mai kuɗin duka a girma ya kalli security inane part ɗina shine abun da ya faɗa a taƙaice nuna masa wani apartment yayi nufar wajan yayi ya buɗe ƙofar wani haɗaɗen falon ne mai zaman kasan sa up'chear ya nufa

Tana tafe ta na murmushi gaba daya jinta take kamar anyaye musu damuwa tabbas tasan idan Ayrahta ta samu aiki zasu samu sassaucin rayuwa da salama ta ƙara sa shiga cikin gidan zaune ta ganta a tsakar gidan tayi tagumi babu abunda ke fita daga idanunta sai hawaye wata matsanan ciyar yunwa takeji gaba ɗaya ta kasa jurewa da sauri Mama ta karasa tana tambayarta me ya faru hawaye ne ya shiga sauka a idanunta ajiye abun da ke hannunta Mama tayi tana zama akan tabarma jawota tayi jikinta ta rungume "menene yake faruwa Ayarh? me akai meki ki faɗamin?" turo baki tayi hawaye na kara zuba a idonta in dai kuka ne da shagwaɓɓa dama Ayrah number 1 wajan nan "toh Mama ba yunwa nake jiba tin dazu kuma cikina sai zafi yake min" "shine kuma kike kuka haba Ayrah mai yasa bazaki yi salati Annabi ba ki sani ba komai akewa kuka ba kuma ai yakamata kisan cewa kefa yanzu babba ce" Mama ta faɗa tana jan hancinta murmushi tayi tana boye kanta ajikin Mama "maza tashi ga abinci nan na tawo mana dashi daga gidan hajiya sarai, kici na baki wani labari mai daɗi wanda zai saki farin ciki"
Chapter 2 · 0% Book details