← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

P.a miƙewa tayi da sauri ta nufi office ɗin Abdul ta na shiga ta tuntsire da wata muguwar dariya shima dariya yayi "albishirinki?"ta ce" goro" ya bata amsa "part one dai munyi nasara saura two" ya ce" a haba dai?" Ta ce" ai dama na faɗa wallahi Sai yarinya ta gane kuranta naso ma ace bai gane menene a kujera ba kasan nan gaba menene shirinmu?" girgiza mata kai tayi alamar a'a matsawa tayi ta raɗa masa a kune "gaskiya wannan shawara taki ta matukar yi tabbas ranar muna da shan kallo a Company nan" ta ce" sosai ma kai dai kawai a zuba eyes kaga yadda zan juya rayuwar yarinyar".

Mikewa yayi ya fita office ɗin h.o.d na Company ya shiga da sauri ya miƙa ya na gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska dan duk cikin ma'aikata gidan babu wadda ya yarda da shi kamar h.o.d zama yayi ya na masa magana lokacin "ɗazu kafin na shigo Company an kashe Camera dake office ɗina menene dalilin haka?" "sorry sir ɗazu p.a ke faɗamin wai na bada umarni a kasheta saboda za'a yi wani gyara ne a office ɗin naka wannan dalilin yasa na kashe" ya ce" ita p.a ɗin ce ta faɗamaka haka?" "eh sir" murmushi yayi yana cije laɓansa na ƙasa "sir ko haka da matsala ne" ya ce" a'a babu wani matsala" ya faɗa ya na miƙewa yana fita ya koma office ɗinsa zaune ya ganta tana danna waya a zafafe ya ƙarasa in da take ya ɗauke ta da mari wani irin taurari ta shiga gani suna giftawa ta fuskarta "sha-sha-sha mara tunani duk ranar da kika sake maka manci haka kin ji na faɗami Wllh a bakin aikinki" zaro idanu tayi waje sai tajima gaba ɗaya zafin mari ya kauce idan ta bar aiki tasan rayuwarta ta shiga wani hali.

Miƙewa Ayrah tayi suka fita daga office ɗin "Aunty Suhailat amma dai kin daɗe kina aiki anan ko?" "eh gsky na daɗe sosai Ayrah tun kafin zuwan wannan Mdee ɗin" "Alokacin wani Mdee ne azalumi. Kina so na baki labarinsa? gyaɗa kai tayi alamar eh "Okay Bari mu dawo daga sallah zan baki labarin"
ta faÉ—a dai-dai lokacin da suka isa masallaci.

Bayan sun idar da Sallah zama suka yi cikin lambu dake gefan gun

"Ada idan kikazo neman aiki tofa Mdee ɗin baya taɓa yarda ya ɗauke ki aiki Sai ya lalata ki. Idan baki yarda da haka ba toh sai dai salary naki ya zama zaku raba wannan dalilin yasa yan mata dayawa a lokacin suka shiga wata rayuwa wasu daka haka kuma suka koma karuwanci. Zaro idanu tayi tana kallonta "Amma toh Aunty Suhailat ke ya kika yi?" murmushi tayi "Alokacin da na zo neman aiki Mdee ya nuna min haka babu yadda zanyi saboda ina matuƙar bukatar aiki dan dashi zan taimaki iyayena dole ina ji ina gani yake raba salary na biyu ya ban rabi duk wata hantara idan ya tashi yimin yake haka ya mai dani p.a ɗinsa dan kawai ya cimma burinsa, da yake Allah shine mai kare bawansa sai Ubangiji ya tona masa asiri aka koresa duka daga wajan aikin

"Shiyasa zakiga wasu mata idan zasuje aikin Company suyita rawa kai wallahi ya wanci Company ma aikata su ko kaÉ—an babu Allah a ransu amma fa bana ce mike duka ba" "A'a wasu dan kin san a ko ina akwai nagari akwai na banza" "Haka ne Aunty Suhailat Allah ya sa mu dace" "Ameen ya rabbi" "Sannan ki dunga kula ba kowane zaina miki murmushi ba ki zaci sanki yake a'a wani yana da manufa a kanki ki yi a hankali sister ki san da suwa zakiyi mu'amala"

Sun daɗe agun suna tattaunawa kafin su meƙe su koma ciki "Kije office ɗin Mdee ko zai buƙaci wani abun, kiga lokacin tashi yayi" gyaɗa mata kai tayi ta na nufar left ta hau

Tana isa ta gansa zaune a ya na danna lapton É—insa da'alama kuma wani abun yake, zama tayi kan kujera sai da ya gama sannan ya É—ago ya kalleta "Yau bazan samu damar kai ki gida ba saboda ina da wani aiki so zansa drive ya Kai ki" "Toh shikenan nagode Sosai" "Ita kuma godiyar ta mece?" sunkuyar da kanta tayi batare da ta basa amsaba murmushi yayi ya cigaba da abun da yake

Fitowa tayi zuwa haraba Company drive na ganinta ya buɗe mata mota ta shiga, suna isa ta sauka tayi cikin gida, ta na shiga ta kwanta akan kujera "Wash Allah Mama wollah yau na gaji da yawa" "Ke kuma aikin me kika yi da kika gajin?" "Ni fa ba aiki na yi ba kawai gajiya na yi" "Raguwa ni nataɓa gani angaji ba tare da anyi aiki ba" "Allah Mama ana gajiya" ita dai Mama murmushi ta yi ta cigaba da abun da ta ke dan tasan idan ta biye Ayrah to bazata taɓa bari ta ba
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

# SQUAD 2024

A WANI COMPANY

BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

Fallow my account
Arewabook@hauwauomar05

Page_10_11

Washegari tun wuri Ayrah ta shirya tana jiran Suhail ganin lokacin sai tafiya yake ya sa ta tashi da sauri tanawa Mama bye bye. Tana fita bakin titi ta tsaida me napeep shiga tayi tana faɗa masa inda zataje. Suna isa ta fito tana bashi kuɗinsa ta nufi bakin get ɗin security da ke gun ta gaida tana shiga ciki, sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta ƙarasa left ta hau

Tana isa office ɗin Mdee taji ƙofar a kulle nufar inda p.a take tai tana tambayarta Mdee baizo ba har zata mata masifa ta tuna magungun Mdee sai kawai tayi murmushi tana ɗaga mata gira "Yes Mdee ya je wani guri sai zuwa anjima zai ƙaraso nan so idan kinga bazaki iya jiraba sai ki koma gida sai ya dawo"

Bata ce mata komai ba ta juya tai tafiyarta abunta ƙasa ta sauka Suhailat ta gani da'alama kuma itama zuwanta kenan da sauri ta ƙaraso "Ayrah yau ke kaɗai kika zone? naga Kamar Mdee bai shigoba" "Eh Aunty Suhailat good morning" "Morning dear fatan kinzo lafiya?" "Lafiya qlau ta bata amsa yau kinga wani taro za'a yi a Company so karfe biyu kowa zaije gida sai bayan nan za'a dawo kamar 4:00 idan an tashi ki biyo ni muje wani waje dan shiryawa kinji" "a'a Aunty Suhailat zanje gida kawai sai na faɗawa Mam.. Kasa karasa maganar tayi ganin Mdee tsaye yana kallonsu da'alama kuma ya daɗe a wajan

Nufo su yayi ya na isowa wajan ya kalli Ayrah sai kuma naga ya cenza hanya yayi gaba abunsa murmushi Suhailat tayi "Maza kije ki kaima Mdee coffee kin ji" "toh tace tana bin bayansa suna isa office ɗin p.a ta gaidasa ƙasa-ƙasa ya amsa ya na nufar na sa office ɗin. Ya na shiga ta turo ƙofa ta shiga

Tunda ta shiga taga ko ɗagowa ya kalleta baiba, nufar wajan coffee tayi ta haɗa masa aje masa a kan table ɗin tayi wata tsawa ya daka mata wadda tasa gaba ɗaya hanjin cikin ta ɗaurewa "Ke wace kalar sha-sha-sha ce? kinji nace miki ina bukata ne?" ya faɗa a tsawace jikinta ne ya fara wani irin rawa dan-danan hawaye ya shiga zuba akan fuskarta so take ta bashi haƙuri amma bata da karfin haka tsaki yayi ya zauna akan kuje yana dafe kansa da hannu biyu "Ya salam" ya furta a hankali ya na rufe idanunsa shin me yake shirin aikatawa ne ohh ya Allah

Da gudu ta fita daga office ɗin p.a dake zaune takaleta tana mamaki dalilin da yasa ta fito tana da gudu tana kuka. Ƙasa ta sauka tashiga office ɗin Aunty Suhailat tana shiga ta rungumeta tana wani irin kuka numfashi tane ya fara sarƙewa dalama kuma ciwonta ke ƙoƙarin tashi Suhailat hankali ta ne ya yi mugun tashi da sauri ta kwanta da ita ta fita waje a guje ko left batai tunani hawa ba ta shiga haura bene da bibiyu gaba ɗaya ta shiga damuwa buɗe ƙofar tayi ta shiga tana haki p.a tsayawa tayi tana kallon ta ko bin ta kanta bataiba ta shiga cikin office ɗin Mdee ganin Suhailat a wannan yanayi yasa yayi saurin meƙewa yana kallonta nuna masa ƙofa kawai take ta kasa magana "Menene ya faru ki nutsi ki faɗamin" "Sir Ayrah" "Ayrah sir" tun kafin ta karasa ya fita da sauri ya na sauka ya faɗa cikin office ɗin p.a na biye da shi samunta yayi kwance idanunta a rufe da sauri ya ƙarasa ya na taɓata. Ɗaukarta yayi zuwa pearking lot tun daga nesa yake ƙwalawa drive kira da sauri ya taso ya zo ya buɗe masa motar shiga yayi yana ruƙe da ita suka nufi asibiti Company

suna isa asubiti da sauri Dr ya sa aka shiga da ita É—aki gaba É—aya Suhail ya rasa nutsuwarsa ji yayi hawaye na bin kunchisa da sauri ya saka hannu ya na gogewa ya san koma me ya faru shine sula shi yaja da baimata tsawa ba da hakan bazai faruba

Mama da ke zaune tan kaɗe gari dan bata so Ayarh ta dawo bata gama girkin ba tasan hali ji tayi gabanta yayi wani irin faɗiwa a hankali ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunan Allah laila hailla anta subuhanaka inni kuntu mina zalumin shi take ambata a zuciyarta
Chapter 8 · 0% Book details