← Book details A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

A Wani Company Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya tashi ya nufi cikin ɗakin da ke office ɗin sai da ya kusa shiga kafin ya tsaya ya na duban Ayrah "Kije office ɗin su Suhailat, kuma bayan nan ban yarda kije ko ina ba" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar toh fita ta yi da ga office ɗin kanta a sunkuye ganin p.a ba ta office ɗinta ya sa ta sa ki wa ta irin ajiyar zuciya mai ƙarfi, dan gaba ɗaya ba ta son ganin Suhailat

Da murmushi Suhailat ta tare ta "Yau sai yanzu ake ganinki" zama ta yi ta na gaidata amsawa ta yi cikin sakin fuska "Ina kika shiga yau?" "Babu ko'ina ina office ɗin Mdee" "Okay" Suhailat ta ce ta na chanza hira "ki na son wani abu ne?" "A'a Aunty Suhailat na ƙoshi" to ai ba cewa na yi nima baki ƙoshi ba, ina nufin kamar beskit chocolate da dai sauransu" murmushi Ayrah ta yi jin an ambato kayan kwaɗayi
[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ

# SQUAD 2024

A WANI COMPANY

BY
HAUWAU OMAR
CUTIE MEEYRAT

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS

Fallow my account
Arewabook@hauwauomar05

Page_ 8_9

Ana tashi ta fito harabar Companyn don tafiya gida,ko office ɗin Mdee ba ta koma ba. fitowa wajan get ɗin tayi sai da tayi kusan 5minth bata samu abun hawa ba, hakan ya sa tashiga takawa da ƙafa ta na tafiya dafe kanta tayi saboda wata rana da ake gashi ko rabi bata yi ba, jin horn a bayanta ya sa ta yi saurin juyawa zuge glass ɗin motar ya yi ya na mata wani irin kallo, sunkuyar da kanta tayi ƙasa da sauri ta na wasa da yatsun hannunta

Nuna mata motar yayi alamar ta shiga, babu musu ta shiga kuma har lokacin kanta na ƙasa suna isa ƙofar gidan na su ta buɗe ta fita ko magana bai mata ba yaja motarsa yayi gaba jiki a sanyaye tashiga cikin gidan na su ganin bataga Mama a tsakar gida ba yasa tayi cikin ɗakin, samunta ta yi zaune ta na karatu al'Qur'ani mai girma zama tayi ta na murmushi.

Yana shiga gida faɗawa yayi saman kushin ɗin gaba ɗaya yau ya gaji lumshe idanunsa yayi ya na sauke numfashi tinani rayuwarsa ta baya da ta yanzu ce ta shiga dawo masa hawaye ne ya fara zarya akan kuncinsa tabbas bashi da wani gata sai na mahaifinsa mahaifiyarsa ta tafi ta barsa tin baisan ma menene duniyar ba haka ta watsar da shi ta tafi kawai dan basu da kuɗi alokacin. Allah kenan mai azurta bawansa a sanda ya so mahaifiyarsa taci amanar Daddysa taje ta auri abokinsa kawai dan shi baida kuɗi alokacin bata damu da rayuwar da zasu shiga ba haka ta barsu kuma har yau bata wai wayesu ba tuna irin waɗannan abubuwan ya sa ya kara fashewa da kuka mai cin rai idanunsa sun yi wani irin ja abun ka da fari nan da nan fuskarsa tayi ja a hankali ya kwanta ya na wani irin numfashi aduk sanda Suhail ya tuna waɗannan abun tofa yana shiga cikin wani irin hali ne . Tun yana numfashi a hankali har ya nemin fun ƙarfinsa miƙewa yayi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi yana fitowa ya goge jikinsa da towel ne ɗaure a jikinsa ya kwanta yana rufe idanu kuma har lokacin hawaye bai daina zuba akan fuskarsa ba

Wanene Suhail?

Suhail Arif shine ai nayin sunansa asalin mahaifansa bature ne haka ma mahaifiyarsa

Austiralia. Calvary public hospital

Ihu ne ke tashi a dai-dai room 003 dake cikin hospital ɗin a hankali kuma ihu ya fara disha shewa kyakyawa mutune tsaye a bakin ƙofar idanunsa a rufe da alama yana cikin yanayi na damuwa jin kuka jariri da yayi ya sa yayi saurin shiga cikin ɗaki kwance take akan gadon na marasa lafiya daga ganin yanayi yadda take bacci zaka tabbatar da cewa a wahalce take da sauri ya karasa ya ɗauki jaririn dake gun yana rungumesa tsam a jikinsa kamar wani zai rabasa da shi sun kai tsawan muntina 20 a haka kafin ya ɗago ya kalli matar da ke kan gadon wani uban harara ta watsa masa tana jan tsaki nufar idan da take yayi da sauri ta dakatar da shi da hannunta "karka sake ka kusanci inda nake Arif saboda baka da wani amfani a gare ni cikin dake jikina ne na haife maka kuma na barmaka shi har abada bana fata ka faɗa masa yana da wata uwa wadda tai kaman ceceniya da ni talaka kawai wllh nayi nadamar auran matsiyaci kamar ka kuma ina so kasani aurena da Mahabub babu fashi" ta faɗa tana tashi daga kan bed ɗin ko damuwa da ciwon da jikinta ke mata bata yiba ta nufi hanyar fita da sauri ya karasa gabanta ya na haɗa hannuwansa biyu alamar taji tausayin su ratsesa tayi ta fita tana jan tsaki durkushewa yayi ya na fashewa da wani irin kuka mai cin rai tabbas Mahabub ya cuceshi ya ci amanarsa yanzu da gaske dama Sarah zata iya barinsa saboda kuɗi shin me yasa bata ji tausayin ɗan da yazo duniya ba yau duk wannan maganganu shi kaɗai ya ke yinsu kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya ɗauki jaririn nufar hanya futa yayi daga hospital ɗin gaba ɗaya

Haka rayuwa ta ciga da tafiya Suhail ya taso wajan mahaifinsa kullum shi yake kaisa makaranta ya ɗaukosa bayaso ko wani ƙwarzane ya taɓa masa ɗa watarana ya dawo daga school ya nufi parlon su jun haya niya yasa yayi saurin tsayawa ya na saurare "Arif kenan ban fa na zo ne dan na tambayi ya kake ko ya ɗanka ya ke ba a'a nazo ne dan naji ance kayi kuɗi shine nazo dan kabani nawa kasan tunda dai dani akasha wahala" da wani kallon ya watsamata "Tabbas baki da imani Sarah baki ko tambaye ni ya ɗan ki ba sai Maganar dukiya abar banza wannan damuwarka ce ni koma ya yake bai dameni ba to bazan bayar ba Sarah ina lokacin da bani da kuɗin gudu na ki kai kuma ki maza ki fita a gidanan kafin nasa security su fitarmin dake" ganin da gaske ya ke babu wasa yasa tayi ƙwafa tana fita a ɗakin Suhail da idanunsa ke zubar da hawaye ya tsaya yana kallonta tsaki taja tayi gaba abunta da gudu ya shiga cikin parlon yana faɗawa jikin dad ɗinsa numfashinsa ne ya fara sarƙewa da gudu dad ya ɗauke sa zuwa hospital ɗin dake cikin gidan tun daga wannan lokaci Suhail ke fama da ciwo a zuciyarsa har izuwa wannan lokaci.

Wannan kenan.

Sai kusan la'asar ya tashi a bacci miƙewa yayi yana ambaton sunan Allah, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya gabatar da Sallah.
Mama ce ta dubeta tana murmushi "yau kin daɗe Ayrah lafiya?" murmushi tayi tana bata labarin abun da ya faru "ke yanzu taya zaki iya zuwa gida dama a ƙafa karki kuskura ki ƙara wannan ganganci" "tom Mama insha Allah". "Kin san kuwa su Habib sun tafi yau ya ce na ce miki zai yi missing ɗin ki sosai kuma wai yanan zaizo ya ɗaukeki ku koma cen tare" murmushi "Allah sarki ya Habib nima zanyi Miss ɗinsa sosai Mama".

Washegari da wuri ta fita dan karta ɓata masa lokacin tana fita kuwa ta gansa cikin mota ganin kamar babu drive yau ya sa abun ya bata mamaki buɗe baya tayi zata shiga jin muryasa tayi yana magana "kenan niɗin drivern kine da zaki wani shiga baya?" fasa shiga bayan tayi ta buɗe gaban ta shiga.

"Dole ne kayi taka tsantsan saboda kar Mdee ya gani ta camera" murmushi yayi "haba wai bana ce miki na kashe camera office ɗinsa ba" murmushi kawai tayi suka cigaba da zuba abun ya a hankali ya buɗe office ɗinsa ya shiga itama shiga tayi ta nufi kujera ta zauna "kawomin coffee" miƙewa tayi dan kawo masa jin ta kasa tashi akan kujera sai ƙokarin tashi take amma abu ya gagara ganin tana ta ko kawa ya sa ya ce "me yake faruwa?" ɗago idanunta tayi wanda ya fara zubda ruwa "na kasa tashi" "what kin kasa tashi kamar ya ba yanzu kika zauna ba?" "Allah da gaske nake" ta faɗa hawaye ne ke ambaliya a fusakarta ganin tana kuka yasa ya miƙe dan ganin meke faruwa saka hannunsa yayi ya janyota amma ya ga ko motsi bata yiba durkusawa yayi dai-dai kujera yana dubawa murmushi kawai yayi ya nufi cikin wata drowa hannusa ruƙe da wata roba ya dawo ganin ya na zuba mata ruwa a jiki yasa ta fashe da kuka "sheet" shine abun da ya ce kin shirun tayi ta cigaba da kukanta ƙara janta yayi ta ko faɗa jikinsa wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce sa sai yaji Kamar ya taɓa shork da sauri ya rabata da jikinsa ya na komawa ya zauna "kije office ɗin ƙasa zan nemaki anjima" tana sha shekar kuka ta fita wata irin dariya p.a ta tintsire da ita a lokacin da tazo wucewa ita dai bata kobi ta kanta ba ta fita abunta
Suhailat ganin hawaye akan fuskarta ya sa ta miƙe da sauri tana rukota "menene ya faru Ayrah?" hawaye ne ya kara zubowa "ki yi shiru Please ki faɗamin kinga kin tayarmin da hankali" bata labarin abun da ya faru tayi shuru Suhailat tayi tana nazarin abun kafin tayi murmushi kawai ta bar magana "to kiyi shiru kinji ina ga wani abune a wajan" goge mata hawaye dake fuskartata tayi ta na cewa "yauwa ko kefa nifa sai nagama kamar idan kina kuka kinfi kyau wollah" murmushi kawai tayi tana boye kanta akan cinyarta.
Chapter 7 · 0% Book details