← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsawon minti biyu Aysha tana jan fasali kamar bazata tanka ba, shikuma har wannan lokacin bai gaji da tsugunno a gabanta ba.
“Allah ya bada sa’a”
Ta fada a gajarce, saboda lura da ta yi idan har ba ta amsa masa ba ba zai tafi inda za shi ba.
“Lokaci yana qara tafiya fa"
Ta fada a sanyaye sannan ta dago Fuskarta a hankali ga zube Idanunta cikin nashi.

“Amin.”
Ya amsa yana qoqarin kwaikwayon irin maganarta, yana ja da baya yana qoqarin ficewa daga falon ta sake juyo da fuskarta tana kallonshi, karaf suka hada ido a lokacin da yake qoqarin ficewa, tattausan murmushi watsa mata gamida motsa bakinsa da alamun
“I Love You”.
Ba ta san loakcin da ta maida masa da martanin murmushi ba, haushin kanta ta fara ji ganin cikin qanqanin lokaci wani Da Namiji yana neman canza mata tunani, bayan kuma a da babu jinsin halittar da ta tsana sai ‘ya’ya Maza.

Abdul yana tsaye a daidai gurin da wadanda suka tsinci gawar Sadiya suka tabbatar masa nanne dai dai inda suka tsinceta, kallon gurin yake a nutse yana nazari a cikin zuciyarshi, sannan daga bisani ya umarci Sajen Na Lado ya daukar masa hotunan gurin da ‘yar qaramar kyamarar da suka je gurin da ita.
A nan ya umarci mutanen su jira shi, sannan ya suka fara zagaye cikin kangon gaba daya ko zai samu wata shaida da za ta taimaka masa don samun sauqin gudanar da bincikenshi.

Da ganin cikin kangon an dad'e da fara ginin kuma mai shi sam bai da niyyar qarasawa, domin wasu guraren duk sun yi ciyawa luf-luf, kangon yana da lungu da saqon da zai yi matuqar taimakawa gurin boye masu aikata 6arna, wani lungu daga cikin kangon duk abubuwan shaye shaye ne wadanda aka gama amfani dasu.
Duk inda suka shiga yana umartar Sajan ya dauki hoton gurin, da haka har suka gama zagaye cikin kangon gaba daya, sa’annan suka dawo gurin da aka tsinci gawar Sadiya in da suka bar mutanen a nan.
Abdul yace dasu,
“Babu ko wani dan qyalle ko wani dan abu da kuka tsinta a lokacin da kuka tsinci gawar yarinyar?"
Ya maimaita a karo na barkatai dukda tun tambayar farko sun tabbatar masa babu abinda suka tsinta a gurin.
Suka amsa masa da cewa
“Babu abinda muka tsinta ranka ya
dade”
Ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace
“Nagode qwarai da hadin kan da kuka bani, idan ina buqatar sake ganawa daku zan nemeku a gaba.”
Ya fadi hakan bayan ya miqa musu hannu daya bayan daya sukayi musabiha a tsakaninsu.
Suka amsa da
“Muma muna godiya ranka ya dad'e, kuma duk lokacin daka dawo qofa a bude take a garemu Insha Allahu"
Fuskokinsu cike da Murmushi, suna masu jin dad'in yanda Inspector yake ganin girmansu duk da yanayin talauci daya bayyana quru-quru a jikinsu.

Daga Zango kai tsaye Asibitin da aka binciki gawar Sadiya suka wuce, gurin babban likitan ya nufa, bai sha wata wahala ba gurin samun lokacin ganawa dashi ba duk da dumbin ayyukan da suke gaban likitan, kasancewar ranar Monday ce tushen aiki.
“Dr. barka da aiki.”
Likitan ya amsa da
“Barkanmu dai Inspector, ya kuma qarin haqurin rashin da muka yi?"
Likitan ya sake yi masa ta’aziyar Sadiya domin tun a ganin farko ya gane fuskar Abdul a matsayin dan'uwan Sadiya wanda suka je gurinshi tare da D.P.O.
Abdul yace,
“Alhamdulillah Dr. nagode qwarai"
bai jira likitan ya qara cewa komai ba ya cigaba da magana kan abinda ya kawoshi.
"Dr. abinda ke tafe dani shine, a matsayina na dan'uwa ga Marigayiya kuma Jami’in tsaro, ina buqatar yin bincike don gano wadanda suka aikata wannan laifi, shiyasa nazo gurinka ko zan samu abinda zai taimaka mini gurin bincike na, kuma ina buqatar duk wata shaida ta binciken da kukayi a kan abinda ya faru da ita"
Dr. ya ce, “Gaskiya ka yi tunani mai kyau Inspector, domin irin wadannan azzaluman kamata ya yi a ringa zaqulo su ana miqasu ga hukuma suna fuskantar hukunci dai dai da abinda suke aikatawa, Ubangiji Allah ya baka sa’a. kuma duk lokacin da kake buqatar wani taimako a shirye muke da mu taimaka maka, bari na dauko maka File din binciken namu.”
Dr. na gama fadin haka ya miqe ya nufi wani kabot dake girke a jikin bango Office din, cikinsa dauke yake da fararen takardu masu matuqar yawa, nan take ya zaqulo wani File ya duba jikin File din sannan ya koma mazauninsa.

Karo na uku kenan da kira yake shigowa cikin wayarsa yana katsewa duk da yaga sunanta tangaran a kan screen din wayar, sai a karo na hudu ya dauka cikin fada fada
“Kina nufin yauma bakiyi attending lectures ba kenan? Duk da cewa yau Litinin?"

Sai da ta yi murmushi a can daya bangaren, sannan ta kalli Hidaya da take tuqa motar ta ce,
“Ba haka bane My Lovely, yau bani da lectures din safe sai yamma, shi yasa na yi tunanin kar6ar safayar makullin gidanka da yake hannun Mummy don zuwa yi maka sanitation"

Duk da cewa Namijin Duniya ne sai da hantar cikinshi ta kad'a, domin yasan mosoyiyarsa a dai dai wannan lokacin tana kwance a daya daga cikin Bed Room dinshi tana kwasar barci cikin kwanciyar hankali. yanzu kuma Yasmin ta nufi gidan, me zai faru idan Yasmin ta yi arba da Aysha a gidanshi? Da kyar yayi karfin halin fadin
“Haba dai keda shekaran jiya aka kwance miki hannunki amma shine har kike tunanin zuwa gyaran gida? ki barshi kawai Nagode, zuwa last week idan kin qara samun sauqi da kaina zanzo gidan in dauke ki"
Ya fadi hakan ko zai cimma nasarar dakatar da Yasmin din daga kudurinta.

“Kar ka damu Lovely Yaya, ai ina tare da Hidaya zata taimaka min, kuma hannun ya yi sauqi sosai…”
Cajin wayarta ne ya qare gaba daya, don haka ta yi murmushi tana ba wa Hidaya labarin yanda suka yi da gogan nata.

Kya6e baki Hidaya tayi bayan ta kauda kanta gefe daya tace
"To ko dai komawa gida zamuyi ne tunda naji kamar baiyi murna da zuwan namu b”

“Ba haka bane.”
Ta katsse Hidayar da sauri don jin tana neman yiwa mijinta mummunar fahimta.
“Kinsan irin tsananin so da qaunar da Yaya Abdul yake min, da kuma ganin shekaran jiya aka kwance daurin karayata, don haka sam baya son ina yin aikin da zai wahalar dani, ni kuma na yi niyyar samun albarkar Mijina a yau, so karki damu cigaba da tuqi kawai mu isa gidan da wuri”

Hidaya tace, “Ni kaina shaida ce a kan irin son da yake miki, da farko ban fahimci abinda yake nufi ba sai yanzu da kikamin fashin baqi, ina fatan ranki bai 6aci ba?”

“Laaaa karki damu, ai nasan sam baki fahimce shi bane.”
Amsar data bawa qawar tata kenan bayan ta gyara zamanta a kujera mai zaman banza kusa da Driver, yayin da Hidaya take jan motar cikin qwarewa.
Hidaya irin qawayen nanne masu kwadayi da qin fadawa mutum gaskiya a duk halin da yake ciki, tana bin Yasmin duk ta inda take so, babban burinta kada ta daina samun kyaututtukan da Yasmin take mata.
A Kaduna State University suka hadu da Yasmin, abinda yaja tsawon zamanin qawancen nasu abu biyu ne. Na farko duk abinda Yasmin take so Hidaya bata ta6a fadin aibunshi a gaban Yasmin din, takan qara kuranta abin don qara samun kusanci da Yasmin.
Na biyu kuma Hidaya yarinya ce mai tsananin qoqari a karatu, lokuta da dama ita take yiwa Yasmin duk wani aiki da za’a sasu a makaranta. Iyayen Hidaya talakawa ne na qarshe, da qyar da sidin goshi aka samu nasarar shigar da ita jami’a, lokuta da dama Yasmin din ce take biyawa Hidaya duk wani abu da za’a nema a makaranta. Kuma Yasmin da Iyayenta suna yiwa Hidaya manyan kyautuka na kudi da kayan masarufin da har suke samun rufin asiri ita da mahaifanta.
Yasmin ce ta koyawa Hidaya mota har ya zama a lokuta da dama Hidaya ce take jan mota zuwa duk in da zasu.

****
Duk yanda yaso ya 6oye damuwar shi a gaban Likitan ya kasa samun nasarar haka, abinda ya qara fadada damuwarshi shine yanda yayi ta kiran wayar Yasmin har sau biyar "Is Swich Off!" Kamar yanda Computer take fada mishi.

Likitan ya sake kallonshi yace,
"Inspector lafiya kuwa?”
Cikin mamaki yake masa wannan tambayar ganin daga amsa waya matashin dan sandan ya shiga damuwa.

Dan Murmushin yake yayi yace,
“Ba matsala Dr. ci gaba da bayaninka. Ina saurarenka”
Ya fada cikin qarfin hali bayan ya yi kakarin fadada fuskarsa da murmushi.

“Wadannan sune takardun duk wani bincike da muka gudanar a kan gawar yarinyar.”
Ya fada bayan ya miqa masa fararen takardun hannayenshi, ya zazzaga File din sai ga wata sarqa irin wadda gayu suke sakawa a wuya ta fado.
“Wannan kuma a hannun gawar muka samu ta damqeshi kam a hannunta na dama, da qyar muka samu nasarar bude hannun muka cire shi, amma kuma bana tunanin sarqar zai taimaka maka gurin gano wadanda suka aikata laifin”
Likitan ya fadi haka bayan ya miqa masa sarqar hannunshi da file din da takardun da suke ciki.

Sama sama Abdul ya kalli sarqar sannan ya hada komai ya maida cikin file din kamar yanda likitan ya dauko da farko. Gaba daya hankalinsa yana kan Aysha don haka yayi gaggawar sallamar likitan tare da yi masa godiya a kan lokacin da ya bashi. Shima likitan godiya yayi ma Abdul gami da yi masa fatan samun nasara a kan abinda yasa gaba, sannan ya yi alqawarin baiwa Abdul din hadin kai a duk lokacin da ya neme shi.

Qarfe biyu saura kwata agogon motar tashi ya nuna, hakan shiya bashi tabbacin awa hudu da minti arba’in da biyar kenan da fitowarsa daga gida. sallama suka yi da Sajent Nalado, bayan ya ba Sajent din kudi masu yawa a kan yaje ya wanko masa hotunan nan, ya ci abinci ya koma Office ya jira dawowarsa.
Chapter 9 · 0% Book details