← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dayan hannunta Abdul ya kamo da hannunshi mai lafiya ya ce, “Zan iya cike miki gurbin komai da kowa da kika rasa a rayuwarki Aysha, ke dai kawai ki bani dama ko sau daya ne.”
Ta ce, “Anya ba dadin baki kake mini ba?”

“Gaskiya da gaskiya ke tsakaninmu Aysha.”
“Zan baka dama. amma sai lokacin daka cikamin alqawarin nemo wadanda suka hallaka Sadiya, kuma ka miqa su hannun hukuma aka yanke musu hukuncin daya dace dasu. Duk ranar da hakan ta kasance zan miqa maka ragamar rayuwata.”

"Ni kuma na yi alqawarin tabbatar da hakan da izinin Allah Aysha.” Sai a wannan lokacin ta lura da yanda jikinta ya dan baci da jinin hannun Abdul, hannun ta dago zuwa bakinta da tofa masa duk addu’ar da tazo bakinta.
Saida ta gama tace
“Sannu Abdul, insha Allah yanzu jinin zai tsaya”
Tsakiyar lumsassun idanunta yake kallo cike da matsanancin so da qauna…
“Wash Allah na…” ya fada bayan ya runtse ido ya bata fuska.
Tun daga tsakiyar kanta har qafafunta take jin wani abu yana mata yawo a jiki. Kwantar da idanunta qasa qasa ta sake yi ta qara matsawa har gwiwoyinsu suna gogar juna,
“Wayyo sorry Abdul… akwai zafi koh?”
Fuskarshi a kwabe kamar karamin yaro yace
“Akwai zafi sosai Aysha, ji nake kamar hannun zai cire”
Ya fada muryarsa qasa qasa kamar zayyi kuka. A hankali ta ci gaba da hura yatsar tana rarrashinshi cikin tausayi, sannu kuwa ta furta masa har batasan iyakarshi ba.

A haka suka fado cikin falon ba tare da sunyi sallama ba, sallallami kawai suka hada baki suna jerawa ganin irin zaman da su Abdul din suka yi shi da Aysha, ganinsu baisa ta saki hannunshi mai ciwon ba shima bayyi yunqurin qwace hannun ba.
“Sannu da zuwa Baffa.”
Abdul ya fada muryarsa can qasa qasa, idanunsa kadai zaka kalla kasan yana cikin wani irin yanayi mai faduwa a baki.
Cikin mamaki Baffa ya ce,
“Me zan gani haka Abdul Ahad? Ashe duk maganganun da Yasmin ta sanar damu gaskiya ne sai ma abinda bata fada ba?”
Ya fada cikin masifa yana zare idanu kamar zai kaiwa Abdul duka.
Mommy kam tana tsaye a inda take ta kasa tankawa sai tafa hannaye take cikin mamaki.
Baffa ya kara da cewa
"Duk ilimin addinin da kake dashi ya zama na banza kenan Abdul? A kan wannan karuwar har ka iya dukan matar da mahaifanka suka zabar maka?”

Abdul dai bai ce komai ba illa kallon hannayen Aysha da suke riqe da hannunshi mai ciwo yake hi.

“Ke sakar masa hannu ki hado duk kayanki ki kama gabanki tun kafin na ci mutuncinki, karuwar banza karuwar wofi, kinyi asara wallahi, da quruciyarki kin lalata rayuwarki a banza”

Sai a wannan lokacin ya dago kai ya ce,
"Baffa duk zagin da zaka yi ya tsaya a kaina karka taba Aysha, don ba ita ta doki Yasmin ba ni ne.”

Baki da hanci bude da mamaki yake kallonsa
“Ni kake fadawa haka Abdul? Ashe ban isa na yi hukunci a kan al’amarinka ba?”

“Sanin ka isa dani yasa nace ka tsaya a kaina domin ni ne naka”

“Ke tashi ki fice daga gidan nan tun kafin nasa a fitar dake"
A wannan lokacin Baffan Abdul ya fara kai Aysha bango don haka ta kalleshi kai tsaye ta ce,
“Babu inda zanje tunda ba zamanka nake yi ba.”

“Kinsan da wanda kike magana kuwa? Idan ke ‘yar bariki ce zan nuna miki ke ‘yar koyo ce, wallahi zan lakada miki duka idan kika nemi yiwa Mijina rashin kunya.”
Mommy ke wannan furucin bayan ta cire gyalenta.

“Ashe dai a barikin ma ke uwata ce, don haka kai tsoho ka fara maganin ta gidanka kafin ka yi maganin ta waje"
Aysha ta fadi haka tana watsa wa Baffa da Mummy harara.

“Baffa wannan wane irin rashin adalci ne? a matsayina na Yaya kuma wanda zai auri Yasmin ai ina da ikon da zaku tambayeni gaskiyar abinda ya faru. haka kawai daga yarinya ta fada muku qarya da gaskiya kunhau kun zauna kuna neman ku ciwa wadda bataji ba bata gani ba mutunchi.”
Ya fadi yana maida numfarfashin dake nuna ranshi yakai qololuwa gurin 6aci.

“Kana jin irin muggan maganganun da take fada mana amma zaka rufemu da fada kamar wasu ‘ya’yanka?”
Mummy ta fada tana matso qwallah daga idanunta.

“To wa yaja Mummy? Duk wanda bai ji kunyar hawa jaki ba ai jaki bazai ji kunyar yadashi ba.”

"Ba laifinka ba ne Abdul Ahad, laifin Ardo ne d yake daure maka gindi kana aikata abinda kaga dama, don haka duk iskancin da kakeyi zan sanar dashi, idan yaso shi sai ya dauki matakin daya dace tunda mu bamu isa ba. ke kuma ( ya fada yana nuna Aysha da dan yatsa manuniya alamun jan kunne da kashaidi) zaki san ni kika fadawa maganar banza, zan nuna miki iyalina sunfi qarfin a wulaqantasu, duk abinda ya sameki kar ki zargi kowa ki zargi kanki.”
Baffa yana gama fadin haka ya ja hannun Mummy suka fice daga falon.

“Ina matuqar jin tsoro Aysha” Abdul ya fadi yana kallon Aysha idanunsa na nuna raunin zuciya da tsoro qarara. Baysn fitarsu Baffa.
“Tsoron me Abdul?”
Aysha ta tambayeshi bayan ta maida hankalinta gaba daya a kanshi.

“Baffana mutum ne mai matuqar son iyalinshi, ba kaina nake tsoro ba ke nake jin tsoron kada su cutar mini dake idan babu ni a kusa. kinga yanayin aikina ba na zama bane, ba ko wane lokaci bane zan kasance tare dake.”
“Kar ka damu kanka Abdul. ni kam banajin tsoron komai, bai isa yasa a cutar dani ba sai abinda Allah ya qaddara zai faru dani, na shiga hadarin da yafi wannan kuma na tsallake da taimakon Ubangiji.

Yace
"Dukda haka ina jin tsoro Aysha, dole in nemi duniyar da zan 6oye ki, duniyar da babu wanda ya isa ya 6ata miki rai, duniyar da ako wane lokaci zaki kasance cikin farin ciki da annashuwa.”
Kallonshi tayi tace,
“To sai ka barni na koma cikin ‘yan uwana, don a can din ko wane lokaci ina cikin fara’a da walwala.”

“Ki daina wannan maganar Aysha, gurin Ardo zan kaiki. a can ne in da babu wanda yai bata miki rai…”
“Ina kenan? Wanene Ardo?”
Aysha ta katse shi da wannan tambayar tun kafin ya aje numfashin maganarshi.
“Can garin mu Yola, Ardo shi ne kakana mahaifin mahaifina. Kuma mahaifin Yasmin.”
"Bazai taba yuwuwa ba Abdul, taya za’a yi kace na bika cikin danginka bayan tun a yanzu na lura basa sona, bazan taba barin garina da ‘yan uwana in yi wata tafiyar da bansan iyakarta ba, haka kawai? Ni dai gaskiya ka qyaleni, ka fice kawai daga cikin rayuwata ko ma samu salama gaba dayanmu.”
Bai sake tanka mata ba illah ficewa da ya yi daga cikin falon, cikin motarshi yaje ya dauko wayarshi da tun bayan dawowarshi lokacin su Aysha suna tsaka da rikici ita dasu Yasmin ya barta a motar. Bai bi ta kan 45 miscalls din da ya gani a fuskar wayar ba ya lalubo lambar Ardo ya danna kira. lokacin qarfe takwas da rabi na dare. Miqewa Aysha ta yi tana hararar Abdul din ta nufi cikin daki. yasa hannunshi ya janyota ya zaunar da ita a gefenshi. A speaker ya danna wayar yanda Aysha zata iya jin duk abinda ake fada daga can dayan bangaren. taji tattausar murya mai cike da kamala da dattijantaka ta watso sallama, Abdul ya ce,
“Barka da dare Ardo!"
bayan ya amsa sallamar cikin tsantsar ladabi da kwantar da kai.
“Barka dai Modibbo, ina fatan dai lafiya?”
“Akwai matsala babba Ardo.” Abdul ya fada muryarshi da tsananin damuwa.

“Muryarka ta tabbatar da akwai matsala, me yake faruwa da har ya dimauta Modibbo?”
Cikin nutsuwa Abdul ya gama korawa tsohon bayanin duk abinda ya faru tun daga zuwan su Yasmin da zuwan mahaifanta gidan da shawarar da ya yanke na mai da Aysha can garinsu ita kuma taqi amincewa.
Ajiyar zuciya mai nauyi Ardo ya sauke kafin yace
“Ina ita Aishatu?"
“Gata nan tana jinka Ardo.” Abdul ya matso da wayar saitin bakin Aysha tana jin duk abinda Ardon yake cewa,
"Assalamu Alaiki Aisha.”
Ardo ya furta da muryarshi mai cike da kwarjini. ita kanta Aysha jikinta rawa yake gurin amsar sallamar tsohon, a kwai wata baiwa da Ubangiji yayi wa Ardo, wanda duk taurin zuciyar mutum dole ya shiga nutsuwarshi idan ya saurari maganar Ardo.
Hakan ce ta kasan ce ga Aysha.
“Aysha kiyi haquri da Modibbo, yana tsananin sonki shi yasa yake neman duk hanyar da zaibi ya tserar dake daga masu nufin cutar dake, ki bashi dama gobe ya kawo ki Yola, mu masu tsayuwa ne a kan al’amarinki bamu da nufin cutar dake, ki amince da duk buqatar da Modibbi zai zo miki da ita matuqar bai sa6ama addini ba, don Allah..”
Gaba daya tsohon ya gama kashe mata jiki, sam ba zata iya musa masa umarni mai hade da roqon alfarmar da ya yi mata ba. duk da Aysha bata ta6a haduwa dashi ba, bata san lokacin da bakinta ya yi saurin fadin
“Shikenan! zan biyo shi mu taho zuwa nan din, in Allah ya yarda"
Chapter 12 · 0% Book details