← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyada kai alamar ya fahimta, ya kara mata da cewa
“To wannan karuwar da kike gani aurenta zanyi, kuma nafi sonta dake fitsararriya mara tarbiya, idan kuma kin cika ‘yar iska ki qara tanka mini idan ban farfasa miki jiki ba.”
Ya fadi hakan bayan ya zare belt din wandonsa, sanin da ta yi tsab zai aikata abinda ya fada yasa ta dauki gyalenta da jakarta ta nufi qofa, Hidaya kuwa dama tunda taga shigowarshi ta sa6e ba tare da kowa ya lura da fitarta ba sai Aysha.
“Zaka gani wallahi, wanda ya daure maka gindi shi zan samu inyi masa bayanin duk iskancin da kake yi.”
Da gudu Abdul ya bita tuni ta fice daga falon a guje, Hidaya tana ganin fitowarta da gudu ta rufa mata baya, ko motarta bata dauka ba sai me keke Napep suka dauka ya kaisu har gidan su Yasmin.

Yana zaune a kan kushin yana sauke numfashi cikin tsananin fushi da qunar zuciya, baqaqen maganganun dasu Yasmin suka ringa jifan Aysha dashi musamman kalmar nan ta (Karuwa) yaqi 6acewa daga zuciyarsa, saboda tsabagen kunya ya kasa had'a idanu da ita, ita kuma ko ajikinta wai an yakushi kakkaura. tunawar da ta yi ko sallar azahar bata yi ba gashi har la’asar ta kawo jiki yasa ta miqe da sauri ta nufi cikin Bed room din da take kwana. Tana bada baya ya bita da kallo yana tunanin ko jakar kayanta zata dauko ta ce dashi lallai ya maida ita inda ya dauko ta, dan haka tagumi ya yi yana tunanin kalmomin da zai rarrasheta dasu, ganin ta dauki tsawon lokaci bata fito ba ya sashi sakin a jiyar zuciya, ya nufi dakinshi ya watsa ruwa sannan yai sallar azahar da la’asar a cikin dakin, don yana tsoron fita zuwa masallaci ita kuma ta fice daga gidan.

Yana zaune a falo ya shirya cikin qana nan kaya sai baza qamshi yake yi, Aysha ta shiga falon da siririyar sallama a bakinta, ta yi matsakaiciyar kwalliya cikin doguwar riga pople da dan siririn mayafi a kanta, ita kanta tasan ta yi kyau don dama ita din mai kyau ce, kallo kawai ya bita dashi a zuciyarshi tasbihi yake ga Ubangiji daya kyautata halittar Aysha.
“Yarinya kamar ita ta halicci kanta. ya Allah ka azurtani da wannan kyakykyawar yarinya a matsayin matar aure (Amin)" ya yi addu’ar da iya le6anshi ta tsaya sannan ya amsa a zuciyarshi.
“Aysha don Allah ki yi haquri da duk maganganun da su Yasmin suka fada miki"
Ya fada bayan ya gama kame-kame ya rasa ta inda zai fara bata haquri.

Dan Murmushi tayi masa tace
“Laaaaa... Babu damuwa fa"
Ta qara maida hankalinta a kan allon T.v

“Kina nufin ranki bai 6aci ba?” ya tambaye ta da mamaki.

“Ko kadan raina bai 6aci ba, ni dariya ma suka bani, abinda na fahimta shine tana sonka sosai, don haka ba laifi idan ta yi kishi kan abinda take so.” Ta amsa masa tana kallonsa ido cikin ido.
“Wannan ai ba kishi bane Aysha, hauka dai ko?”

“Kowace mace da ka gani a duniya a kwai yanayin kishin da Ubangiji ya saka mata a zuciyarta, karka ga laifinta ita nata kalar kishin kenan.”

"Amma na tabbatar ke ba za ki yi irin haka ba"
Ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa.

“Me yasa kake tunanin ba zan iya haka ba?”

“Saboda kina da sanyin hali…”
Ya amsa cikin salon jan tsawon hirar tasu.
Dariya tayi kawai, can kuma tace
“Zan yi abinda ya fi haka idan ni ce, shi yasa bazan ta6a yin soyayya ba a rayuwata"

Dariya yayi yace,
“Ki dai yi tunani Aysha, amma daf kike da fadawa a soyayyata, kin ga daga lokacin sai in ga salon kishin naki.”

Shiru tayi bata tanka masa ba, a maimakon zaman qudan da suke yi ma sai ta qara maganar T.V don ta gaji da hirar, Abdul ya katse shirun da cewa
“Me za ki ci? Don na lura yanzu ki ka tashi sai kuma ki ka tarar da rikicin su Yasmin.”

“Ba na jin yunwa fa, na riga na sha Lipton tun kafin dawowarka”

“Lipton ai ba abinci ba ne, ko na dafa miki Indomie da qwai?”

Batasan lokacin da murmushi ya qwace a fuskarta ba, tana kallonshi ta ce
“Namiji da girkin abinci?”

“Eh mana! kuma ko qwararriyar mace babu abina zata gwada mini a fagen iya girki da kwarewa”
Ya amsa kai tsaye da zallar gaskiyarsa.

"Ya yi kyau hakan, kaga matarka ta huta da shiga kicin”
Sai da ya yi dariya sosai sannan ya ce, “Ke kenan Aysha? Don babu yarinyar da zan aura na yi mata girki sai ke matar so a gurin Abdul Ahad"

“Lallai kana jin dadin zolaya ta, bayan kuma ni ban saba wasa da yara maza ba”

Dariya Abdul ya qyalqyale da ita jin abinda Aysha ta ce, sai dai yayi dariya mai isarshi sannan ya ya kalleta ya ce,
“Aysha don Allah shekarunki nawa?”

“Kai nifa ba yarinya ba ce, shekaruna goma sha bakwai da kwanaki.”
Ta amsa masa tambayar tasa cikin salon son girma da kwarzanta kai.

“Lallai kin wuce a kiraki yarinya, amma kuma shafal kike baki da nauyi, ki dage da cin abinci mai yawa don shekarunki su tabbata a kanki.”
Murmushi tayi, sai kuma tace
“So kake na zama qatuwa har na ringa kasa tashi?"

"Idan muka yi aure ni ba sai na ringa daukarki ba?”

“Wa zaka aura? Da alamu kana mantawa Aysha ce a gabanka ba Yasmin ba.”
Ta amsa Fuskarta a had'e, don sam bata son yana maganar zai aureta.

“Ina sane da Aysha nake magana, Aysha dai ita zan aura in Allah ya yarda"

“Yunwa nake ji ka dafa mini Indomie, amma banda qwai. Zanji idan ba cika baki kake yi ba"

Dariya ya sake yi,
“To bani minti goma, yanzu zaki ci girki mai dad'i irin wanda baki ta6a ci ba.”

“Jagwalgwalo kenan, don shine abinda ban ta6a ci ba.”

“Wani irin jagwalgwalo kuma? Girki mai rai da lafiya zaki ci, jirani ina zuwa”
Yana gama fadin haka ya fada cikin kichin da sauri.

Minti goma sha biyar ya fito da flet a hannunshi an rufa daya a kan daya, a kan dining ya ajiye sannan ya koma kiching din ya fito da Juice da Cup ya aje a kan dining.
“Komai ya kammala Ranki ya dad'e, Bisimillah!” ya fad'a yana tsaye a kusa da Aysha, ba ta ce da shi komai ba ta nufi dining din, da sauri yaja mata kujera ta zauna a kai, dan qauri qauri ne ya daki hancinta a maimakon qamshin girkin Indomie, haka kawai ta ji batason gwasale qoqarinshi don haka ta yi Bismillah tare da kai cokalin data dibi Indomie bakina, runtse ido ta yi ta tauna da qyar ta hadiye, da sauri ta tsiyayi ruwa a kofi ta kwankwada sannan ta qara yunqurin qara ko loma biyu zuwa uku ne, ganin da tayi yana zaune a kan dining din shi bai zubo Indomie ba yasa ta kalleshi da murmushi a fuskarta ta ce,
“Ina naka abincin? Ko wannan dad'in duk don ni aka yi?"

Murmushi kawai ya yi sannan ya ce, “Ke dai ki cigaba da cin abin cinki, jira nake ki gama ki bani making xin da ya dace dani.”
Aysha ta ce “Menene wannan a gaban rigarka nake gani?”
Aysha ta tambayeshi tana qara kallon gefen rigarshi da idanu, da sauri ya sanya hannu ya rufe gurin. Rufewar da yayi yasa ta lura da yatsarsa daya nad'e da plasta amma har a lokacin yana tsatstsafar da jini.
Zaro ido tayi da sauri ta ce,
"Subahanallah ciwo ka ji Abdul?”
Ta ture kujerar da take zaune ta koma mazaunin kusa dashi, hannunsa ta kamo sai a lokacin Aysha ta lura da rigarshi duk ta baci da jini. A hankali cikin tausayawa ta cire plastar, ganin yankan da yake jikin dan yatsan yasa ta fara hawaye tana fadin
“Na shiga uku ni Aysha, garin yaya hakan ya faru Abdul?”

Dan murmushi yayi ganin yanda ta damu.
“Ki kwantar da hankalinki, kawai gurin yanka albasa ne na yanke dan yatsa ba tare da na sani ba"
“Daman baka iya girkin ba?”
ta tambayeshi har a lokacin hawaye bai bar tsiyaya a idanunta ba.

“Gaskiya ban iya ba, kawai dai ina neman duk hanyar da zanbi na burgeki ne, ni idan kin ganni a kiching ruwan zafi kawai zan dafa"
Kura masa idanu Aysha ta yi tsawon lokaci tana kallonshi, sai a lokacin ta ji wani irin abu mai kama da son Abdul yana tsargawa a cikin zuciyarta .
“Wannan wane irin so kake mini Abdul? Don kana neman hanyar da zaka burgeni sai ka wahalar da kanka? Don Allah ka daina”
Ya kalle ta yace, “Ban ta6a jin ina son wata yarinya a azuciyata tunda Allah ya halicceni sai a kanki Aysha, soyayyarki wata jarabta ce da Ubangiji ya saka mini a rayuwata, ni kaina bansan iyakacin son da nake miki ba, na fara sonki tun a ranar dana fara ganinki a kan babur wayyo kudina ke da ‘yan uwanki, don Allah ki so ni ko da kwatan son da nake miki ne. don Allah ki tausaya mini Aysha, wallahi ina sonki so irin na mutuwa"
A jiyar zuciya mai nauyi Aysha ta aje taci gaba da kallon qwayar idanun Abul, hannunsa mai ciwon yana riqe a hannunta. gaba dayansu sun shiga wani yanayi da ita Aysha baqone a gurinta.
Aysha tace,
"Maza basu da alqawari Abdul, duk wani naqasu da zaka gani daga gareni a dalilin Namiji na sameshi, me zai sa na sake sakankancewa har wani ya sake cutata Abdul?”
Yace,
“Kowa da irin halinsa Aysha, ki bani dama ko kadan ne na gwada miki irin son da nake miki, wallahi bazakiyi dana sanai ba da ikon Allah.”

“Idan na amince maka ya zaka yi da Yasmin? Bayan kuma da kunnena na ji tana fadawa qawarta a Family din ku ba’a auren mata biyu.”

“Qarya take Aysha, inda zaki qara tabbatarwa ba soyayyar qarya nake miki ba a yanzu haka maganarki tana gaban kakana.”

“Zaka iya auran wacce bata da kowa da zata kallah a matsayin Dangi ko dan Uwa?”
Chapter 11 · 0% Book details