Sashe 14
A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ardo ne ya fara magana da cewa,
"Alhamdulillahi rabbil Alamin, dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah S.W.T mai hikimar fitar da matacce daga cikin rayayye, tsira da Aminci su qara tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W da Alayensa da Sahabbansa. Lallai al’amarin yarinyar nan Aysha yana tattare da abubuwa na ban al’ajabi da mamaki game da bil'ada. Amma a gurin Ubangiji wannan ba komai ba ne daga cikin qudura da iradarsa. Yana aikata abinda ya so a lokacin da ya so kuma ga wanda ya so.
A lokacin da Modibbo ya zo min da batu a kan Aysha tare da nuna min hotonta na yi mamaki qwarai, ba don komai ba kuwa sai yadda na ga zallar son Aisha a idanun Modibbo wanda ban ta6a ji ko ganin yana son wata yarinya kamar ta ba. tun a lokacin na fara tunanin akwai wata qulalliyar dangantaka da Ubangiji yake son qullawa a tsakaninmu da wannan yarinya Aisha.
Bayan Modibbo ya kora min duk wani bayani dangane da abinda ya sani na al’ajabi daga rayuwar Aisha, kamar misali yadda ta riqe hannun Yasmin ta karya ta, da yadda ta kwanta haske ya zagaye ta duk jama’a sun kasa isa gare ta, sai ‘yan’uwanta da suke tare da ita. Tun daga lokacin na san akwai wani boyayyen al’amari a tattare da ita. Ko da na yi istihara har na tsawon kwanaki bakwai a kanta babu abinda Ubangiji ya fahimtar da ni sai akwai wani dunqulallen sirri a kan Aisha. Kuma babu wanda ya isa ya samu nasarar cutar da ita sai abinda Allah ya hukunta a kan ta.
A rana ta takwas da yin istihara ta ina zaune a nan falon sai Allah cikin ikonsa ya sa su Hassana suka ziyarce ni. Su suka sanar da ni akwai abinda zai shiga tsakanin Modibbo da Aisha, amma in yi haquri da duk abinda zan ji daga Modibbo, kuma shi ma in kwantar masa da hankali. Idan lokaci ya yi za su zo da mahaifisu don warware mana wace ce Aisha da duk wani 6oyayyen sirri da yake tattare da ita.
Tabbas kun cika alqawari, domin a yanzu babu wani abu da ba mu fahimta ba a dangane da rayuwar Aisha. Kuma in Allah ya yarda ba za mu ta6a ba ku kunya a kan amanar Aisha da kuka danqa a hannunmu ba. za ta zamo jika a gare ni. kuma sirika ga iyayen wannan zuri'a. idan Allah yasa ta amince zan hada aurenta da Modibbo, domin yana mata so irin wanda ban taba ganin wani namiji yana yi wa mace irinsa ba. A game da ‘yan’uwanta kuma da suke zaune gida daya a can Kaduna! Na dauki alqawarin insha Allahu matuqar ina raye zuwa sati mai zuwa za mu tafi gidan tare da Aisha. Zan yi musu nasiha mai ratsa zuciya don warware qullin tsanar DA NAMIJI da yake zuciyar kowaccensu. Sannan zan danqa kowace yarinya a hannun iyayenta da danginta.
Ku kuma Allah ya saka muku da alkhairi, Ubaniji Allah ya jiqan mariqiyar Aisha Zahra’u. allah ya saka mata da alkhairi a kan rainon Aisha da ta yi.”
“Amin summa amin.”
Suka amsa gaba daya.
“Abdul’Ahad ina fata yanzu kanka ya daina shirin bugawa dangane da al’amarin Aisha?”
Aunty Hassana ta tambaye shi tana murmushi.
Sosa qeya yayi cikin matuqar kunya, ya sunkuyar da kanshi yana satar kallon fuskar Aisha tana sharar barci.
“Yanzu na fahimci komai, kuma in Allah ya yarda zan riqe Aisha da amana muddin raina, ba zata ta6a yin kukan maraici ba insha Allahu.”
“Allah ya sa haka Abdul, Ubangiji Allah ya taya ku riqo”
Aunty Hussaina ce ta fadi hakan da murmushi a fuskarta.
“Amin summa amin.”
Aka amsa gaba daya.
“Akwai dukiya mai dan dama da Aisha ta gada daga gurin mahaifinta, su Hassana za su tattara duk dukiyar su tura a cikin asusun ajiyar ka Abdul, idan an maida kowace yarinya gurin danginta za su tattara duk dukiyar da yake gidan da su Aisha suka yi rayuwa ita da ‘yan’uwanta wanda Alhaji Buba ya tara ba ta hanyar halali ba, su raba a gidajen marayu. Sannan za mu sanya hadimamnu su shafe gidan daga doron qasa. Domin irin wadannan gidajen hadari ne ga rayuwar al’umma.”
Karin bayani kenan daga bakin Abdul Yassar, mahaifi ga su Hassana.
“Qwarai kuwa, hakan ya yi daidai.”
Inji Ardo ya amsa cikin gamsuwa da bayanan Abdulyassar.
"Ni ma akwai wasu kudade masu yawa da na gani a cikin motar Aisha a daren da Allah ya qaddara haduwarmu a gidan abinci. sannan akwai wayoyinta da tun ranar da ta koma gidan ban qara bi ta kansu ba, kuma ban bata wayoyin ba.”
In ji Abdul, bayan ya fahimci za a hada lissafin dukiyarta guri daya.
“Ai tun a daren jiya na sanya an dauko min kudaden da wayoyin nata. Idan mun turo da dukiyar gadonta cikin asusunka sai ka siya mata wata wayar, da sabon layin waya”
In ji Aunty Hassana. Miqa Aisha ta fara yi cikin nutsuwa, sannan salati ya biyo baya. Cikin sanyin murya irin ta wanda ya dauki tsawon lokaci yana barci.
Daya bayan daya take kallon su bayan idanunta sun gama wartsakewa. Tashi ta yi daga kwanciyar da ta yi sannan ta sanya hijabinta tana kallon su Aunty HAssana da idanun neman qarin bayani.
“Sannu Aysha, ya kike jin jikinki a yanzu?” Aunty Hussaina ce ta jefa mata wannan tambayar.
Sai da ta nutsu ta qara fahimtar sauyin da ta samu a jikinta, sannan ta amsa mata murya a sanyaye.
“Ina jin jikina kamar ba nawa ba. kamar an sauke min wani nannauyan dutse a jikina"
“Kar ki damu, da sannu za ki wartsake ki koma kamar da.”
Ta fada mata cikin salon rarrashi.
“Aisha daga yau kin dawo cikin familynsu Abdul da zama, idan Allah ya kai mu zuwa sati mai zuwa za ku tafi Kaduna da Ardo don a maida su Nafisa gaban iyayensu, gidan nan kuma da kuke ciki za mu kulle shi. Daga yau idan muna buqatar ganin ki nan za mu zo kai tsaye.” Aunty Hassana ce ta fadi haka tana kallon Aisha don ganin yanajin fuskarta.
Sam bata ji wata damuwa ba a ranta, don haka ta amsa mata kai tsaye ba tare da musu ko jayayya ba.
"Kanwata mun yi miki miji fa…”
Kunya matsananciya ta rufe Aisha jin abinda Aunty Hussaina ta fada mata a kunnenta, da saurinta ta boye fuska a jikin Aunty Hassana tana dan murmushin jin kunya ganin duk su Ardo sun zubo mata idanu suna dariya.
“Qwarai haka ne Aisha, tabbas mun zava miki Abdul’Ahad a matsayin mijin da za ki aura, amma Ardo ba zai aurar da ke gare shi ba har sai ya cika alqawarin da ya yi miki na nemo wadanda suka kashe Sadiya, ya miqa su gaban hukuma an yi musu hukunci daidai da abinda suka aikata.”
Aunty Hassana ta fadi haka da alamun babu wasa a maganarta.
Qasa-qasa Aisha ta saci kallon fuskar Abdul, caraf suka hada idanu. Ashe tuni ita yake kallo. Da sauri ta sadda kai qasa tana jin wani tsantsar so da qaunar Abdul yana kwarara a cikin zuciyarta.
***
Yana kwance a kan gadon da take kwana a lokacin zamanta a gidanshi, zuciyarshi cike da kewa da shauqin son Aisha, tun bayan dawowarshi daga Yola dazu da yamma. Wayarshi ya janyo ya danna kiran lambar sabuwar wayar da layin da ya sai wa Aishan, kafin ya baro ta a can.
Tana falo tana hira da Aunty Aisha auta daga cikin ‘ya’yan Arxo, shekarunta arba’in cif duniya, shekarunta ashirin da biyu da aure, amma har lokacin Allah bai ba ta haihuwa ba. mijinta yana tsananin son ta kuma dan uwa ne a gare ta don haka suka dangana suka bar wa Allah komai, sai addu’a da suke yi ba dare ba rana. Idan ka kalle ta ba za ka yi tsammanin ta wuce shekaru talatin a duniya ba. wayayyiya sosai, kuma mace ce mai tsananin son gaskiya da tsayuwa a kan gaskiyar. Shi ya sa Arzo yake bala’in son ta a duk cikin ‘ya’yanshi. Suna matuqar shiri da Abdul, domin shakaru bakwai ta ba shi. Aunty yake ce mata sabanin sauran qannen mahaifinshi mata da yake kiransu da Yakumbo. Ita aka yanke shawarar danqa amanar Aisha a hannunta.
Ta yi murna sosai lokacin da Ardo ya danqa musu ita da mijinta. Ta iya zama da jama’a shi ya sa a cikin awowin da ba su wuce uku ba suka shaqu sosai da Aisha. Mummy take kiranta da shi kai tsaye, don sunan mahaifiyarta gare ta, yayin da ta fara kiran mijinta da Daddy.
Ringin din wayarta shi ya katse mata labarin rayuwarta da take ba ta, sai da ta yi murmushi sannan ta nuno mata fuskar wayar saitin fuskarta don ganin mai kiran nata. Abdul’Ahad ne
“Anya kuwa Abdul yau za ka bar diya ta ta samu barci?” Abinda ta fara fadi kenan bayan ya amsa sallamar da ta yi masa. Sai da ya yi dariya daga can bangaren sannan ya sake rungume filon da take kwanciya akai ya lumshe ido yace
“Aunty ba laifina ba ne, laifin diyarki ne. Tana gani ina ta kiran wayarta fiye da sau dari amma ta qi dauka, ni kuma idan ba muryarta na ji ba sam ba zan iya barci ba”
Dariya ta qyalqyale da shi, ta ce
“Abdul ni fa yanzu na zama surukarka, don haka dole girma da kunya ya ringa shiga tsakaninmu.”
“Haka ne kuma fa Aunty, to dan taimaka ki ba ni diyarki a waya in yi mata sai da safe.”
Murmushi ta yi daga bisani kuma ta katse wayar tana shafa gashin kan Aisha da ke kwance a jikinta.
"Babyna Abdul yana tsananin son ki sosai, a yadda na tausaya miki a tarihinki da kika ba ni kin ga yanzu A DALILIN DA NAMIJIN kin samu waraka daga duk wani qunci da DA NAMIJI ya dasa miki a zuciya. Ina tabbatar miki Abdul sai ya zame miki bawa a kan soyayyarki. Kin ga NAMIJI ya yi miki rauni, sannan Da NAMIJI ya warkar da ke. Don ba duka suka taru suka zama daya ba.”
“Haka ne kam Mummyna. Ni ma a yanzu na yarda da batunki. Tabbas a maza akwai gurbatattu kuma akwai na kirki. A DALILIN DA NAMIJI na ga duhu da haske a cikin rayuwata…
QARSHEN KASHI NA BIYU