Sashe 10
A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gudu yake da motar kamar zai tashi sama, burinshi da addu’arshi ya isa gida kafin su Yasmin su isa duk da yasan hakan ba abune mai yuwuwa ba, tun dazu Yasmin ta ba shi tabbacin suna hanyar gidan nashi, kuma daga lokacin zuwa yanzu an samu tsawon minti arba’in da biyar.
Suna shiga gidan suka watsar da jakunkuna da mayafansu a falo, kichin Yasmin ta nufa tadauko musu kofuna ta dawo sannan ta bude frij din falon ta dau lemo, suka dararrashe suna sha suna hira, babu wata alama da suka gani a falon wanda zai tabbatar musu da wata halitta a gidan, hankali kwance suke hirar son da Yasmin take yiwa Abdul, labari take bawa Hidaya a kan irin salon soyayyar da zata gwadawa Yaya Abdul dinta idan aka daura musu aure
“Kuma kinsan abin da ke qara kwantar mini da hankali?"
Ta tambayata fuskarta dauke da fara’a
Girgiza kai hidaya tayi alamar A'a, ta kara da cewa
"Sai kin fada farin watan Abdul Ahad"
Fati tayi da Idanunta ta cigaba da cewa
“Mu a familynmu sam ba a auran mata biyu, duk iyayenmu Maza matansu dai dai ne, kuma duk ‘yan uwan juna, kakanmu ne kawai mai mata hudu. kuma tun daga kanshi ya haramtawa ko wane da Namiji da yake zuri’armu auren mata biyu. Kinga aurena da Yaya Abdul mutu ka raba, bani babu fargabar zaiyi mini kishiya balle har hawan jini ya kamani”
Da matuqar mamaki Hidaya take taya qawarta ta murnar ita da Abdul mutu ka raba, amma a zuciyarta dariyar wauta da wawancin qawarta takeyi, domin a zuciyarta take jin Abdul bazai ta6a zama da Yasmin a matsayin mata ita kadai ba, domin babu wani alamun mugun son Yasmin a tattare dashi.
Agogon Bed room yana buga qarfe biyu dai dai Aysha ta bude qwayar idanunta daga barcin da ta dauki awanni biyar tana yi, bala’in yunwa take ji don haka ta fada bandaki da sauri ta yi brush, tana sanye da best fara kar da gajeren wando Three quater baqi, tunanin da tayi a kan sai yamma Abdul zai dawo don haka ta saki jiki ta yi shigar da take so sannan tasha magani ta kwanta, dukda taga lokacin sallah yayi amma tayi niyyar shan ruwan lipton sannan ta dawo daki don sauke farali.
Hayaniya da dariyar da Aysha take jiyowa a falo baisa ta fasa nufar falon ko kuma ta koma daki ta canza kayan jikinta ba, ita sam ta ma manta da wane irin kaya take sanye dashi, gashin kanta ya sauka har qasan kafad'unta yana kwance luf luf gwanin ban sha'awa, siririyar sallama tayi sannan ta sanya kanta cikin falon.
Dif suka dauke wuta, suka k'ame k'am tamkar masu shirin daukar hoto, kallo daya Aysha ta yi musu ta kauda kanta ta nufi kan dining table donjin da ta yi ko sallamarta basu samu sararin amsawa ba.
Ta hada lipton ta sanya qaramin cokali a ciki ta koma kan kujerun falon ta zauna a daya daga ciki bayan ta kunna T.V da rimot din da ta dauka a kan hannun kujerar da take zaune.
Hankalinta kwance tamkar bata san da wasu halittu a falon ba, bata sansu ba, kuma mai gidan wato Abdul bai fada mata zai yi baqi ba don haka bata yi shirin tarbarsu ba, a zuciyarta take rayawa tunda ta gansu a gidan a falo tabbas mai gidan yasan da zuwansu, zata iya yuwuwa ma shi ya kawo su lokacin da take barci, don haka kowa tasa ta fissheshi.
Ta fada a zuciyarta gami da ta6e baki ta ci gaba da shan lipton din tana kallon T.V.
Hidaya ce ta fara farfadowa daga suman ido biyun da tayi, sannan ta sanya hannu ta jijjiga Yasmin don dawo da ita cikin hayyacinta.
“Wannan balarabiyar fa Yasmin? Ko qanwar Abdul ce don naga Familyn ku irin kyau ne”
Kallo daya Yasmin tayi mata ta gane ita ce yarinyar da kamanninta suka qi 6acewa daga ma'adanar hotunan zuciyarta.
Ita ce yarinyar da Abdul ya fara kalla da idanun So sa6anin ita da zasu yi aure tana gama makaranta.
Ita ce yarinyar da taja mata zama a gida har na tsawon sati uku ba tareda ta leqa koda qofar gida ba.
Ita ce yarinyar da ako wane lokaci ta samu dama zata iya hallaka har lahira saboda tsananin tsanar da tayi mata.
Amma saboda tsabar wulaqanci Abdul ya rasa karuwar da zai kai har cikin gidanshi kuma kan gadonshi sai wannan mai kyan dan macijin? Yarinyar da kallo daya ta yi mata ta ji ta tsaneta tsana mai tsanani? Ashe saboda wannan karuwar ne dazu Abdul yake ta yi mata kwana kwana don kar taje gidanshi?
“Lallai lokacin daukar fansa ta yazo"
Ta fadi hakan a zuciyarta. Dukda wani sashi na zuciyarta na tunatar da ita karon battarsu da yarinyar a lokacin haduwarsu a plaza.
'Amma ai sarkin yawa ya fi sarkin qarfi.” Wani sashi daga zuciyarta ke qara mata qarfin gwiwa.
Dan haka cike da tsana ta watsawa Aysha wani mugun kallo ta maida hankalinta kan Hidaya ta ce,
“Allah ya kyauta wannan ta kasance daga cikin zuriyarmu. Wannan da kike ganinta ba kowa ba ce face Karuwa!! irin ‘yan iskan qananan karuwan nan da duk inda suka ga kyakykyawan Matashi da kudi sai suyi ta bibiyarshi ko da ta hanyar asiri ne har sai sun cimma biyan buqatarsu a kanshi"
Ta fadi hakan cikin karaji da d'aga murya don Aysha ta ji abinda ta ce.
“Amma dai anyi asarar kyau, irin wannan ai zama ya kamata kiyi a gida duk kwarton daya matsu ai ya san inda zai sameki.”
Hidaya ta watso mata wadannan maganganu don taya qawarta yaqi.
Cikin jin dadi Yasmin ta ce,
"Ya za’a yi ta zauna a gida Hidaya? Tun tana qarama ta saba hulda da ‘yan bariki irinta duk randa bata samu matayi ba kinga dole ta fito ta nema"
“Amma kinyi kuskure qaramar ‘yar iska, wannan karon komarki bata kamo komai ba, kin fad'a inda zaki kwashi kashinki a hannu”
Hidaya ta fadi haka, sannan ta mike ta fara daure gyalenta a k'ugu.
Duk maganganun da suke yiwa Aysha tana jinsu, bata motsa daga inda take zaune ba kamar yanda bata fasa shan lipton dinta ba, sai data gama sannan ta maida hankalinta gaba daya kansu bayan ta dora qafa daya kan daya, murmushi ne a kan fuskarta domin har ga Allah maganganun da suke mata dariya suke bata. Saida ta gama kare musu kallo ta maida hankalinta kan Yasmin tace
“Hajiya in tambayeki mana?"
“Ina jinki qaramar karuwa"
Yasmin ta amsa tana jijjiga jiki tamkar zata rufe Aysha da duka,
"Menene tsakaninki da mai gidan nan? Ta tambayeta ido cikin ido da alamun nuna rashin damuwa da sunan da ta kira ta dashi.
"Kanwarshi, Kuma mai niyyar zama amaryarshi nan da watanni hudu masu zuwa”
Hidaya ta amsa ta cikin gadara da isa irin tasu ta gwanaye a fagen shisshigi.
Sai da Aysha ta watsa mata kallon kashedi sannan ta ce
“Ban kasa dake ba bare har ki tsomamin wawwaran bakinki, ki jira idan Uwardakin naki ta gaza sai ki dora daga inda ta tsaya"
“Ai amsar da ta baki gaskiya ne, ko kina musu ne in qara tabbatar miki da haka ta hanyar lakad'a miki dukan kawo wuqa?” Yasmin ta amsa a fusace sannan ta mike tsaye tana gyara d'amara da gyalenta.
Sai da Aysha tayi dan dariya jin amsar da Yasmin ta bata, da mamakin jin cewar da ta yi zata mata duka Aysha ta kalleta ta ce,
“Kina nufin kina da qarfin iko a kan Abdul kenan?”
“Qwarai da gaske.”
Ta amsa tun kafin Aysha ta qarasa aje numfashin maganarta.
"Da kyau! don Allah idan Abdul ya dawo gidannan ki saka shi ya koreni a gidanshi, idan kikamin haka tabbas zan gane cewar Abdul naki ne ke kadai. Kuma soyayyar shi tafi qarfina”
Ta fadi haka duk da bata jin son Abdul dai dai da qwayar zarra a zuciyarta.
“Lallai kam zan tabbatar miki ina da qarfin iko a kanshi, saboda isa ta ma tun kafin ya dawo gidan zan kora ki inda kika fito, bayan mun miki dukan kawo wuka ni da qawata, yanda ko a hanya kika ga Abdul ba zaki sake marmarin kallonshi ba balle har kice kina sonshi"
“To bisimillah ga fili ga mai doki, kuma inda ba kasa ai nan ake gardamar kokawa”
ta fada bayan ta gyara kwanciyarta a kan kushin din da take zaune.
Jikin T.V Yasmin ta nufa da sauri ta fara qoqarin zaro wayoyin da zasu doki Aysha dashi, tana qoqarin ciro wayoyin tana jifanta da duk wata mummunar kalma da tazo bakinta Hidaya tana tayata.
“Banza wulaqantacciya, karuwa! da idon Allah haka zaki qare abin dakin mazaje kwararo kwararo har daga qarshe ki samu wanda ya fiki gogewa a bariki ya sanya miki cuta mai karya garkuwar jiki ki mutu a wulakance."
Kaf wadannan maganganu a kunnen Abdul daya bude qofar falon ya shigo cikin sauri.
Ranshi a matukar 6ace yake kallonta,
“Yasmin ashe baki da mutunci?” ya fada cikin mamakin maganganun da ya ji suna fita daga bakinta.
Da matukar fushi ta tare shi da cewa, “Akwai babban mara mutunci daya wuce kai Abdul? Idan ka matsu da yawa ai bai kamata ka kawo karuwa irin wannan ba, sai ka je can Yola ka samu Ardo ka yi masa bayanin a matse kake, kaga daga nan sai a sassauto da daurin auren mu zuwa nan da sati daya...”
Da matukar mamaki a fuskarsa yake kallonta, ya ce,
“Haka kika ce ko?”
"Qwarai kuwa.”
Ta amsa tana girgiza kafada cikin tsantsar rashin kunya.