Sashe 7
A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu sha wata wahala ba lokacin da suka isa Ofishin ‘yan sandan, bayan Abdul ya nuna musu I.D Card dinsa cikin qanqanin lokaci suka sada su da Ofishin D.P.O na gurin, sananne ne a gurin Abdul don haka suka gaisa cikin raha da barkwanci.
“Wannan Madam ce Abdul?”
Tambayar da ya yiwa Abdul din kenan bayan ya lura da yanda Abdul din ke damqe da hannunta yana kakkareta.
“Eh ranka ya dade.”
Amsar da ya bashi kenan a gajarce yana kallon qwayar idanun Aysha.
"Da ganin irin wannan kulawar da kake bata ai nasan amarya ce, Allah ya bada zaman lafiya, gaskiya kunyi matuqar dacewa da junanku"
“Amin na gode Sir.”
Abdul ya amsa addu’ar da ya yi masa, bata ce komai ba illah sake daure fuska data yi, har suka gama barkwancinsu bata gaida D.P.O ba sai shine ya ce, “Madam barka dai.”
Ganin yanda Abdul ya tsareta da idanu yasa tace,
“Yauwa”
“Ranka ya dad'e a kan case din yarinyar da aka tsinci gawarta a wani kango yau da asubah mukazo, yarinyar qanwata ce, jiya da daddare mun fita cin abinci da matata da qanwar tawa a can muka nemeta mu rasa, saboda dare yasa bamu bada cigiya ba a gidan Radio muna jiran sai yau da safe, to sai kuma ga wannan mummunan labari da muka samu, shi yasa muka zo nan kai tsaye don samun bayani a kan in da a ka tsinceta da kuma dalilin mutuwarta ta.”
“Oh My God! Sister din ka ce? Allah ya gafarta mata”
D.P.O ya fadi haka cikin jimami.
"Amin summa amin"
Suka amsa gaba dayansu.
“Yanzu dai muna zaman jiran binciken likitoci ne a kan gawar, na ba babban likitan lambar wayata, idan suka gama bincike..."
Ringing din wayar D.P.O shiya katse masa maganar da yake yi.
"Hello Dr."
Abinda ya fara fad'i kenan daga bangarensa, sannan yayi shiru yana saurare daga can 6angaren,
"Ok to! gamu nan zuwa, an samu ‘yan uwan yarinyar"
Nan take gaba daya suka dunguma zuwa asibiti a motan Abdul din.
Suna zaune gaba dayansu a Ofishin likitan suna sauraron sakamakon binciken dalilin mutuwar Sadiya da yake karanto masu daga wata farar takarda da take hannunshi.
“Wadanda suka saceta sun yi qoqarin biyan buqatarsu da ita ne ta qarfi ita kuma ta yi qoqarin qwatar kanta, sunyi artabu sosai hakan yasa sukayi mata munanan raunika a duk wani sashe na jikinta, sannan sukai mata mummunar fyade, duk ciwukan jikinta yafi qazanta a matancinta, har yanzu da babu rai a jikinta matancinta yana fitar da jini, ba mutum daya ko biyu ne suka yi mata fyade ba, zasu kai mutum biyar zuwa bakwai.
Al’amarin ya qazanta sosai gaskiya, domin a binciken da muka yi mun gano tun kafin su gama aikata masha’a da ita rai ya fice da jikinta. Duk in da masu laifin nan suke ya kamata a nemo su donsu fuskanci hukuncin daya dace dasu.
A yanzu mun gama duk abinda ya dace muyi, saura naku na jami’an tsaro"
Ganin gawar Sadiya shine abinda yasa ta jingina jikinta sosai da na Abdul hankalinta a matukar tashe, zuciyarta a bushe take ko digon hawaye ta kasa fitarwa.
Shima qara tallafeta ya yi, domin ya lura da yanda jiri yake diban ta.
Duk sassan jikin Sadiya ciwo ne har da su yakushi bayan yanka da wuqa, basu iya kallon matancinta ba saboda bayanin da likita ya yi musu. Basu jima a asibitin ba Abdul ya yi sallama da D.P.O a kan cewa zai maida Madam gida ya dawo.
A mota babu mai cewa wani qala, idanun Aysha sun bushe qyamas ko a lamar hawaye babu, zuciyarta a dake take.
Aysha a zuciyarta take fadin cewa ya zama dole su dauki fansar mutuwar Sady koda hakan shine abu na qarshe da zata gudanar a rayuwarta.
Suna shiga gidan taja ta tsaya a falon, kallon qwayar idanunta kawai yayi ya san rigima ce fal a cikinta.
Kiran da ya shigo wayarsa ne ya katse mata hanzari, shi kuma Abdul din ya nemi guri ya zauna a nutse, daga yanda yake amsa wayar ne ya bata tabbacin da wani mutum mai muhimmanci yake magana, ganin yanda yake kallonta yana amsawa da
“To ard'o! Eh muna tare da ita tun jiya, a tayamu da addu’a…To…na gode! sai munyi waya.”
Duk da Aysha bata san me ake fada masa daga can 6angaren ba ta san maganarta ake yi, hakan yasa duk taji ta tsargu, ba shiri ta nemi guri ta zauna.
Kallonta yayi, sannan yace,
"Yanzu kin yarda da abinda nake gaya miki ko? Ina bin diddigin al’amuranki tare da sawa ayi miki addu’a tun ranar da na fara haduwa dake, kuma hakan ya samo aSali ne daga irin tsananin son da nake miki.
Kya6e baki kawai tayi, alamun ko a jikinta, kamar bazata amsashi ba sai kuma tace,
“Ina son in koma gida, don in sanar da ‘yan uwana halin da ake ciki, kuma mu yi shawarar ta inda zamu fara bincike domin gano wadanda suka aikata mana wannan zaluncin"
“Ki bar maganar bincike a hannuna, domin da ni yafi dacewa, kuma ‘yar uwata ce kamar yanda na sanarwa D.P.O"
Abdul ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba, saina ya cigaba da danna wayarsa
"To ni dai ina son tafiya gida"
Ta sake fadin haka bayan ta watsa masa wani mugun kallo.
Fuskar Abdul a daure yake kallonta ido cikin ido,
“Ki daina maganar komawarki gida, domin sam bazan bari ki cigaba da aiki irin na jaruman maza ba”
“To saboda me? Wai ma ina ruwanka dani ne da kake neman takurawa rayuwata??”
Aysha ta fada cikin masifa tana riqe da kugu bayan ta miqe tsaye.
“Saboda sam bai dace dake ba"
Abdul ya fada daga inda yake zaune, babu damuwa ko kadan a fuskarsa.
"To ina ruwanka? Ina ruwanka da rayuwata? nifa wallahi ka takura min, ban sanka ba, bansan daga inda ka fito ba, haka kawai ina gudunar da rayuwata zaka zamemin qarfan qafa.
Bayan duk A DALILIN DA NAMIJI muka tsinci kanmu a wannan hali da muke ciki. dole ne in koma cikin ‘yan uwana, domin samun qwarin gwiwar aikatawa wadanda sukai mana wannan zalauncin abinda ya dace da su"
“Kun zama hukuma kenan?”
Abdul ya fada hankalin shi kwance cikin rashin damuwa da duk abinda ta fad'a.
“Hukumar banza, hukumar wofi…ai mu munfi hukuma, domin ba wanda ya isa ya hana mu aikata abinda muka so kuma a lokacin da muka so…”
“To! Ai ban hana ki tafiya ba, ko na daure ki ne?bismilla ga hanya nan.!”
Ya fada yana nuna mata kofar fita, sannan ya maida hankalin shi ga danna remot din TV.
Cikin fushi da karin tsananin bakin ciki ta sake cewa
“Wai ana dole ne a rayuwa? bana sonka, ko soyayya dole ce? Ka bani wayoyi na mana kaga in ban bar maka gidanka ba”
Kallonta ya sake yi sama da kasa, cikin fada shima yace
“Ya zama dole ki zauna da ni, kuma ki so ni, ke karya kike yi ma kice ko kadan bakya so na, ni ba irin namijin da ake k'i bane”
Yaraf ta zauna a kan kushin, rashin abin cewa yasa ta fashe mishi da kuka mai tsananin karfi.
Tashi yayi ya nufi wata hanya a cikin falon da bata san ko ina zata 6ille ba, can sai gashi ya dawo da cofin ruwa a hannun shi ya nufo gurin da take zaune tana kuka, kallonta kawai yayi, da sanyin murya yace
“Yi haquri ki sha ruwan sanyi sai muyi magana ta fahimta”
Da farko Aysha qin amsar ruwan tayi, sai da taga ya nufo bakinta gadan-gadan da kofin ruwan sannan ta kar6a a fusace ta sha, bata a jiye kofin ba saida ta shanye ruwan gaba daya.
A hankali sanyi ke kwarara a cikin zuciyarta da duk sassan jikinta, wata nutsuwa ke kwarara a ruhinta, shiru tayi ta jingina bayanta da jikin kujera gami da lumshe idanun ta.
“Me yasa kake neman zamowa mai qarfi a kaina ne? me yasa kake samun nasarar ta6a jikina bayan babu 'Da namijin daya ta6a samun nasarar haka? Me yasa kake neman canza min aqida ta ne? me yasa kake neman juya min alqibla ta ne? me yasa kake neman….”
Da sauri yace,
"Saurara Aysha ki saurare ni don Allah, duk wadan nan tambayoyi maki amsarsu guda daya ce, saboda soyayyar gaskiya nake yi miki, kuma sam bani da niyyar cutar dake, nine wanda Ubangiji ya turo don kawo qarshen matsalolinki, ki bani dama sau daya kawai Aysha, ki bani damar zamo wa mai share miki hawayenki.
Wallahi bazan ta6a baki kunya ba, zan tsaya a kan al’amarin mutuwar Sadiya kamar yanda zan tsaya a kan mutuwar qanwata, ki bani dama don girman Allah. idan kin amshi roqona daga yau bana buqatar ki sake musanta umarni na, ina sane da al’amarin ‘yan uwanki. Kuma zaki koma garesu amma ba yau ba, kin amince da duk abinda nace?”
Ya karasa da tambayar yana kallon cikin idanunta. Kallon kallo suka rinqa yiwa junansu har na tsawon mintina goma, qoqari take ta gano gaskiyar maganganun da ya yi mata, yayinda shi kuma Abdul din yake qoqarin tabbatar mata da abinda ya fada gaskiya ne har zuciyarsa.
Bata san mai yasa zuciyarta take saurin karaya da amincewa Abdul ba, ada babu wani Namiji daya isa ya nuna mata yatsa ba tare da ta karya ba, amma a kan Abdul-Ahad zuciyarta da gangar jikinta masu rauni ne.
Kai kawai Aysha ta daga wa Abdul din alamun ta yarda da maganganunsa ganin da ta yi har a wannan lokacin jiran amincewarta yake yi.
Murmushi yayi fuskarsa na bayyana tsantsar jin dadi da amincewar da tayi dashi. Yace,
“Me kike son ci don kar in kawo miki abinda zuciyarki bata so?"
Murmushi kawai Aysha ta yi don ta gane yana tsoron ta sake yi masa amai irin na dazu ta ce,
“Duk abinda ka kawo zanci, ba baquwar zafi bace.”