← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan cikan kwanaki uku ya koma gurinshi, zaune a gaban malamin yana saurarar bayanin da yake mishi.
“Dan ka yana cikin wani irin mugun yanayi kamar yadda Allah ya fahimtar dani, haka shi ya tabbatar min da waccan yarinya da kake fadin ita ce silar mutuwar danka sam bata da haqqi a kanshi, kuma shi yaron na ka bai kasance mai aikata ayyukan alkhari ba a duniya, don haka duk inda wannan yarinya ta shiga zaifi kyau ka nemo ta domin roqarma danka yafiya a gareta ko zai samu sassauci a halin da yake ciki, kuma ka ji6anci ba da sadaqa a na roqar mishi yafiya a gurin Ubangiji, kuma ka dage da addu’ar Allah ya yafe mishi da kai da duk wani wanda ya zalunci wannan yarinya"

Da wannan bayanin ya bar gurin Malam jikinshi a sanyaye, bai 6oye wa mahaifiyar Nasir komai ba a kan abinda Malamin ya sanar dashi, kuma baiyi sanya ba gurin aikata shawarar da Malam ya bashi.
A kullum mahaifiyar Nasir ta na dafa abinci mai yawa a kai makarantu na almajirai a na rabawa sadaqa a na addu’ar Allah ya gafartawa Nasir, ya bayyana Fatima.

***
Ya na zaune a tanqameman Office dinshi yana shan A.C masinja yake sanar dashi yana da baquwa, yayi matuqar mamaki jin cewa mace ce baquwar tashi, a saninshi bashi da ajenda da wata mace a ranar yau sai dai da yake shi din mai jama’a ne sai ya kauda mamakin da yake, yayi Umarnin a shigo da ita.

Numfashinsa ne ya kusa dauke wa don ganin kyakykyawar budurwar da ta kasance baquwar tashi.
Ina shiga Office din na maida qofar na rufe tare da sanya key ta ciki na kulle na zare makullin na saka a aljihun wando na.
Da rausaya na karasa kujerar gaban teburinshi na zauna, sannan na dora kafa daya kan daya ina kallon yanda a ka qawata ciki da waje na Ofis din amma da dukiyar haram.
Tunda a ka sanar dashi zuwana yake mamaki, da ganin shigowa ta irin kyan da nake dauke dashi da shigar da nayi na riga da wando sun fitar da ainihin surar jikina duk mamaki suke bashi, ganin na rufe qofar tare da zare dan key din shine abu mafi mamaki a tare da ni.
Ban ce komai ba tsawon minti biyu illah wurga lumsassun idanu na da nake yi daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.
“Yan mata lafiya dai ko?”
Ya katse shirun daya ratsa tsakaninmu don ganin bani da niyyar magana. Tsawon daqiqa talatin ina jan fasali kamar bazan tanka ba, daga bisani na watsa idanuwa na a kanshi tare da fadin.
“Alhaji Musa koh?”
Sai da ya sauke ajiyar zuciya jin tattausar muryata sannan yace,
“Qwarai kuwa ni ne, me yake tafe dake?”
Numfashinshi ne ya tsaya cak na wasu ‘yan daqiqu ganin bakin bindigar da nayi arresting dinshi da ita, nan take ya daga hannuwa sama, duk jikinshi ba inda ba ya kyarma, tsananin tsorata ya hanashi furta komai.

“Ka san me ya kawo ni gurinka a daidai wannan lokacin?”
Na tambaye shi har a wannan lokaci ban janye bindigar daga kanshi ba.

“A’a… Don Allah karki kashe ni, duk abinda ki ke so zan baki.”
Ya fada bakinshi na rawa da alamun miqa wuya.

“Good! gara da kai tunanin zan iya fasa qwaqwalwar ka idan kai qoqarin yi min gardama, na san kana da labarin ‘yan bindiga mata da suka shiga gidan yari suka sace Fatima, kuma nasan kaga yanda muka yi da masu gadin duk da dai bamu kashe ko maigadi daya ba.
Ba wani abu ya kawo ni gurinka ba illah buqatar dukiyar gadon Fatima da yake gurinka, nasan komai a kan dukiyar ta da yake hannun ka wanda dan uwanka ya mutu ya bar mata, ka dad'e kana shanawa da dukiyar da ba taka ba, don haka lokaci yayi da zaka miqa komai ga mamallakinta kaima ka huta.

Sati daya na baka ka gama tattara komai zan dawo in amsa, kuskure daya da za kai shine ka yi qoqarin yi min taurin kai ko kuma ka shigo da hukuma cikin al’amarin, idan kai haka zamu kar6ii dukiyar ta qarfi sannan in huda ko wane sashe na jikinka da alburushi, idan kunne ya ji…”
Ina gama fadin haka na maida bindigar aljihun wando na sannan na bud'e qofar na fice ba tare da na qara kallonshi ba.

Tsawon minti talatin baisan ina kanshi yake ba, har a wannan lokacin hannunshi yana d'age a sama ya kasa saukewa, don gani yake a ko wane lokaci ya sauke zaiji saukar bindiga a qwaqwalwarsa.
“Ranka ya dad'e lafiya kuwa?”
Masinjanshi ya maimaita tambayar a karo na biyu tare da qwanqwasa teburin gaban Alhajin da qarfi, firgigit ya yi tamkar wanda ya tashi daga barci, bai ce da masinjan komai ba ya dauki makullin motarshi da wayarshi ya nufi gida, hularshi ma a nan ya barta saboda tashin hankali.
“To fa! Kome yake damun Oga? Da alamun wannan baquwar ta zo wa da Oga mummunan saqo. Allah ya kyauta….”
Abinda masinjan ya fad'a a zuciyarshi kenan ya janyo qofar ofis din tare da sanya kulle kofar ta waje.

“Ina fatan bai yi yunqurin bada matsala ba?”
Nafisa ta tambayeni lokacin da muke tsakiyar gow slow bayan dawowarmu daga Office din Alhaji Musa kawun Fatima.
“Ba a yanzu ne zan san haka ba sai kwanakin da na bashi sun cika ba tare da ya aiwatar da abinda na umarceshi ba”
Na amsa mata kai tsaye, idanuna yana kan titi.

“Bana tunanin zai bada wata matsala, domin shi kanshi ya san ba dukiyarshi ba ne, kuma idan ya miqa dukiyar ga mai ita ai an sauke mishi nauyi ne.”
Nafisa ta fadi haka tana qoqarin sakawa motar da take gefenmu signal domin ta daga mana qafa mu shiga gabanta.

“A ganin ki kenan ko? Idan ya na tunanin haka meyasa tun da can bai miqa dukiyar ga Fatima ba?”

“Kuma fa hakane.”
Ta fadi haka tana gyada kai cikin gamsuwa.

“Mutane akwai su da son kudi, don haka basu da damu da ko wace hanya zasu bi don samun kudin ba, su dai kawai suyi mugun kudi, a kirasu masu kudi….”
Karaf idanu na a cikin nashi, ashe shine mai motar gefenmu, dauke kai nayi ba tare da na sake kallon inda yake ba, amma a jikina ina jin har a lokacin da ya daga mana qafa muka shiga gabanshi ni yake kallo.
“Dan sandan nan ne.”
Na fada a zuciyata, ina tunanin haduwarmu dashi kwanaki uku da suka wuce a bikin birth day din Hajiya Danasha.
***
Tsananin damuwa da tashin hankalin da yake ciki shiya hana shi ganin rama da bak'in da babban aminin shi Alhaji Muhammd ya yi.
Sama sama suka gaisa ya fara kora masa bayanin yanda sukai da yarinyar da ta ziyarci Office dinshi dazu da rana.
Bai katse shi ba sai da ya lura ya gama fadin abinda ya kawo shi sannan ya saukar da ajiyar zuciya ya fara da cewa.
“Nifa Alhaji banga wani abin tashin hankali a wannan maganar ba, lokaci yayi da ya kamata ka tsakarke dukiyarka, idan har zan ba ka shawara ka ji ya kamata ka tattara duk dukiyar da kasan ta Fatima ce ka damqa mata, sannan ka qara da roqonta gafara.
Ni yanzu da ka ganni na gane kuskure na, a kullum addu’a na ke Allah ya hada ni da Fatima in roqi gafara a gareta, domin Allah ya bayyana min duk wani abu da yake 6oye wanda ban sa ni ba, shi yasa nake bin duk wanda na san na cuta ina mayar masa da haqqinshi tare da roqon gafara….”

Baki bude yake kallon shi tunda ya ji ya fara wadannan maganganun masu kama da soki burutsu.
“Alhaji kasan me ka ke fada kuwa? In ba Fatima dukiyarta fa ya na nufin rasa biyu daga cikin uku na dukiyata.”
“Qwarai nasan da haka, domin miqa mata dukiyar tata shine samun kwanciyar hankali a gareka a nan duniya da ranar gobe qiyama.”

“Gaskiya bazan iya ba, yanda na saba da juya naira bazai yuwu lokaci daya in koma mai rufin asiri ba.”
Ya fada cike da tsananin damuwa yana jujjuya kai.

“To me ka ke tunanin za ka yi? yaran nan tunda suka fasa gidan prison su ka fitar da Fatima ba qaramin shiri suke da shi ba.”

“Duk shirinsu ai hukuma tasha gabansu, don haka zanje in samu hukuma tun kafin kwanakin da suka d'iba min ya cika.”

“Ka manta kashaidin da tayi maka kenan?”
Alhaji Muhammad Abban Nasir ya fada yana mamakin tsaninin san zuciya da taurin kai irin na aminin nashi.

“Sam ban manta ba, amma ba zan iya miqa musu duk dukiyar nan ba, dole in dauki mataki don kare kaina.”

“Wallahi ba zaka ta6a samun nasara ba, tunda ba a kan gaskiya ka ke ba.”
Alhaji Muhammad ya fad'a ranshi a 6ace.

“Fatan da kake min kenan?”
Alhaji Musa ya tambaya yana kallon aminin nashi a fusace.
"Ba mugun fata na ke maka ba, illah gaskiya da nake fada maka kuma wannan shi ne aminci na gaskiya.”

Alhaji Muhammad ya fada cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali.

“Ka riqe gaskiyar ta ka, ina tabbatar maka ni zan yi Nasara a wannan karon battar tamu, kana zaune zaka samu labarin an damqe ‘yan bindigan da suka fasa gidan yarin mata, tare da mai laifin da suka sace”

“Idan kuwa hakan ya faru ni da kaina zan sake shigar da qara in wanke Fatima daga zargin da a ke mata tare da tabbatar wa kotu cewa d'ana ne yai qoqarin keta ma ta haddi ita kuma ta kare kanta”

Tsaki mai qarfi Alh Musa yaja sannan ya mike a fusace ya nufi hanyar ficewa daga falon baqin na Alhaji Muhammad ba tare da ya qara tankawa ba.
“Allah yaba mai gaskiya sa’a”
Kalmar qarshe da Alhaji Muhammad din ya rakashi da ita kenan.!
Chapter 2 · 0% Book details