Sashe 5
A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, me yake shirin faruwa ne?”
Ya fada a fili lokacin da agogon hannunshi ya buga qarfe goma sha biyu na dare a wannan lokacin motocin gurin duk sun gama watsewa, sai ‘yan dai dai ku da ba za’a rasa ba. Motar ta ya koma don ganin ko a wane hali take ciki, tana zaune a inda ya barta amma idanunta a rufe suke.
“Aysha… Aysha… Aysha… sai da ya kirata sunanta ya fi a qirga amma bata amsa ba.
“Aysha don Allah ki yi mini magana mana.”
Nan ma dai shiru ta yi bata bashi amsa ba. Tabbas bata da lafiya domin duk miskilancinta idan ya hadata da Allah tana amsa masa, don haka ya yi tunanin ko ta yi barci ne.
***
Yana zaune yana jan casbaha bayan ya idar da nafilfilin dashi kanshi bai san iya adadin raka’o’in da ya yi ba, lokaci zuwa lokaci yana mai da idanunshi kan faffadan gadon dake gefensa qirar Italiya, inda ya kwantar da ita ba tare da ta san a wane hali take ciki ba.
Kallon a gogon bangon dake maqale a dakin yayi wanda ya nuna masa qarfe hudi daidai na asubahi, hakan shiya tabbatar masa da awanni uku kenan da kwantar da ita a kan gado, domin bai bar gidan abincin ba sai wajen qarfe daya saura kwata na dare, bayan duk jama’a sun gama watsewa.
Motoci biyar suka rage a gurin biyu daga ciki tasu ce shi da Aysha, uku kuma baisan mamallakansu ba, motarshi ya matsar kusa da in da ta faka tata motar, da bisimillah ya dauko ta cak ya kwantar da ita a bayan tashi motar, idanunshi a runtse, yana jin wani iri a zuciyarsa.
Sannan ya kwashe wayoyinta da kudi da duk wani abu muhimmi da yake cikin motar Aysha.
Haka nan ya bar motar tata a gurin kuma a bude, a zuciyarshi yake addu’ar
“Ya Allah ga ajiyar motar Aysha nan.”
Har ya isa muhallinshi bata san a ina kanta yake ba, don haka ya sake daukarta cak kamar ‘yar qaramar yarinya har zuwa Bed room dinsa, a zuciyarsa yana ta istigfari.
Tashi yayi daga kan dardumar da hanzari kamar ya yi mantuwar wani muhimmin abu yana buqatar ya je ya dauko. Kofi ya dauka a saman frig sannan ya dauki robar ruwan Swan mara sanyi ya nufi gadon da take kwance, fuskarta fayau a idanunsa sai yaga ta qara masa kyau fiye da da domin bai ta6a mata kallon qurilla irin na yau ba.
Addu’o’I yake ta tofawa kala kala a ruwan da ya zuba a cikin kofin da yake hannunsa, sai da ya dauki tsawon minti goma yana addu’a sannan ya fara shafa mata ruwan addu’ar a fuskarta bakinshi dauke da Bisimillah, tsawon lokaci yana shafa mata ruwan addua har ladanin unguwarsu ya kwad'a kiran sallar farko na asubahi, kan frige ya ajiye kofin sannan ya nufi bandaki ya sake dauro alwalar sallar asubahi.
Tana zaune daram a kan gadon tana bin lougo da saqo na dakin da kallo don tantance shin a ina take?
Bata tantance ba ta ji motsin bude qofa don haka ta maida kallon ta gurin don ganin mai shigowa, idanunta a cikin nashi sukai musayar kallo tsawon minti daya, shine ya fara saukar da kwayar idanun shi sannan ya qara fadada fara’ar fuskar shi yana fadin,
“Alhamdulillahi kin tashi?”
Har a wannan lokacin bata sauke qwayar idanunta ta daga kanshi ba, kallo daya ta yi mishi ta gane shi, dan Sandan nan ne da yake neman takurawa rayuwar ta.
Daure fuska ta yi dam! sannan ta watsa masa harara cikin masifa tace
“kai malam! menen gaminka dani kake neman takura min? Ina yar uwa ta Sadiya?"
Ta watsa mishi tambayar duk da bata da tabbacin ya ganta ko bai gan taba.
Saida ya tatusasa muryarshi kasa-kasa sannan ya fara magana da cewa
“Ki kwantar da hankali ki don Allah Aysha, wallahi bani da nufin cutar da ke, yanzu dai kinga na yi alwala zan tafi masallaci, ki bari idan na dawo sai muyi maganar"
Da baya da baya yake tafiya yana kallonta har ya fice daga dakin yayin da ita kuma take watsa mishi harara tana huci har ya 6ace wa ganin ta.
Tana zaune a inda ya barta har ya dawo daga masallaci, da sallama ya shigo cikin dakin! sanin daraja da ladan da yake tattare da amsa sallama yasa ta amsa masa a ciki ciki, don bata tunanin ya ji abinda tace.
Har ya nemi gurin ya zauna daga can gefan gadon bata fasa kallon shi tana watsa masa harara ba.
“Idan kika daure fuska qara kyau kike yi, idan kika harareni wani sanyi da farin ciki ne ke kwarara a cikin zuciyata, don Allah ki ciga ba da harara ta.”
Ya fadi hakan murya kasa kasa yana watso mata murmushi.
Tabe baki tayi tana kallon shi haushin shi yana qara cika mata zuciya.
“Ina ‘yar uwata Sady?”
Shiru yayi na ‘yan mintuna ba tare da ya bata amsata ba, har sai da ta sake maimaita masa cikin daga murya.
“Kwantar da hankalinki Aysha, Sadiya tana cikin qoshin lafiya da yaddar Allah. idan anjima gari ya waye zan dauke ki muje gurinta.”
Hayayyako masa tayi da masifa tana cewa
“Menene nufinka da ka dauko ni zuwa nan ko an faxa maka a daji nake kwana? Kai wai ma miye gami na da kai?.”
“Allah ya baki haquri. gani na yi baki da lafiya, a tunanina zanyi gwaninta idan har na taimaka miki"
“To ba kai gwaninta ba, kuma ban gode ba. Har abada bazaka ta6a yin abinda zanji ka min gwaninta ba"
Ta fada tana murguda mishi baki, gabas da yamma.
“Da yake daman can ba don ke na yi ba, na yi ne don Allah kuma don masoyiya ta.
Ya fadi haka idanunshi na kanta don jin amsar da zata bashi.
“Masoyiya? Wace ce masoyiyar taka?”
Ta watsa masa tambayar tana kallonshi da madaukakiyar mamaki a fuskarta.
“Aysha Azzahara’u ce masoyiyar tawa, tsananin son da nake mata yasa bazan ganta a cikin wani mawuyacin hali na kasa taimaka mata ba, ko da kuwa da zan rasa rayuwata ne"
Ta6e baki tayi a lalace, sannan ta kalleshi sama da kasa ta watsar, sannan tace
“Allah ya kyauta… Aysha ta yi a sarar masoyi…”
“A ganinki ko? ni dai na san a duniya babu wanda ya kai Aysha da ce da masoyi, sabo da tsanain son da yake mata ya sanyawa kansa bibiyar al’amuranta ba tare da saninta ba, a hakan kike ganin tayi a sarar masoyi?”
A yanzu kam kallon wahalalle take masa, kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta budi baki ta ce,
"Ai saka ba da himma, amma ka sani bazaka ta6a cimma burinka ba.”
“Kin san me Ubangiji zai zartar a gobe ne?”
Ya tambayeta yana mai kallon qwayar idanunta.
Bata kalleshi ba kuma bata bashi amsa illah kwantar da kanta data yi a kan filo ta runtse idanunta.
Ganin hakan da ya yi yasa ya nufi falo ya kwanta a kan kejera yana tunanin maganganun da suka yi da ita, shi kadai yake yiwa kansa murmushi, wani dad'i da farin ciki yana kwarara a cikin zuciyar shi, babu abinda ya fi tsaya masa a rai illah yanda take juya dan qaramin bakinta tana masa tsiwa a kan duk maganar da ya yi mata.
Qarfe takwas na safe ta ji ficewar shi da mota, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi domin tana tunanin Sadiya ya je daukowa kamar yadda yayi mata alqawari, minti arba’in tsakani ta ji dawowar shi da sauri ta nufi hanyar da taga yabi lokacin da zai tafi sallar asubahi, a falo ta ja ta tsaya don jiran qarasowar su, hannunsa ta gani dauke da ledoji manya manya guda biyu, ganin ya maida qofar ya rufe ya tabbatar mata shi kadai ne babu Sadiya.
“Ina Sadiyar?”
Ta tambaye shi bayan ta tare masa hanyar wucewa Bed room.
Murmushi ya yi sannan yaja ya tsaya ya zuba mata kyawawan idanunshi, minti daya suna musayar kallo daga bisani yace,
“Haba Baby..! ai a ganina sannu da zuwa ya kamata ki fara yi mini a matsayina na mai shirin zama mijinki…”
“A ganinka ka ce koh? Don haka ni banyi niyya ba, ina ‘yar uwata na tambayeka ba dogon surutu ba”
Ta fada bayan ta katse maganar daya fara yi tun kafin ya sauke numfashi.
“Baby rigima ko? ‘yar uwar ki tana cikin qoshin lafiya, wanka zan yi muyi break fast sai in dauko miki ita.”
Haushi da takaici ne ya cika mata ciki, wai ta ya ya ma wannan dan nacin ya samu nasarar dauko ta zuwa gidanshi? Ta tambayi kanta a cikin zuciyar ta.
“Yi haquri, ga doguwar riga da hijabi na siyo miki ki yi wanka ki yi sallah sai mu yi break fast, daga haka abu na gaba a gareni shi ne dauko miki Sadiya don samun kwanciyar hankalin matata Aysha.”
Bata kalleshi ba kuma bata amsa masa ba, illah juyawa da ta yi zuwa cikin bed room din da ta tsinci kanta tun data farko.
Bayanta ya bi da kallo, a zuciyar shi yake addu’ar Allah ya mallaka masa Aysha a matsayin matar aure,
“Amin” ya amsa a fili, sannan ya sunkuci leda daya ya bi bayanta zuwa cikin bed room din.
Tana zaune a gefen gadon daya mamaye fiye da rabin dakin, ta dora qafa daya kan daya tana kadawa, ta hada girar sama data kasa. Yana shigowa ta watsa idanunta a kanshi, ta rasa abinda zata ce don haka ta cigaba da kallonshi har ya zazzage kayan cikin ledar a kusa da inda take zaune.
“Ga bandaki can ki shiga ki yi wanka ki canza kayan jikinki ki bada faralin sallar da yake kanki, duk dogayen riguna ne, domin nafi qaunar ganinki a cikin doguwar riga kafin muyi aure…”