← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa diyar albarka, Ubangiji Allah ya yi miki albarka”
Yayi mata addu’a da muryarsa dake tabbatar da yayi farin ciki da saurin bin umarninshi da ta yi ba tare da musu ko gardama ba.
“Amin summa Amin" suka amsa tare da Abdul, sulalewa Aysha ta yi zuwa cikin daki don ta je ta bada faralin sallolin da suke kanta ta Magariba da Isha’i. wani sanyi da dadi ne ke kwarara a zuciyar Aysha domin yau ne karo na farko da wani DA NAMIJI ya sanya mata albarka.
WARWARA
Zaman minti biyar suka yi a babban falon da Ardo yake ganawa da baqi na qofar gida. babu wanda yaga shigowar su cikin falon a mutanen gidan, kuma Ardon bai nemi su shiga cikin gidan ba, sai umarni da yayi wa Abdul ya bude fridge din falon ya dauko musu ruwan sha da kofuna.
Qarfe goma sha biyu da rabi na rana a garin Yola ta yi wa su Abdul da Aysha, kasancewar jirgi suka hau kuma da suka isa shatar mota ya daukar musu har zuwa tafkeken Family House dinsu. Bayan musayar gaisuwa da suka yi tsakanin Ardo da Aysha sai sunkuyar da kai da ta yi cikin matsananciyar kunya, Abdul kam ko ba a fada ba an san farin ciki ne fal a cikinshi, yana zaune a dan nesa da inda Aysha take ya kalli Arxo ya kalleta.

“Anya kuwa ita ce Aishar dana gani a hoto Modibbo?”
Ya tambaya yana kallon Abdul cikin yanayi na tsokana.
“Qwarai itace Ardo, me kaga ta yi?”
“Gani na yi tafi wacce na gani a hoto kyau nesa ba kusa ba, anya bazanyi maka juyin mulki ba? don tafi dacewa dani ba kai ba”

“Haba dai Ardo, me zata yi da tsoho bayan ga sabon jini? ai tsoho sai su Adda da suka ga jiya suka ga yau!”

“Aisha wai ba zaki auri tsoho ba?”
Ardo ya tambayi Aysha yana dariya cikin nishadi, murmushi kawai Aysha ta yi gami da sake sunkuyar da kai qasa cikin kunya mai tsanini, kwarjini da girman farin dattijon su suka hanata sakewa, ji take kamar qasa ta tsage ta shige don kunya.

Sallamar da a ka doka a qofar falon ita tasa Aysha dago kanta da sauri tana kallon hanyar shigowa, da Ardo da Abdul suka mai hankali gurin amsa sallamar gamida bada umarnin shigowa.
Aunty Hassana da Aunty Hussaina ne tare da mahaifinsu mijin Ammi Zahra’u, wacce ta zame wa Aysha Uwa da Uba da dangi gaba daya.
Duk da tun lokacin sasuwar Ammi Aysha taga Dattijon tana da shekaru goma sha biyu ne a duniya hakan bai hana yanzu da ta ganshi ta shaida fuskar sa ba.
“Oyoyo Aunty Hassana.”
Aysha ta fada cikin murna tare da ta shi da sassarfa ta isa gareta ta rungumeta sannan ta koma kan Aunty Hussaina ta rungumeta tana dariya don tsananin farin cikin ganinsu. Har qasa Aysha ta durqusa ta gaida Abbansu Aunty Hassana, ya amsa mata cikin sakin fuska da walwala.
“Diyar Zahra’u ta girma sosai, me kuke bata Hassana?”
Dattijon ya tambayi Aunty Hassana fuskarshi qunshe da murmushi yana kallon Aysha, kunya tasa Aysha ta boye fuskarta a jikin Aunty Hussaina tana murmushi. Da fara’a a fuskokinsu tamkar sun ta6a ganin juna suka gaisa tsakaninsu, sannan Dattijon mai farin gashi duk jikinsa ya rungume Ardo suka sake yin gaisuwa irinta larabawa, har qasa su Aunty Hassana suka tsugunna suka gaida Ardo shima Abdul ya tsugunna cikin ladabi ya gaida Abbansu Aunty Hussaina, da fara’a ya amsa masa sannan suka yi gaisuwa a tsakanin su da Aunty Hassana. Mamaki ne fal a zuciyar Abdul ganin wadannan kyawawan larabawan ‘yan biyu kuma kyawawan ‘yan mata masu kama da Aysha. idan bai manta ba Aysha ta sanar dashi zai iya auran wadda batada da dangi? amma ga wadannan ‘yan biyu abinda ya raba kamanninsu da Aysha kan ne su farare ne tas yayinda ita kuma bata kaisu haske ba. A yanda Abdul ya fahimta shine a kwai sanayya ta ‘yan uwantaka tsakanin Aysha da ‘yan matan. da shaquwa mai tsanani tsakaninsu.
Abbansu Hussaina ya ce,
“Hussaina sai ku sallami qanwar taku koh?”
ya fadi hakan yana kallonsu daya bayan daya. robar ruwan swan wanda Aysha bata lura dashi ba a hannun Aunty Hassana ta miqo mata, ruwa ne fari tas a cikin sa amma bai kai rabin robar ba.
Hussaina ta ce,
“Shanye ruwan cikin robar nan yanzu Aysha"
Ba tare da wani tunani ba ko kokwanto a zuciyarta ta bude robar ruwan ta kai bakinta bata ajiye ba sai da ta shanye ruwan ciki gaba daya! Aunty Hassana ce ta amshi robar ruwan a hannun Aysha ta a jiye a gefe, ganin duk sun maida hankalinsu a kanta yasa mamaki da shakku suka fara qoqarin kawo farmaki a zuciyarta, bata sami damar yin tunani ba saboda wani barci mai qarfi da yayi awon gaba da ita ta sulale ta kwanta a jikin Aunty Hussaina da take zaune kusa da ita.Aunty Hussaina ce ta cire dan qaramin hijabin dake jikin Aysha gashin kanta mai laushi da santsi ya bayyana, mahaifin nasu ne ya matsa daf da inda take kwance ya tofa mata addu’a a tsakiyar kanta sannan suka dan ninka suka rufe mata gashin kanta, suka maida hankalinsu gaba daya kan mahaifinsu.
Atishawa Aysha ta saki mai qarfi har guda uku, amma duk da haka bata farka daga barcin da ya yi awon gaba da ita ba.

“Alhamdulillah.”
Kalmar da mahaifinsu Hassana da Hussaina ya furta kenan sannan ya cigaba da janyo addu’oin bude majlisi cikin harshen larabci don samun albarkar Allah da manzonsa, sai da ya dauki tsawon minti goma yana jero addu’oin daga qarshe ya rufe addu’ar tashi da kalmar Assalamu alaikum.
Sai da ya jira suka amsa sallmar tashi sannan ya fara da cewa,
“Da farko dai sunana ABDUL YASSAR, wadannan da kuma ‘ya’yana ne ‘yan biyu da Ubangiji cikin baiwarsa ya azurtani dasu Hassana da Hussaina kamar yandna kuka ji Aisha ta kira sunansu, mu mun kasance daga cikin jinsin Aljanu amma musulmai masu bin Alqur’ani da sunnar Annabi (S.A.W)
Mu mazauna qasar Sa’udiyya tun kaka da kakanni, a taqaice dai a daren da za’a haifi wannan yarinya Aysha muka samu sa6ani tsakanina da mai dakina Zahra’u mahaifiyar su Hassana da Hussaina,cikin fushi ta bar qasar Sa’udiyya a wannan rana, kasancewar mu tafiyar mu ta aljanu ba daya ne da taku ta Bil’adama ba. Sai ta dira a kasar Nigeria. Tana ta yawo sai Allah ya nufeta da giftawa ta gidansu Aysha. lokacin ita mahaifiyar Aysha tana tsaka da naquda tana neman taimako a gurin Ubangiji har ta fara fitar da rai da rayuwar duniya ta ji ana gyara mata tsugunno domin jaririyar jikinta ta samu damar fitowa duniya cikin sauqi. A hannun matata Zahra’u aka haifi Aysha bayan rasuwar ita mahaifiyar ita Aishar, sai riqon Aishar ya ci gaba da kasancewa a hannun mai dakina Zahra’u, mahaifin Aysha yana daga cikin maza marasa adalci ga iyalansu shi yasa sam Zahra’u bata qaunarshi. Aysha ta taso da halaye irin namu na aljanu. kadan daga cikinsu sune tana da kaifin qwaqwalwa duk da qarancin shekarunta, Tana da dauriya da Juriya da rashin tsoro, ba kamar bil’adama ba, tana da zafin nama da yin wasu abubuwa da sam bil’adama bazai iya ba. shekarun Aysha sha biyu a duniya Allah ya dauki ran mai dakina kuma uwar goyon Aysha. kafin rasuwar ta ne ta saka wasu hadimanta a jikin Aysha, shi yasa duk mai nufin cuta ga Aisha baya samun nasarar isar hannunshi jikinta. Idan ranta ya baci takan kwanta wani haske ya zagayeta wannan daga cikin aikin hadiman Zahra’u ne, tanada qarfin da bil’adama bashi dashi. A idanun namun daji sukan ganta ta zama naman dawa shi yasa har ta yi rayuwa shekara guda a dajin babu dabbar data ta6a yunqurin cutar da ita. Wadannan duk aikin hadiman Zahra’u ne, a ranar da Zahra’u ta koma ga Ubangiji ne na tofa wata addu’a a kan Aysha ta yi barci bata farka ta ganta a ko ina ba sai gidan mahaifinta, wannan addu’a da nayi mata shine sanadin da sam bata iya barci da kanta idan har ba irin addu’ar aka sake yi mata ba, rashin samun hakan da kuma son ta yi barci yasa har wani namiji ya koya mata shan kayan maye, shi kanshi yaron bai samu nasarar hakan ba sai a dalilin abu daya, A lokacin da Zahra’u ta rasu mun dauki gawarta zuwa Sa’udiyya ni da su Hassana da sauran hadimanmu ciki har da wadanda suke jikin Aysha, wannan dalilin ne yasa ya samu nasara a kan Aysha na koya mata shan kayan maye.

Dawowar hadiman Zahra’u jikin Aysha suka iske wannan baqon al’amari sunyi matuqar baqin ciki da ganin haka, duk yanda suka so hana ta shan kayan mayen al’amarin yaqi yiwuwa da yake komai sai Allah yaso da taimakon addu’a suke dakusar da qarfin kowace qwaya da tasha bata wuce awanni biyar tana barci, a yanzu dai mun fitar da hadiman mu daga jikin Aysha, kuma daga yau in Allah ya yarda ba zata sake shan wani abu don samun barci ba, zata ringa barci lafiya kamar kowane bil’adama. Duk wani taurin zuciya da taurin kai mun fitar mata dasu, jarumtar da hadiman suke bata da yanzu duk mun kaudasu. Ba komai ne yasa muka yi hakan ba sai don mun yi istahara munga kune mutanen da zasu iya tsayuwa a kan al’amarin Aysha, amma duk da haka zamu ringa bibiyar al’amuranta lokaci zuwa lokaci, kuma duk sanda take cikin mawuyacin hali zamu taimaka mata.”

Bayan Aunty Hassana ta lura ya gama bayaninsa sai ta fara bai wa su Ardo tarihin rayuwar Aysha kamar yanda ta fada a baya, sannan ta qara da tabbatar da duk wani abu daya kusance ta suna sanar da ita ta hanyar saqo a wayar hannunta da lamba 777, ko bayani a kan rasuwar Sadiya saboda wayoyinta suna ajiye a gurin Abdul ne shi yasa basu tura mata ba. sannan ta ce,
“Da fatan zaku kasance masu tsayuwa a kan al’amarinta kamar yanda Abbanmu ya fada a baya.”

Aunty Hussaina ta sauke numfashi ta ce,
"Muna tsananin son godiyarmu bazamu bari wani abu ya cutar da ita ba.”
Chapter 13 · 0% Book details