← Book details A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

A Dalilin Da Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Abdul ya sauke mai qarfi gami da zuba mata idanu kamar zai hadiyeta.
A kunyace ta miqe zuwa cikin bedroom har tana hardewa da qafafunta sabo da kallon qurilla da yake binta dashi. Minti biyar da shigarta dakin ta ji alamun ficewarshi daga gidan.
***
Tunda suka ga qarfe biyu na dare ya yi Aysha da Sadiya basu dawo ba hankalinsu yayi mummunar tashi, a wannan rana babu wacce tayi barci a gidan suna zaune jigum jigum a falo da casbaha a hannayensu suna ja, domin tabbas sunsan babu lafiya.

Baba Jummala tana zaune a kan darduma bayan ta idar da nafilfili, ta dad'e tana adduo’I a cikin sujjadarta tana roqon Allah ya tsaresu Aysha a duk halin da suke ciki. Fatima kam tana jan carbi tana hawaye, a fili take addu’ar kada Allah yasa wani mumunan abu ne ya faru dasu, idan wani abu ne ya samu su Aysha ya zasuyi? Tun a cikin daren Safiyya da Rahma suka fara tunanin ko zasu fita don bin bayansu.

Baba jummala ta ce,
“A yanzu bamu da tabbacin a wane hali suke ciki, amma mu jira idan gari ya waye zuwa qarfe goma na safe idan basu dawo ba sai abi bayan su"
Suhaila ta ce,
“Amma fa Baba Jummala idan kika duba irin haka bata ta6a faruwa ba.”

Safiyya tace,
“Hakane Suhaila, amma bari mu jira zuwa safiyar kamar yanda Baba ta yi umarni"

Har gari ya waye babu wani labari a kan rashin ganin Aysha da Sadiya, kuma tsananin damuwa ta hana su kunna T.V balle su san halin da ake ciki.
Da ruwan tea da burodi kawai suka iya karyawa domin damuwa da tunani ya hana Baba Jummala shiga kiching, ruwan shayin ma sai Safiyya ce ta dora. Qarfe goma dai dai suka gama shiryawa don shiga cikin garin Kaduna da niyyar bin kowane gidan cin abinci dasu Aysha suka ta6a zuwa.
Har qarfe hudu na yamma basu samu inda su Aysha suke ba, sai daga qarshe suka yi tunanin su je BBQ, gidan wani abinci ne da yake tashe a garin Kaduna. Suna zuwa gurin suka yi fakin da motocinsu, basu shiga ciki ba sai da suka fara duba motocin da suka yi fakin a gurin, daya bayan daya, da tsananin mamaki suke kallon motar su Aysha.

Rahma ta ce, “Ai a bude take”
Ta fada da sauri bayan ta kama qofar mai zama kusa da Driver taga ya bude, amma duk wani muhimmin abu an kwashe.
“Da ganin yanda aka bar motar nan a bude babu lafiya”
Safiyya ce ta fadi haka bayan sun gama duba ko ina a cikin motar. Suka maida motar suka rufe gami da kutsa kansu cikin gidan abincin. Duk iya binciken da ya kamata suyi sunyi, amma sam basu ga alamarsu Aysha ba. Hankalinsu ya qara tashi suka fito daga ciki suna tunanin abinda ya kamata suyi na gaba.

Gurin mai sai da ice cream suka nufa suna tambayarsa ko yaga masu motar can tun jiya da daddare?

Mai shagon ya amsa da
“A’a amma dai har na kulle shagona jiya da daddare misalin sha biyu na bar waccen motar tana nan da kuma wani mutum da ya tambayeni ko naga wata yarinya ta sanya doguwar riga ta wuce ta nan, tunda na amsa masa ban ganta ba ya bar gurin nan amma har na tashi yana nan tsaye a gurin waccen motar da kuka nuna min”

“Innan lillahi wa’innan ilaihir raji’un.” Abinda suke ta maimaitawa kenan har suka zauna a cikin motar da suka je neman su Aysha da ita.
“Me kuka fahimta da bayanin da mai shagon can ya yi mana?”
Nafisa ta tambaya tana kallonsu daya bayan daya. Siyama tace,
“Kamar shi wannan mutumin yana tambaya ne a kan Sadiya don jiya baqar doguwar riga ta sanya, Aysha kuma ta sanya kananun kaya”
Ta fadi hakan tana kallonsu don jin ko hasashenta dai dai ne.

“Qwarai tunaninki hakane, amma abin dubawar shine miye hadin mutumin da Sadiya har yake tambayar ko anga inda ta shiga bayan ta fito daga gidan abincin? Kunga wannan maganar tana nuna ba a san in da Sadiya ta shiga ba. To idan hakane Aysha tana ina a wannan lokacin da abin ya faru? Miye hadin Aysha da wannan mutumin da har zai san Sadiya ta 6ata daga bakin Aysha? Me ya kaishi gurin motar dasu Aysha suka fita da ita? Waye ya kwashe kudi da takardun da suke cikin waccen motar? Ina Aysha ta shiga? Idan kuma tabi wannan mutumin ne mai zaisa ta bishi bayan duk irin tsanar da tayi wa ‘Ya‘ya Maza?”

Rahma tace, “Ni wallahi kai na duk ya kulle, na rasa irin tunanin daya kamata inyi"
Ta karasa fadin haka fuskarta na bayyana tsananin damuwa.
“Ina ganin ya kamata mu koma gida, ko zamu samu nutsuwar yin tunanin abinda ya dace"
Safiyya tayi wannan furuci tana kallon su baki daya.
Sama Suhaila ta daga kanta tana mai fadin,
“Ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar da take tunkararmu”

Baki dayansu suka amsa da "Amin"
Nan take Siyama ta juya kan motar dan komawa gida.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” kalmar da Baba Jummala da Fatima suke ta maimaitawa kenan bayan Suhaila ta gama kora musu bayanin duk abinda suka ji kuma suka gani bayan fitarsu.

Baba Jummala ta fara magana tana dubansu gaba daya
“Abinda nake so ku fahimta kuma kusa a zauciyarku shine, tabbas Aysha tana nan a raye, kuma duk in da take muna zuciyarta, domin matuqar Aysha ta rasu to tabbas sai munji a jikinmu da zuciyarmu. Sadiya ce kawai bamu san tana raye ko ta mace ba, amma nasan matuqar Aysha tana raye sai tabi duk hanyar da ya kamata don ku6utar da Sadiya su dawo garemu a tare, duk in da Aysha take zata dawo garemu idan lokaci yayi, don haka daga yau ba zamu sake fita nemanta ba sai dai mu cigaba da yi mata addu’a”
***
Yau Litinin wanda yayi daidai da kwanakin Aysha uku kenan a gidan Abdul-Ahad kuma a wannan ranar ce Abdul ya tabbatar mata zai fara binciken sanadin rasuwar Sadiya gadan gadan, don a wannan rana Sadiya ta cika kwanaki uku da rasuwa.
Bayan gama binciken likitoci da shige da ficen da Abdul yayi ya samu aka bada gawar Sadiya don kaita makwancinta na gaskiya.

Limamin masallacin da yake sallah ya samu ya yi masa bayanin komai har ya fahimce shi. Ba tare da wata matsala ba akai jana’izar Sadiya da taimakon Abdul da taimakon wannan Limamin.

Aysha na sanye da sket na English wears daya daga cikin kayan da Abdul ya qara kawo mata ranar wata asabar, yana zaune a kan kushin yana shan tea cikin sauri, a lokacin agogo ya buga qarfe bakwai da kwata na safe. Sanye yake cikin kakinshi na ‘yan sanda wanda yai matuqar yi masa kyau.
Aysha na zaune a qasa nesa kadan da inda yake zaune, tunda ta daga kai ta kalleshi sau daya bata sake kallonshi ba. Ba a yi minti biyu ba ta fara hamma saboda tsananin barci da take ji, kusan kwana ta yi tana kuka duk idanunta sun kumbura shi yasa bata son hada ido da shi.

“Aysha?”
Ya kira sunanta a sanyaye gami da katse mata tunanin da take yi.

A sanyaye ta amsa da “Na’am!” ba tare da ta kalle shi ba
“Ki dago kanki ki kalleni mana, magana mai muhimmanci nake so muyi"
Ya fadi haka yana daga inda yake zaune. Bata dago kai ba kuma bata kalleshi ba illah sake kauda kanta gefe data sake yi.

Har kusa da inda take zaune ya matsa ya sanya hannu ya dago fuskarta, idanunta a cikin nashi da sauri ya saki fuskarta yana fadin
"Subhanallahi me yake damunki Aysha? kuka kikai a daren jiya ko?”

Wani sabon hawaye ne ya gangaro a Idanunta tayi shiru ba tare da ta furta komai ba.
“Oh My God menene ne haka? Ki fada mini damuwar ki mana?”
Ya fadi hakan cikin tsawa yana zaro mata idanu.
A tsorace ta dago ta kalleshi, cikin rawar murya ta ce,
“Ni….Ni…Ni barci nake so nayi kuma barcin ya qi zuwa….saboda….saboda ban sha maganin da na ke sha…ba.."

Da mamaki ya kalleta, sannan ya ce, “Kina nufin sai kinsha wani magani ki ke iya barci?”
Kai kawai ta iya daga masa, alamar “Eh”

Daki ya shiga da sauri ya fito da Memo da Biro ya miqo mata
“Rubuta irin maganin da kike sha da duk wani abu da kike buqata in je in kawo miki.”

Tafe Abdul yake a cikin mota cikin tsananin tashin hankali da sanyin jiki, me yake shirin gani ne? Aysha tana shaye shaye ne kenan? Kuma duk tsawon wadannan kwanaki ukun da tayi a gidanshi bata iya barci saboda rashin shan kayan maye? Hasbunallah wani’imal wakil.
Wayarsa ya janyo ya kira Number Ardo bayan ya faka motar tashi a gefen titi, a hannunshi na hagu peper da Aysha ta rubuta masa irin maganin da zai siyo mata ne.
“Hello Ardo ni fa ina cikin rudani a kan al’amarin wannan yarinyar, kaina yana neman bugawa…”
Abinda ya fara gayawa Ardon kenan bayan sun gama gaisawa.
Saida tsohon yayi dariya irin tasu ta manya sannan ya ce,
“Na sani Modibbo, ka kwantar da hankalinka, kuma duk wani baqon al’amari da zaka gani a tattare da ita kada ka tsananta bincike, kai mata duk abinda take so, amma kada ka sake ka barta ta koma cikin ‘yan uwanta. Lokaci ya kusa da zaka samu duk wani amsar tambaya a kan rayuwar Aysha. Ka qara haquri har zuwa wannan lokacin.”
Da haka suka yi sallama da Ardo bayan ya fada masa maganganu masu sanyi da kwantar da hankali.

“Zan tafi Office Aysha. ki kwanta ki yi barci idan kinsha maganin, duk wani abu da kike da buqata ki duba kichen ko kan dining ko kuma Bed room suna nan. Yau ne zan ziyarci unguwar Zango, dan bincike na musamman a kan wadanda suka kashe Sadiya, buqatata kawai ki yi mini addu’a.”
Chapter 8 · 0% Book details