Sashe 9
Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fita tabi bayansa da kallo shi ko kunya baya ji, kitchen ta wuce ta dauko abincin zuwa part dinsa abinda ta gani yayi mutukar tayar mata da hankali da kuma bata tsoro dan mata da maza ne wurin su takwas ciki harda wannan katuwar budurwar tasa da take yawan ganin su tare wadda mommy bata so sannan tayi iya bakin kokarin ta akan ya rabu da ita amma yaƙi rabuwa da ita, daga matan har mazan duk ta fuskanci basu da kunya da nutsuwa shiyasa tana ajiye musu abincin tayi tafiyar ta domin zama ne na rashin kamun kai da rashin kunya duk da dama ba wai yau ne ta saba ganin su shida budurwar sa zaune kujera ɗaya ba wani cikin jikin wani, in banda warin sigari babu abinda part din nasa keyi tun daga hanyar shiga, tana fitowa taji an saki kiɗa waƙar turanci na faman tashi wacce ta karaɗe gaba ɗaya ilahirin kafatanin cikin gidan kuma tun da suka kunna kidan nan har 1 na dare basu kashe ba ta yuyu ko sun shirya kwanan zaune ne, ita kam tashi tayi zaune dan ta kasa bacci saboda hayaniya da kuma ƙarar kidan dake tashi, lallai sai yau ta sake yarda da cewa mommy babbar katanga ce dake tareshi da aikata ɓarna da sakin layi tunda yanzu dai gashi daga tafiyar ta yau har ya fara raba hali, kanta ta dafe saboda wani irin ciwo da taji yana yi mata sakamakon rashin bacci da kuma tarin gajiyar da take dauke da ita gefe guda kuma ga hayaniya da sautin da kunnuwanta basu da bukatar ji cikin wannan lokaci, kwanan zaune tayi saboda yadda ba suyi bacci ba haka itama ta gagara bacci har wurin asubah kuma su dinma basu tsagaita da hayaniyar da suke yi ba sai da aka yi asubah sai lokacin ta fara jin ƙarar motoci suna fita daga gidan daya bayan daya illa shi da Najla ne kadai suka rage, kashe komai yayi suka kwanta sai bacci wanda basu tashi ba sai azahar dan lokacin har an idar da sallar azahar domin misalin ƙarfe 2:30 ne na rana, kai tsaye part din mommy ya shiga domin samo musu abinda zasu ci shida yar lelen tasa wadda ko ƙuda baya son yaga ya taɓata,
Imaan na zaune tana tsefe kitson kanta ta tara jiyo kiran nasa kamar yadda ya saba kira na rashin arziki dan ko sunan ta wahala yake masa kai bama iya wahala kadai ba bama ya cikin lissafinsa shiyasa ya kasa riƙeshi har yau, itama hakan bai dameta ba sai dai amma bata son wanna uwanin da yake kiranta dashi saboda ko a rubuce bai yi kama da irin sunanta ba,
"kinyi mana breakfast?"
Kai ta girgiza alamar a'a,
"ki shiga ki hada mana breakfast ki kawo mana yanzu yanzun nan...."
"toh...." Juyawa yayi ya fita ita kuma ta shiga kitchen ta hada tea ta soya ƙwai sannan ta dauki bread ta fita, har lokacin ba wai sun tashi daga baccin bane a bisa dukkan alamu dan jiya kwana suka yi suna jin kide kide da shaye shaye, breakfast din ta ajiye musu tana ƙokarin tafiya taji muryar Najla,
"ke... Me kika kawo?"
"tea ne da bread sai ƙwai...."
"Bana yin breakfast da tea da bread..... Kije ki soya min dankali sannan kiyi min sos din hanta ko ƙoda sannan ki dafa min noodles......."
Shuru tayi tai tsaye tana kallonta,
"me kike jira? Ko baki ji abinda ta fada bane?"
"naji"
"then lost...." ya fada yana yatsina fuska, fita tayi a ranta tana tausayin rayuwarsu dan yanzu kuma sai taji ma sun fara bata tausayi wannan wacce irin rayuwa ce? Bata jin sun yi koda sallar asubah bare ta azahar dan kwana suka yi suna jin raye raye, kitchen ta shiga ta soma shirya abinda aka sakata kamar yadda ya bata umarni tana yi tana tsaki saboda ta fahimci kamar wannan Najla din tana da tsirfa da iyayin masifa banda haka menene na sakata a gaba tana bata umarni irin haka kamar itace ta dauketa aiki ko kuma kaman zamanta take yi. Ta gama fere dankalin tana soyawa ta jiyo ƙarar wayarta ta hannu ƴar karamar Nokia keypad wadda mommy ta siya mata wacce ke ajiye can gefe guda, da hanzarinta taje ta dauka dan ta san baya wuce mommy ai kuwa ita dince nan ta dauka fuskar ta cike da fara'a ta amsa da sallama, tambayar farko da mommy din ta fara yi mata bayan sun gaisa shine Anaam ya kwana a gida? Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ja wani gwauron numfashi sannan cikin taushin murya tace,
"mommy ya kwana a gida amma gaskiya akwai matsala saboda jiya kwana suka yi suna Kade kade da hayaniya acikin gidan nan shida abokansa da kawayenshi...... Basu runtsa ba haka ma basu bar jama'ar gidan nan sun runtsa ba har sai bayan asubah......." shuru tayi sakamakon jin motsin da tayi daga bayanta tana juyawa ta ganshi tsaye idanuwansa jajur,
" am mommy ina aiki ne zuwa anjima za muyi magana... " ba tare da ta jira cewar mommy ba ta kashe wayar ƙit ta koma gaban kaskon da take soya dankalin,
" idan kin gama munafurcin da gulmar ki kawo mana..." daga haka ya juya ya fita yana harararta, jikinta duk a sanyaye ta hada komai ta dauka ta nufi part dinsa, to amma ai ba karya tayi musu ba abinda ya faru ne ta fada ba wai sharri tayi ko ƙage ba,
Samun sa tayi zaune kusa da Najla hannunshi cikin nata tana faman murza wa gami da sunbatarsa, Anaam da mata sai Allah,
"ke me kika fadawa mommy?" taji muryar Najla tana tambayarta, shuru tayi bata amsa ba haka bata daga ko kai ta kallesu ba,
"munafuka, to ki bude kunnen ki da kyau kiji, wallahi muddin kika raba shi da mahaifiyarsa sai kin kwammace kida da karatu.... Shashasha kawai..... Nonsense...... Useless and hopeless...."
Juyawa tayi zata fita taji cikin tsawa yace mata "dawo nan, shiga ki gyara min bedroom da ko ina dake cikin part din nan akuya kawai daƙiƙiya...." duk abubuwan da suka fada mata babu wanda yafi bakanta mata rai da kuma bata haushi kamar yadda ya kira ta da akuya wai ita yake kwatantawa da akuya, kwalla ce ta zubo daga idonta a lokacin da take cikin bedroom din nasa tana gyarawa, tsaf tsaf ta gyara ko ina ta wanke toilet sannan ta fita har lokacin suna zaune falo suna ciyar da junansu abincin da ta kawo musu,
"ki dafa min sakwara da miyar ganda ita zamu ci da daddare...." ta ji murayarsa can ciki, "toh"
"nikuma tuwon shinkafa nake so miyar kubewa saboda na ɗan yi two days banci ba nikuma ka sanni da son tuwo babe...."
"toh" ta fada tare da Juyawa ta fice daga cikin falon tana jin zuciyar ta kamar zata faso ko kuma zata fashe saboda bakin ciki.......... ✍🏻
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
_*Ummi Shatu*_👌🏻
[8/8, 9:57 AM] Baby Aysher: ©️Love story 2025
*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA...!*
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
*8*
***Gaba ɗaya bata da hutu saboda aiki ne daga wannan sai wannan, wani na jiran wani kuma duk a kanta ita kaɗai tamkar baiwar da suka saka kuɗi suka siyo a kasuwa, daga shi har Najla rashin mutunci da tijara kawai suke zuba mata iya son ran su, su sakata aiki sannan su bita da baƙaƙen maganganu a maimakon gode matan da ya dace suyi,
Daren yau sai da ta zo kwanciya sannan abubuwan da suka faru a yau din suka fara dawo mata, macaroni Najla tace ta dafa mata sannan tayi mata farfesun kaji a matsayin abincin dare shi kuma yace ta dafa masa noodles ita zai ci, tana dab da gaba abincin taji fitar su daga gidan ya tafi ya kai ta shopping saboda dama taji suna maganar lokacin da ta shiga part din.
Koda ta kammala abincin ɗauka tayi ta kai musu part dinshi sannan ta dawo part din mommy ta cigaba da abubuwan dake gabanta, wurin lokacin sallar ishah suka dawo, tana kitchen tana dumama abincin da zata ci sai gashi ya shigo rai a ɓace,
"ke.... Ubanwa yasa ki dafa abincin baki jira sai lokacin da zamu ci ba? Kin dafa abu tun ɗazu duk sun sandare..... Maza je ki dauko ki zo kiyi warming dinsu banza ballagaza...." bata ko kalleshi ba ta bar abinda take yi ta fita zuwa part dinshi ta tattaro warmers din ta zo ta sake dumamawa duk da cewa ba wai sun huce bane, maganganun da ya fada mata ba suyi mata ciwo ba a lokacin da ya fada mata din sai da ta zo kwanciya sannan kalmar ballagaza da ya kira ta dashi ya fara sosa ranta kai anya ma kuwa yasan menene ma'anar ballagaza da har ya kirata dashi?, ji take kamar ta fashe da kuka ko zata ji sanyi cikin ranta amma kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya ƙi bawa kukan nata damar ya fito. Haka ta kwana da ɓacin ran abinda suka yi mata shi da Najla sai dai hakan bai hana su sake wulakantata ba kai kamar ma basu san abinda suke yi mata yana damunta ba, bata da yadda zata yi banda ta cigaba da rayuwa dasu a haka har zuwa lokacin da mommy zata dawo saboda ta san duk tsanani wuyarta mommyn ta dawo tana dawowa komai zai wuce sannan ya zama tarihi amma a halin yanzu dai tana aikatuwa sannan tana shan wulakanci kala kala.