← Book details Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Anaam what are you trying to do? Please rabu dashi mu tafi.... " bai saurare ta ba ya fincike ya nufi guy ɗin baiyi wata wata ba ya kwaɗa masa kwalbar a kanshi take kwalbar ta fashe ta farfasa masa kai jini ya ɓalle babu ɓata lokaci mutane suka fara taruwa a wurin, daƙyar Najla ta saka shi cikin mota suka tafi duk da ta san yaudarar kansu suka yi kawai amma dole sai wani abu ya biyo baya kamar yadda aka saba dan Anaam mugun dan zafin kai ne haka kuma cikakken ɗan rigima ne dan ba ya rabo da rikici kusan kullum cikinsa yake. Hotel ɗin da suke suka sake komawa kamar yadda rayuwarsa dama can shi tafi yawa a hotel.................. ✍🏻

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira dubu ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[8/2, 1:21 PM] Baby Aysher: ©️Love story 2025

*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA..!*

*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad :ummishatu*

*Arewabooks:ummishatu*

*2*

***Yanda taga jikin mommy har rawa yake saboda ɓacin rai hakan ya tabbatar mata ba lafiya ba sannan duk yadda akayi Anaam ya sake yin halin nasa wato ya ɗauko rigima ko wani abu mai kama da haka kamar yadda ya saba,

Kaiwa da kawowa kawai mommy keyi cikin falonta da waya a hannunta tana kiran layin wayar shi amma baya shiga saboda yasa wayar tashi a flight mood wato ta yadda ko an kirashi ba za a same shi ba,

"mommy lafiya kuwa?"

Imaan ta faɗa cikin damuwa domin tafi mintuna biyar tana tsaye tana kallon irin kai kawon da mommy ke yi,wuri mommy ta samu ta zauna kafin tace,

"Anaam ne ya fasawa wani yaro kai...."

"innalillahi....." ta fada bayan ta rufe bakinta da dukkan hannayenta, kai gaskiya wannan bawan Allahn baida tausayi dan ya jima yana jefa mahaifiyarsa cikin damuwa kuma har gobe bai hankalta ba bare asa ran zai saduda,

"Duk duniya bani da wata damuwa ko matsala sai Anaam..... Rigimar yau daban ta gobe daban......"

"mommy kiyi haƙuri insha Allah wata rana sai labari, Allah zai dawo dashi kan hanya...... Kiyi haƙuri....."

Shuru mommy tayi cike da ɓacin rai da damuwa dan ta kasa koda magana ma. Har dare wayarshi bata shiga ita dai mommy sai bacci ɓarawo amma da ƙyar ta iya bacci,

Kamar yadda jaddawalin aikinta yake part ɗin mommy kaɗai take gyarawa sai na Anaam haka ita ce ke yiwa mommy abincin da zata ci saboda ba komai mommy ɗin ke ci ba a yanzu duba da yanayin da take ciki na rashin cikakkiyar lafiya, sashen mommy ta fara gyarawa ta kunna turaren wuta ko ina ya ɗauki ƙamshi amma bata gyara bedroom ɗin mommy ba dan bata riga da ta tashi ba, kanta tsaye ta wuce bedroom ɗin Anaam kuma ba tare da tunanin komai ba ta bude ƙofar ɗakin ta shiga kai tsaye saboda ta san baya gidan kuma duk yadda akayi bai kwana a gidan ba, jin ɗakin tayi turniƙe da hayaƙi wanda bama zata gane ko hayaƙin menene ba saboda wani irin ƙauri yake yi marar daɗi, cikin sauri ta lalubi makunna ta kunna hasken lantarkin dake cikin bedroom ɗin, ganin shi tayi zaune gefen gadonshi duka kafafuwanshi na kan gadon ya jingina yana riƙe da shisha yana zuƙa, tsorata tayi dan daga shi sai gajeren wando, duvet yaja ya rufe jikinsa yana yi mata wani mugun kallo na ƙin jini kamar yadda ita ma taƙi nasa jinin,Juyawa tayi zata fita nan taji yace,

"ke ban hanaki shigo min bedroom kai tsaye ba....?"

"Ban san cewar ka dawo ba..." iya abinda ta faɗa kenan ta kaɗa kanta ta fita ta ja masa ƙofar dakinshi ta rufe, kitchen ɗin mommy ta wuce dan ɗora mata breakfast, wai ace tsabar rashin sanin ciwon kai mutum daga tashin sa daga bacci ya hau zubawa cikinsa hayaƙi dan rashin sanin darajar kai, ko tantama bata yi jiya bai dawo gidan nan ba sai bayan da ƙarfe biyu ta wuce na dare, yana can yana yawon bin mata da yan iskan abokai, tsaki ta ja tana girgiza kanta,lallai wata haihuwar babu komai acikinta face jarrabawa, haƙiƙa mommy na cikin jarrabawa. Hango shi tayi ta window ɗin cikin kitchen ɗin ya fito daga part ɗinsa sanye cikin bakaken kaya na sport, ji tayi ta gaza cigaba da abinda take yi kawai ta tsaya ta zuba masa ido tana kallonsa kamar tana son hango wani abu a tare dashi, sai bayan da ta ga shigarsa cikin sashe na musamman da aka tanada dan motsa jiki sannan ta iya dauke idanuwanta daga kan shi taci gaba da abinda ke gabanta har lokacin lamarin Anaam bai bar zuciyarta ba dan yayi mugun tsaye mata a rai, Allah ya iyo shi cikin gata da jin daɗi amma son zuciya ya hana shi ganin hakan, a har kullum kuma a koda yaushe idan ta samu kanta cikin kaɗaici ko kuma a kebabben wuri bata iya komai illa ta zauna ta yi ta tuna rayuwarta da halin da ta tsinci kanta har kawo yanzu, wani lokacin tayi kuka iya karfinta amma babu mai rarrashinta har ta gaji dan kanta ta bari, a duk sa'ilin da ta tsinci kanta cikin wannan yanayi tana jimawa bata dawo daidai ba haka kuma tana dadewa cikin bakin ciki da tarin damuwa, Allah sarki mommy mace mai kirki, hakuri, son jama'a da kuma kyautata musu,

Tsawon mintuna 30 ta kwashe acikin kitchen din kafin ta kammala haɗa abincin karyawar ta dauka ta fita zuwa falon mommy, tana zaune da cazbaha a hannunta tana ja kuma fitowarta kenan da alama sallar walaha ta idar, ajiye mata tayi kayan karyawar kan dinning table kamar yadda ta saba sannan ta durƙusa ta gaida ta, duk da tana cikin damuwa amma haka ta amsa mata fuska a sake,

"Anaam ya dawo gidan nan?"

"ehh ya dawo mommy"

"yana ina?"

"na hango shi ya shiga wurin motsa jiki..."

"je ki kira min shi"

"toh" daga haka ta tashi ta fita hankalinta a dan tashe dan bata kaunar ko hada ido dashi bare zuwa inda yake sai dai amma bata da yadda zata yi haka kuma bata da zabi tunda aiken mommy ne,

Kunnuwanshi toshe da airpod sabgar gabanshi kawai yake yi baima san tana yi ba dan ko shigowarta bai ji ba, zagawa tayi ta gabanshi sai lokacin ya lura da ita, kamar yadda ya saba bata fuska yanzun ma hakan yayi tare da zare abin kunnen shi guda daya ya kalleta,

"what?"

"mommy na kiranka..."

Bai kara ce mata komai ba ya mayar da abin shi cikin kunne yaci gaba da abinda yake, itama juyawa tayi ta fita ranta a jagule, wurin mommy ta koma ta sanar da ita yana zuwa sannan ta wuce cikin bedroom dinta domin gyara. Sai da ya kwashe mintuna goma sannan ya ƙaraso falon mommy, cikin bacin rai da damuwa mommy ke kallonsa,

"Anaam...... Bayan rashin mutuncin da ka shuka jiya duk bai isheka ba sai da ka hauro min katangar gida ka shigo cikin dare? Ban hanaka hauro mun katanga ba...."

"mommy to ya kike so nayi dan Allah? Kin hana masu gadi bude min gate to zan kwana a waje ne?"

"Dama ai a wajen ka saba kwana, akan wanne dalili zaka dawo min gida karfe 2 ko 3 na dare kuma ka tsammaci za a bude maka gate?"

"mommy nifa na gaji da zaman gidan nan.... Ana takurani da yawa dan Allah kawai a bani hakkina in bar gidan nan...."

"Anaam..... Idan ka sake fada min wannan maganar wallahi tallahi sai naci mutuncinka...... Idan har kana son wani abu daga gareni to kaje company kayi aiki kamar sauran mutane, muddin ba zaka yi aiki ba to babu dalilin da zai sa in rinka kwasar kudi ina baka kana zuwa kana kashewa abokai da karuwai....... Kudin a bola nake tsinto su ko kuma inji buga su gareni? "

" mommy nifa babu aikin da zanyi, ni kawai idan kika bani kudina da mahaifi na yabar min ya isheni inje in gina rayuwata..... "

" are you listen to your self?? Anaam really? Ni kake fadawa zaka gina rayuwarka? To bari kaji, babu abinda zan baka sannan idan ka kuskura ka sake ɗauko wata rigimar wallahi sai na ɓata maka sannan kar ka sake ɗaukar min Atm card ka cire min kuɗi, maza maza ka dawo min da Atm card dina yanzu yanzu...... "

Tashi yayi ya fita ba tare da ya kara cewa komai ba, duk abinda yake faruwa a cikin kunnen Imaan sai bayan da taji fitarsa sannan ta fito daga cikin dakin mommy, wucewa tayi ta bar mommy anan domin ta hau kan table zata yi breakfast sai dai zuciyarta cike take fal da tarin damuwa da kuma bacin rai. Shima nashi ran a bace yayi wanka, turare kadai ya fesa ya dauki key din motar shi ya kama hanyar fita bayan ya saka kananan kaya kamar yadda ya saba dan yafi ta'ammali dasu fiye da manyan kaya, part din mommy ya shiga wadda har lokacin tana kan dining tana cakular abincin dake gabanta dan ta kasa ci,

"Gashi..." ya fada cikin bacin rai ya ajiye mata Atm din a gabanta, binsa tayi da kallo har ya fice daga cikin falon, kanta ta dafe da hannu daya taci gaba da tagumi da kuma tunanin duniya wanda kullum cikinsa take.

Kai tsaye cikin fushi hotel din da ya saba zama shi da Najla ya tafi, har lokacin tana kwance tana shakar bacci bayan kayan mayen da ta dirka,

"baby...." ya fada bayan ya dafa ta a hankali, sanye take da rigar bacci pink color mai santsi,

"my.... Ka dawo?"
Chapter 2 · 0% Book details