← Book details Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***Duk da wannan tsautsayin da Anaam ya haɗu dashi na accident din da yayi hakan bai sa ya kama kansa ya nutsu ya zauna wuri ɗaya ba, da zarar ya faki mommy za a nemeshi a rasa musamman ma yanzu da Najla ta shigo gari tun bayan da taji labarin accident din da yayi bayan ya kaita gida a kan hanyar sa ta dawowa, sau da dama Imaan na zama ta tambayi kanta anya kuwa yana son ya gama da duniya lafiya? Anya kuwa yana son yaran da zai haifa suyi masa biyayya? Kai gaskiya duk macen da zata auri Anaam abar a tausaya mata ne kuma a jajanta mata dan bashi da maraba da ɗan Allah bani sai dai Allah sarki mommy a hakan take cigaba da kulawa dashi sam bata nuna gajiyawa duk da wani lokacin yana fusata ta, gashi wani abun haushi har yanzu bai daina kalato fada ba duk da wannan ciwon da ke hannunshi ga ɗan banzan yawo da zarar ya ga mommyn bata nan zai shiga gari, gaba daya dai kowa na gidan haƙuri yake yi dashi, Najla kuwa har gobe bai daina kashe mata kudi ba saboda ba wai ya san zafin neman su bane shiyasa babu abinda ya iya sai kashe su, yau dai ran mommy idan yayi dubu to sai dai ya baci saboda tun sassafe ya fita daga gidan bayan ya san yau ne ranar da zasu koma asibiti zai ga Dr kamar yadda suka saba gashi ya kashe wayar shi har zuwa dare bai dawo gidan ba kamar yadda ya saba, mommy ta cika fam tana jiran dawowarsa amma ba shi ya dawo gidan ba sai ƙarfe 1 na dare,

"Anaam zo...." mommy tace dashi bayan ya gama parking ya fito daga cikin motarshi, cikin mamaki ya kalli wurin da mommy din ke tsaye sanye da babban hijabi hannunta rike da carbi,

"mommy ba kiyi bacci ba...." bata amsa masa ba ta juya cikin part dinta yana biye da ita,

"Anaam menene matsalar ka ne a rayuwa? Me ke damunka? Me yasa a koda yaushe burinka ka bijirewa umarni na? Me yasa har yanzu ka kasa yin hankali?? Am quite sure kasan yau da safe kana da appointment da Dr dinka amma ka fice ka tafi gantalinka baka dawo gidan nan ba sai yanzu....... "

" mommy wani uzuri ne fa ya fitar dani "

" uzurin banza da wofi ba, kai koda yaushe kwakwalwarka bata fada maka gaskiya sai dai karya..... Baka da wani buri ɗaya mai kyau a rayuwarka, kawai rayuwa kake yi sakaka babu plan babu komai..... A wannan age din naka da ace kana da hankali da cikakken tunani da yanzu ka mallaki iyali sannan nima ka hutar dani a abubuwa da dama cikin rayuwa amma look at you..... "

Shuru yayi yana sauraren fadan mommy wanda kana ji kasan cikin tsananin bacin rai take yinsa sannan duk da ta saba yi masa faɗa amma wannan faɗan na dabanne dan kamar zata rufe shi da duka, ba dan yawuce munzalin duka ba da shi kansa ya san dukan da yau zai sha ba dan kadan bane, sai da ta gama faɗan sannan ta tashi cikin fushi ta wuce cikin bedroom dinta, duk abinda ke faruwa cikin kunnen Imaan wadda bata yi bacci ba kamar yadda mommy bata yi ba ita dai ta san damuwar mommy damuwarta ce domin a yanzu ita ce gatanta bayan ubangijin da ya halicce ta, tana jin sa shima ya gama zamansa cikin falon ya tashi ya fita zuwa part dinsa bayan wayar shi ta fara ƙara da alama Najla ce ke kiransa cikin wannan tsohon daren ko me zata fada masa ko kuma zasu fadawa juna oho ai dole ma su zama shashashu basu da lokacin komai a rayuwa sai nasu da na soyayyarsu sannan soyayyarma marar tsafta da alkhairi dan wannan soyayyar tasu kwata kwata babu alkhairi aciki tunda basa yin abinda ya kamata, da wannan tunane tunanen dai ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gabatar da sallar nafila raka'a hudu,.

Washe gari mommy ta kasa ta tsare ta sa shi ya shirya ta tisa shi a gaba zuwa asibiti kuma a ranar aka cire ɗorin da aka yi masa duk da yana ta faman wasa da hannun baya kiyaye duk wasu ka'idoji da dokoki da likita ya shimfida masa abinda yake so kawai yake yi a hakan ma dan mommy na tsaye a kansa, tunda ya samu hannu ya warke kuma shikenan yaci gaba da rashin jinsa son ransa rigimar yau daban ta gobe daban haka ta jibi daban ga rashin kwana a gida dan wani lokacin idan suka tafi yawonsu shida Najla sai su fi 4 days bai waiwayi gida ba kuma yana garin, duk damuwa da bacin rai sun yiwa mommy yawa saboda a kullum bata da burin da ya wuce na ta ga Anaam dinta ya zama cikakken mutum mai daraja wanda kowa zai ganshi yayi san barka ba wai ayi ta Allah wadai dashi ba sai dai har yanzu haƙarta ta kasa cimma ruwa kullum abun ta'azzara yake yana sake tabarbarewa maimakon asamu sauki sannan bugu da ƙari wannan yarinyar Najla sam bata yi mata ba shiyasa ba zata taɓa bari ya aure ta ba kamar yadda yake so dan kullum maganar sa aurensa da Najla shi so yake tayi masa aure a aura masa Najla, da yake Imaan ta san damuwar mommy ita dai hakuri kawai take bata tana sake kwantar mata da hankali dan ko yau ɗinnan sai da likitanta yazo ya dubata kuma yayi korafin bata rage tunani kamar yadda ya jima yana fada mata haka kuma tasa abu cikin ranta wanda ba a son hakan domin ajiye abu acikin rai yana haifarwa da zuciya matsala mai girman gaske, bayan tafiyar da Imaan ta kalli mommy cikin tausayawa da kuma damuwa tace,

"mommy dan Allah ki daure kiyi hakuri ki rage wadannan tunane tunanen da damuwar ko dan lafiyarki..... Na san akwai bacin rai amma kiyi hakuri...."

"Imaan nayiwa Anaam komai dan ganin ya zama na gari, na bashi dukkan gata da kulawa dan ya zama na gari amma abin ya faskara...... Har yanzu baiyi hankali ya zama irin mutumin da nake so ya zama ba a maimakon haka ma sai girma yake sake yi yana sake shiga jeji..... "

" mommy ki dai kara hakuri kici gaba da yi masa addu'a... "

Yammacin ranar da ya dawo mommy ta sake yi masa gargadin lallai lallai ya rabu da Najla amma yace shi babu mai raba shi da ita dan yana sonta, kayansa ya je yadauka set hudu ya zuba cikin karamar bag ya jefa a motar shi ya fita daga gidanma gaba daya, duk jikin Imaan a sanyaye yake saboda ganin abinda yayi wa mommy wato duk kokarinta a kansa baya gani sannan duk yadda take saka shi a hanya baya ganewa, mommy din bata cewa komai tun bayan da hakan ta faru face carbinta da taci gaba da ja kamar yadda ta saba sannan lokaci zuwa lokaci tana dauko diary dinta tana dan rubuce rubuce a ciki, daren ranar babu abinda ta iya ci sai ruwan tea kadai da ta dan sha shima bai fi rabin cup ba Imaan tayi mata sai da safe bayan ta tabbatar mata da babu abin da take bukata wanda zata sake yi mata. Washe gari har karfe 9 Imaan taji shuru mommyn bata fito ba gashi har tayi dukkan ayyukanta ta kammala ciki har da hadawa mommy din breakfast kamar yadda ta saba, ganin 10 saura ya sata shiga bedroom din mommy din nan ta kanta kwance kan rug din da take salla kamar me yin bacci a hankali ta matsa kusa da ita tana tashin ta a ranta tana cewa yau mommy tayi dogon bacci dan bata taba kaiwa irin wannan lokacin tana bacci ba amma ta yuyu ko sallar walaha tayi bayan ta idar ta dan sake kwanciya,nan ta fara tashinta,

"mommy....." shurun da taji ne yasa ta sake kiran sunan ta amma shuru ganin tayi kiran da dukkan iya karfin muryarta amma shuru babu amsa ya sata fita a guje tsakar gidan nan tayi kicibus da baba kande wadda ɗaya ce daga cikin matan dake dafa abinci a gidan, tare suka tafi bedroom din mommy a birkice amma itama koda suka je sai ta kasa gane komai gaba daya ta rude domin gata nan kamar mai yin bacci, fita suka sake yi suka kira wasu daga cikin ma'aikatan gidan daga karshe dai aka kira likitanta amma koda yazo bayan ya gama yan gwaje gwajensa sai Imaan ta ganshi ya fito yana share hawaye sannan cikin kidima ya soma kiran Layin wayar Anaam,

Yana kwance kan cinyar Najla tana wasa da sumar kansa kiran ya shigo, tsaki ya dan ja kafin yace "shi kuma wannan me zanyi masa da wannan safiyar yake kirana?"

"wane ne?" ta bukata tana jan sumar kansa,

"Dr din mommy ne..." daidai lokacin ya daga kiran, firgigit ya tashi zaune tare da sakin wayar ta fadi kafin ya kwalla ƙara tare da fashewa da kuka ya zabura ya nufi hanyar fita, da sauri ta bishi ta rike shi tana tambayar me ya faru, hawaye na bin kumatunsa yace mata,
Chapter 11 · 0% Book details