← Book details Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gaba ta bude ta shiga ta zauna a takure ya figi motar suka fita daga cikin gidan sai faman tsaki yake yi shi kadai. Tashin farko wurin da suke buga snooker ya fara zuwa yayi parking tana zaune aciki tana kallon sa ya fita ya barta aciki yaje ya zauna tare da karbar sigari a hannun wani ya fara busawa zuwa can ya tashi ya karbi sandar snooker din ya fara yi a takaice dai sai da ya shafe sama da awa ɗaya awurin sannan ya dawo cikin motar lokacin har ta gama ƙosawa da zaman da take yi tana ta faman jan tsaki a zuci da fili, kasuwa suka je ta shiga ta sissiyo duk abubuwan da suke da bukata, lokacin da ta dawo samunshi tayi yana waya da Najla wato LOML kamar yadda yayi saving no dinta, tana jinsa suna cigaba da hirar su shida masoyiyar tasa bayan sun canza harshe daga hausa zuwa turanci kuma ta yuyu yayi hakanne saboda ita watakila baya son taji abinda suke tattaunawa, maimakon gida sai taga ya sake kaisu wani wuri wanda bata san ko inane ba nan ya sake fita ya barta cikin motar sai faman kalle kalle take tana kallon masu shiga da fita amma jikinta ya bata duk yadda akayi wurin hotel ne sai dai ita babu wanda yake ganinta kasancewar gilasan jikin motar duka bakake ne daga wajen, tayi zaman a kalla rabin awa kafin ta hango shi suna fitowa shi da wata wadda kamar ta taba ganin fuskar ta, kafin su karaso ta ganeta dan kamar itace wadda ranar ta samesu a part dinsa tana zaune kan cinyarsa, yanzun ma gashi nan sai sake narkewa take yi a jikin sa kamar zata koma cikin cikinsa, sunkuyar da kanta tayi sakamako jin ya bude kofar motar zai shigo, ji tayi mararta tayi wata irin murdawa sannan ta kulle nan take, bata fahimtar me suke cewa saboda da turanci suke yin magana kuma anan dinma sai da suka ɓata lokaci kafin suka iya hakura suka rabu yaja motar suka nufi gida, suna zuwa bakin gate ya tsaya yace,

"fita...." bata yi magana ba ta soma tattara kayan ta bude kofa ta fita ta rufe masa kofa, ganin sa tayi ya fito da sauri ya sha gabanta har yana kokarin yin tuntube,

"shiga mota.... Shiga mota nace miki kin tsaya kina kallona, baki jin hausa ne.... Are you dumb?"

"ka barshi zan karasa..."

"ke dalla bana son bata lokaci nace ki shiga...."

Juyawa tayi ta bude murfin kofar amma kuma me gani tayi kan kujerar da ta tashi ya baci da jini wanda sam bata san da zuwan sa ba ita dai kawai taji mararta ta murda ta juya shikenan ashe bakonta ne yazo, wata matsananciyar kunya taji ta rufeta dan ta san shima abinda ya gani kenan shiyasa ya matsa da sai ta shiga ya shigar da ita ciki saboda kada sauran mutanen gidan su gani, zama tayi cike da kunya ta rufe kofar motar ya yi horn ya tura hancin motar ciki yana jan tsaki saboda harga Allah baiyi niyyar shiga gidan ba, wani wurin zai je amma wannan ta rusa masa lissafi. Parking yayi tana kokarin fita taji yace,

"ke shekarunki nawa?"

Kallonsa tayi amma taga ba ita yake kallo ba kawai gabansa yake kallo,

"27...."

"Amma shine dan tsabar dakikanta baki san lokacin da period dinki zai zo ba...... Zaki zo ki bata min sit din mota...... Ki shiga ki fito ki zo ki wanke min sit...." ba tace komai ba ta fita bayan ta kwashi kayan nan ya bita da kallon tsana da jin haushi aransa yana sake jaddada shirme da gidadanci irin nata banda haka ya za ayi kina abu shekara da shekaru amma ki kasa sanin time din da zai zo miki bayan yanzu gashi nan an waye harda su app ake amfani, fita yayi daga cikin motar ya nufi part dinsa yana jan tsaki........ ✍️

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

_*Ummi Shatu*_👌🏻
[8/7, 9:12 AM] Baby Aysher: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t

©️Love story 2025

*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA...!*

*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

*7*

***Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki ko kuma wadda bata da laka a jikinta haka take takawa zuwa cikin gidan, jinta take yi ta muzanta ko kuma ta gaza wurin kulawa da abinda yake matsayin sirrinta ita kadai wanda duk duniya ba kowa ne zai sani ba face wasu kayyadaddun mutanen da ya zama dole sai sun sani. Sai da ta fara gyara jikinta tukunna tana yi tana mamaki yadda a kayi har wadannan kwanakin suka zagayo ba tare da ta farga ba koda yake ita kanta rayuwar yanzu haka take mutane suna cinye kwanakinsu ba tare da sun ankare ba, motar tashi taje ta gyara inda ta zauna kamar yadda ya bukata, dama yaya lafiyar kura bare kuma tayi hauka, sai da ta tabbatar da ta tsaftace masa inda ta bata sannan ta rufe kofar motar ta koma ciki wurin mommy tana shaida mata sun dawo, duk da mommyn taga jimawarsu sannan kuma taga sun daɗe amma sai bata yi magana ba saboda bata son jin duk wani abu wanda zai ɓata mata rai ko ya tayar mata da hankali,kallon Imaan din tayi kawai tace,

"idan kin huta ki dafa min jallop din shinkafa da wake..... Ki sanya ganye sosai..."

"to mommy...." ta fada a sanyaye dan taƙi jinin ganin mommy cikin irin wannan yanayin na rashin walwala duk da a mafi yawan lokutta hakan take kasancewa ko kuma take tsintar kanta. A cikin ƙasa da sati biyu mommy ta shirya tafiya medical check up kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci tana ziyartar ƙasar chairo domin a duba lafiyar ta amma wannan Karon tana so ta je har Saudiyya domin gudanar da umarah,

Sai da mommy ta zaunar da Anaam tayi masa faɗa sosai wato kar taji kuma kar ta gani, ko a labari bata son jin ya aikata ba daidai ba ko wani abu mai kama da haka a dan wannan tafiyar da zata yi, kamar gaske kuma kamar yaji faɗan ya karkata kai yana saurarenta tare da bata tabbacin insha Allah babu wani abu da zata ji daga gareshi wanda ba alkhairi ko na farin ciki ba,

"Allah yasa haka.... Allah yayi maka albarka...."

Sallama tayi da kowa na gidan bayan tayi musu rabon kuɗi ya shiga mota suka tafi rakata shi da malam bala driver wanda shine ke jan motar. Imaan tana daki a kwance bayan tafiyar mommy tana ji a ranta babu daɗi saboda duk lokacin da mommy tayi tafiya ta kan tsinci kanta cikin kadaici da kuma kewa to yanzun ma hakan ce ta faru da ita, a haka dai take ta ɗan Al'amuranta kamar yadda ta saba ko wai zata samu ta rage tunane tunanen da ta saba yi a duk sa'ilin da ta keɓe, tana tsaka da yin sallar la'asar ta soma jiyo amon muryar sa yana faman kwaɗa mata kira kamar wadda ta aikata masa wani laifin,

"ke ƴar aiki....... Ƴar aiki..... Ƴar aiki...."

A gaggauce ta idar da sallar ta bude kofa ta fita zuwa babban falo inda take jiyo kiran nasa,

"uwani.... Uwani..."

Daidai lokacin ta isa gareshi ta tsaya a ɗan tsorace dan bata san dalilin kiran ba,

"ke baki ji ina kiranki bane?"

"naji ina sallah ne...."

"menene ma sunanki? Uwani ko umma?"

Sunana Imaan.... "

" kina jina, ina da baƙi wadanda zasu zo anjima, ki dafa mana abincin mutun kamar 10 haka sannan bana son ƙazanta..... "

" toh " ta fada kanta a ƙasa sannan cikin ƙosawa dan haka kawai bata son ko doguwar magana dashi kai ba magana ba kaɗai ko zama inda yake bata so, tashi yayi daga zaunen da yake ya fita ita kuma ta wuce kitchen a ranta tana tunanin to kuma wacce masifar ce take tunkaro su haka? Taji yace zai yi baƙi sannan ayi girki har na mutum 10 bata da amsar tambayar haka kuma duk hasashenta ta gagara hasaso komai shiyasa kawai ta mayar da hankali wurin girkin da ya sakata duk da bata so, fried rice ta dafa sannan ta hada salad wanda ba ita ta gama aikin ba sai bayan sallar magriba, ta gama kenan tana salla ta sake jin shigowarsa, kamar ɗazu yanzun ma a gurguje tayi sallama ta fita nan ta ganshi tsaye da sigari a hannunshi yana zuka, sam bata son warin sigari sannan ta tsani warin dan wani lokacin harda ciwon kai yake sakata shiyasa ta tsaya daga can nesa dashi,

"kin gama abincin nan?"

"ehh..."

"good, ki dauko shi ki kawo part dina and don't waste my time...."
Chapter 8 · 0% Book details