← Book details Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"love ban san me mommy take nufi dani ba.... Mommy ta hanani duk wani abu wanda yake nawa wanda kuma ya kamata a ce na mallaka irin na mahaifina da ya rasu ya bari........ Na kasa gane komai"

Tashi tayi zaune tana kallonsa fuskarta dauke da mamaki,

"my.... Me kake cewa ne? Mommy ta hanaka komai? Dama har yanzu babu abinda ta baka na daga dukiyarka? Hmmm Anaam you are not a small boy, you are an adult now, ta yaya za ka bari hakan taci gaba da faruwa? You have to fight for your right okay?"

Hannunta ya rike cikin naci," baby na rasa ta inda zan bullowa mommy ta aminta dani har ta yarda ta bani duka abubuwan da suke mallakina, na rasa wanne irin hankali take so inyi bayan wannan wanda nayi a yanzu.... "

" ya dai kamata ka tashi a tsaye Anaam..... Lokaci yana kure mana...... Ya kamata mu bar Kasar nan mu tafi can Kasashen ketare mu gudanar da rayuwar mu.... "

" Baby ina iya bakin kokari na kuma believe me komai ya kusa zuwa karshe..... "

Tun daga wannan rana da ya fita basu sake saka shi a idanuwansu ba, washe garin ranar Imaan tana kokarin shirya breakfast take tambayar mommy,

" mommy Anaam yana nan ne in hada breakfast dashi?"

Kallonta mommy tayi bayan ta gyara zaman gilashin dake fuskarta sannan ta rufe littafin dake hannunta wanda Imaan din bata san ko na menene ba,

"Imaan ta yaya zan sani? Rabona dashi tun jiya da safe lokacin da zai fita? Sanin kanki ne Anaam yana iya kaiwa 1 week bai dawo gidan nan ba, idan kin ganshi ya dawo ko yazo to matsala ce.... Na rasa yaya zanyi da yaron nan in huta.... Ni dai banyi sa'ar haihuwa ba.... "

"kiyi hakuri mommy, dan Allah ki daina fadin irin haka, insha Allah kinyi sa'ar haihuwa kuma za kiyi farin ciki da alfahari da hakan anan gaba.... Komai yana iya canjawa sannan Allah shi ne yake canja komai kamar yadda shine yake da kowa kuma yake iya canja bawa a duk lokacin da ya so hakan.... "

" Imaan sai yaushe Anaam zai yi hankali? Sai yaushe zai zama ɗa na gari kamar sauran yara nagartattu irin wanda iyayensu ke alfahari dasu? Sai yaushe zanji sanyi da dadin haihuwa acikin raina? Wasu yaran suna tausayi da kaunar iyayensu kamar ransu, suna bin umarni da kiyaye duk wasu sharruda na iyayensu amma ni banda nawa ɗan.... Me nayi da na cancanci wannan jarrabawar? Imaan ina ji a jikina da raina kamar na gaza a matsayi na ta uwa.... Na kasa bawa yarona ƙwaya daya tal tarbiyar da ta dace har ya zama na gari... Tabbas na gaza a matsayi na ta uwa kuma kamar ban cancanci na zama uwa ba domin na kasa tarbiyantar da abinda na haifa.... "

" Sam mommy baki gaza ba..... Wallahi baki gaza ba kuma baki kasa ba.....,Allah ya kan jarrabi bawansa ta duk hanyar da ya so da kuma abinda ya so, ba gazawarki ce tasa Anaam ya zama haka ba kawai ƙaddara ce tazo da haka....."

"Imaan i feel like I failed as a mother..... Mate din Anaam suna can suna gina rayuwarsu wasu harda iyali amma shi yana nan yana bani ciwon kai bashi da aiki sai dauko rigima da abubuwa marassa dadi ahakan kice ban gaza ba a matsayi na ta uwa?"

"mommy baki gaza ba, wallahi tallahi ke uwa ce ta gari wacce kowanne ɗa zai yi alfaharin samun ki matsayin mahaifiyarsa.... Kiyi hakuri da yanayin da kika samu kanki na jarrabawa....."

"shikenan Imaan..... Zaki iya tafiya kiyi aikin ki"

Sai da ta bari Imaan din ta fita kafin ta cire gilashin dake fuskarta ta soma share hawayen ta kamar yadda ta saba............ ✍️

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[8/3, 12:04 PM] Baby Aysher: ©️Love story 2025

*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA.....!*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

*3*

***Bata son ta rinƙa yi masa kuka matsayinta na mahaifiyarsa domin bata fatan Allah ya kuntata masa da wannan kukan da take yi saboda shi sai dai bata da yadda zata yi wanda ya wuce tayi kukan, ta jima zaune tana sharar hawaye daga karshe ta lallaba ta koma cikin bedroom dinta batare da ta gama yin breakfast ba, tsantsar damuwa da kuma yawan tunani ya sanya taji gefen kanta na yi mata matsanancin ciwo kamar yadda ya saba a duk lokacin da BP dinta ya hau, jiri take ji sosai haka kuma bata gani yadda ya kamata wannan dalilin yasa ta kira Dr wadda dama shine likitan dake dubata ko kuma duba wani daga cikin ahalin gidan idan bukatar hakan ta taso,

Cikin sanyin murya tayi magana lokacin da taji Dr Najib ya ɗauki wayar, "Dr please idan babu abinda kake yi ka zo ina son ganinka...." daga haka ta katse wayar ta sake gyara kwanciyar ta kan gadonta inda take kwance. Bayan kimanin mintunan da basu haura 30 ba Dr Najib ya ƙaraso matashin likita wanda ko a haife bazai fi Anaam dinta ba amma gashi nan shi ya zabawa kansa rayuwa mai kyau da kuma hanya mai bullewa sabanin shi nata ɗan da yana can yana ɓarewa duniya gyaɗa tana ci, yan gwaje gwaje Dr yayi mata kamar yadda ya saba kafin cikin damuwa ya dauki first aid box dinsa ya bude yana magana cikin nutsuwa,

"Hajiya baki rage damuwa ba, last time da na zo na dubaki bp dinki yayi high sosai and yanzu har yafi zama high fiye da wancan lokacin.... Dan Allah ki rage damuwa, komai yayi zafi maganinsa Allah..."

"insha Allah Dr" ta fada ba wai dan ta san hakan zata yuyu ba sai dan kawai ta katse maganar daga iya haka, magunguna ya bata kamar yadda ya saba ya dauki kayan aikinsa ya yi mata sallama ya tafi, zubawa magungunan ido tayi tana kallon su wanda a zahiri basu din take kallo ba tunani take yi a can karkashin zuciyarta, duka abubuwan da suka tattauna Imaan naji saboda tana dining tana shirya mata lunch, a hankali cikin sanyin jiki ta taso ta zo gabanta ta tsugunna tace,

"mommy ga abincin na kammala na shirya miki table kici sai ki sha magungunanki....."

Kallonta mommy tayi kafin tayi magana cikin damuwa "Imaan bana jin zan sha wannan maganin.... Wallahi na gaji da shan magunguna babu dare babu rana"

"to ai babu yadda za ayi ne mommy, a hakan zaki daure kibi dokar likita tunda yace shan maganin yana da mutukar muhimmanci...."

"nagode Imaan Allah yayi miki albarka..."

"Amin mommy, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana...."

Murmushi mommyn tayi tare da fadin "amin" ta mike zuwa table, sau tari Imaan ke sakata farin ciki da debe mata kewa tare da mantar da ita damuwarta.

*

"My.... Na zaci a wannan birthday din nawa zaka siya min mota amma sai naji shuru.... Wallahi duka friends dina suna da mota ni kadaice banida ita....."

"Baby kar kiyi fushi.... Ai baki fada min tun farko kina son mota ba....."

"wallahi yanzu mota kadai nake so.... Dan Allah my ka siya min ko ka bani acikin naka...."

Ɗan shuru yayi yana nazari dan yanzu idan yace zai siya mata sabuwar mota to zasu kwasota da mommy dan ba zata bashi kudi ba haka kuma ya san ba lallai ya sake ganin Atm card dinta ba bare yaje ya cire mata kudi kamar yadda ya saba, sannan mobile app dinta da yake shammatarta ya dauki wayarta har ya bude yayi transfer zuwa account dinshi yanzu ta canja pin da komai da komai gashi baby tace tana bukatar mota kai ai kuwa dole ya bata mota tunda dai har ta rokeshi, sabuwar motar da mommy ta siya wadda bai fi 3 weeks da kawota ba yaji a ransa ita ya dace ya dauko ya bawa Najla ko dan ya faranta mata,

"babe.... Bani 20 minutes zanje na dawo"

Daga haka ya tashi ya fita sai gida, yana shiga ya nufi part din mommy ko kallon part dinsa bai yi ba, tana zaune saman kujera Imaan na ƙasa tana matsa mata ƙafafunta, ya tsani yarinyar nan Imaan dan gani yake kamar harda ita take zuga mommy take yi masa wani abun,

Zama yayi kusa da mommy din yana kokarin gaisheta, kallon sa tayi cikin tuhuma tace,

"me ka zo dauka?"

"mommy sai kace wani ɓarawo?"

"to ai kai duk lokacin da ka shigo baka fita haka sai ka daukar min kudi ko Atm card ko waya ka cire min kudi....Yanzu kai Anaam a ganinka wannan rayuwar da ka ke yi zata haifar maka ɗa mai ido?"

Hararar Imaan yayi wacce ke zaune har lokacin tana matsawa mommy ƙafafuwanta, jikin ta ne kawai taji ya bata Anaam na harara ta saboda ya tsani mommy ta rinƙa yi masa faɗa a gabanta, tashi tayi sim sim ta fita,

" mommy kiyi hakuri, wallahi ni babu fa wani abu da nake yi...."

"au babu wani abu da kake yi? Yaushe rabonka da gidan nan? Baka da aiki sai zama a hotel.... Sai kudinka sun kare ka zo ka fakeni ka diba to yanzu idan kudi ne ya kawoka ka koma inda ka fito bani dashi...."
Chapter 3 · 0% Book details