← Book details Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" I lost my beloved mother....." daga haka ya fita duk gwiwowinsa a sanyaye sannan har ga Allah bazai iya cewa ga yanayin da yake ciki ba, wannan shine tashin hankalin da bai taba sanin akwai shi ba sai yau, bai taba shiga cikin hali na firgici ko kuma tashin hankali irin wannan ba tunda ya zo duniya, bai san ya akayi ya kai kansa gida ba kawai dai yaga gidan cike makil da ɗan adam wanda baya iya gane kowa sannan baya fahimtar komai, hawaye kawai yake iya fitarwa yana jin wani irin zafi da daci acikin zuciyarsa, yaje kan gawar tata bayan an shirya ta amma har lokacin baya iya gane komai daga karshe dai bazai iya cewa ga abinda ya faru ba domin fita aka yi dashi a sansandare zuwa asibiti. Imaan itama acikin firgici take da tashin hankali shikenan gatanta itama ya tafi domin mommy ita ce gatanta a yanzu uwa daga Allah, tayi kuka tayi kuka har ta kai ta kawo yanzu bata iyawa, ba ita kadai ba dukkanin daukacin mutanen dake zaune karkashin mommy kama tun daga kan ma'aikatanta na gida da na office kowa yaji mutuwarta haka kuma cikin tashin hankali suke saboda mace ce mai hakuri mai alkhairi da yawan kyautatawa bayin Allah sannan babu mugunta ko girman kai cikin tsarinta, tana da kyawawan halaye da dabi'u masu kyau shiyasa ta samu yabo wurin kowa sannan iya yawan mutanen da suka halarci jana'izarta kadai ya isa fahimtar da kai tana da kyakkyawar mu'amala da kowa haka kuma ta samu kyakkyawan karshe dan ranar ta kama ranar Juma'a ne mutanen da take bawa abinci sun zo sun cika kofar gidan kowa yazo sai yaji labarin rasuwar ta dan haka unguwar gaba daya ta dinke da mutane,

Yanda Anaam ke can asibiti ba ci ba sha haka itama Imaan take gida babu ci babu sha saboda tashin hankali har akayi kwana biyu, kawai idan ta zauna sai ta fara kuka dan duk inda ta kalla mommy take gani da duk wani motsi nata, sam bata dauketa matsayin yar aiki ba matsayin ƴa ta dauketa, irin zaman da suka yi da mommy tun bayan zuwan ta gidan har kawo maganar su ta karshe su take tunawa, itace mutum na karshe da suka yi magana da ita a daren da zata rasu yanzu gashi babu ita sai suna magajin rayi, tayi kuka tayi kuka har hawayen ta suka kafe ya zamana bata da ƙarfi ko kadan bare tayi kukan sai dai ido kawai daga karshe ma'aikatan gidan mata suka sakata a gaba da ban baki saboda mommy uwa ce garesu baki daya ba wai iya ita kadai ce tayi rashinta ba kowa cikinsu yayi rashi kawai dai ita tafi su shakuwa da ita ne kasancewar itace keyi mata hidima......... ✍🏻

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[8/10, 8:40 PM] Baby Aysher: ©️Love story 2025

*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA.....!*

*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

*10*

***Gaba ɗaya Imaan bata cikin farin ciki bare a samu nutsuwa a tattare da ita, radadin mutuwar mommy yaƙi barin zuciyar ta haka kuma tunaninta yaki barin cikin kwakwalwarta, ko a mafarki bata taba kawowa mommy mutuwa yanzu ba, yau dai da yake Baba Mari ta sakata a gaba dan dole take tura abincin da aka ajiye mata ba wai dan tana jin dadinsa ba sai dan babu yadda ta iya haka kuma bata da yadda zata yi tana ci tana kukan zuci a haka har ta dan ci kwata daga cikin wanda aka kawo mata.

Tun bayan da aka kai Anaam asibiti bai san inda hankalinsa yake ba bare yasan a inda yake kwance, Najla ce ke tare dashi tana zaman jinyarsa har akayi kwana bakwai kuma sai lokacin ya iya gane abinda yake faruwa da kuma halin da yake ciki sannan take mutuwar mommy ta dawo masa wadda yake jinta kamar cikin mafarki, wani kuka ya fashe dashi tare da tashi zaune ya sauka daga kan gadon da yake domin shi kadai ne yanzu cikin dakin ita Najla ta fita zuwa pharmacy, yana tafe yana share hawaye sai gata ganinsa yasa ta cikin sauri nufarsa tare da riko hannunsa,

"Babe ina zaka je?"

Ba tare da ya kalleta ba yace "zan je gida....."

"A'a babe kayi hakuri, ai ba a riga anyi discharging dinka ba, kayi hakuri har zuwa time din da Dr zai sallameka please...."

Har lokacin tana rike da hannunsa, girgiza mata kai yayi kafin yace "Ba zan iya ba queen..... Bazan iya zama anan ba...." daga haka ya fara tafiya, duk yadda ta so ta hana shi bai hakura ba dole ta bishi suka tafi bayan ta tattaro komai nasu dake cikin dakin da aka basu, fata ya rinka yi acikin ransa Allah yasa suna zuwa gida ya ga mommy sai dai amma kaddara ta riga fata dan lokacin da suka je gidan tun daga bakin gate zaka gane akwai abinda ya faru, cikin gidan ya shiga hawaye na bin kumatunsa part dinsa ya shiga kawai ya rufe kofa ya zauna yana kuka kamar karamin yaro, kuka yake sosai kamar ransa zai fita, ganin shuru shuru bai fito ba yasa Najla tashi ta nufi part din nasa saboda ada tana can sashen mommy sai nuna ta ake yi ana cewa itace wadda Anaam zai aura ita dai Imaan tana zaune tana kallonta saboda dama ta santa ba wai yau ne ta fara ganin ta ba. Bugun duniya Najla tayi amma Anaam yaƙi bude kofar har tayi ta gaji ta koma part din mommy tana sanarwa da mutane amma duk wanda yaje haka yake dawowa saboda yaƙi ya bude kofar yana zaune yana ta gunjin kuka cikin budewar murya, sai zuwa yamma sannan aka samu ya bude kofar, saka shi a gaba Najla tayi yayi wanka yaci abinci sannan ya fita bakin gate wurin masu karbar gaisuwa dan har lokacin mutane basu daina tururuwar zuwa gaisuwar ta'aziyya ba. A haka a haka a kwana a tashi asarar mai rai har aka share zaman makoki nan kuma ma'aikata da sauran jama'ar gidan kowa ya fara tunanin inda zai nufa dan cigaba da gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum, itama Imaan tana cikin masu wannan tunanin saboda dama zaman mommy take yi to ita kuma mommy gashi yanzu babu dan haka zamanta a gidan bai da wani amfani, kusan kowa na gidan ya watse dan haka itama ta shirya jakarta dan tafiya gobe duk da bata san inda zata je ba kuma bata da wani wurin zuwa amma ya zama dole ta bar gidan saboda yanzu gida ya zama na Anaam komai ya zama mallakinsa ita kuma dama jininta da nashi bai zo daya ba kai baima hadu ba sam sam, washe gari ta tashi da niyyar tafiya saboda komai na gidan ya tsaya haka kuma kowa ya kama gabansa bai fi su uku suka rage ba daga mai gadi sai malam bala driver, wanka tayi ta shirya ta saka kayanta ta dauki jakarta ta fito, shigowar wata babbar mota jeep ya dakatar da ita daga fitar da take kokarin yi, Alhaji Nura bature taga ya fito daga cikin motar wanda yake shine makocin mommy kuma kowa ya san shi a unguwar saboda yana daga cikin manyan mutanen dake rayuwa cikin unguwar,kada kai tayi ta wuce abinta tayi gaba saboda tun bayan da akayi rasuwar nan kusan kullum sai anyi manyan baki yan gaisuwa, muryar mai gadi ta dakatar da ita daga kokarin fitar da take yi,

"Imaan..... Zo ana neman ki"

Dawowa tayi har lokacin tana rike da jakarta, durkusawa tayi ta gaida Alhaji Nura ya amsa fuskar sa cike da alhini da damuwa kafin taji yace, "kece Imaan ko?"

"ehh nice....."

"Anaam yana nan ne?"

"ehh kamar yana nan bai fita ba gaskiya"

"ok muje ciki ki kirawo min shi...."

Wucewa tayi yana biye da ita har cikin gidan, a babban falon baki ya zauna ita kuma ta wuce part din Anaam inda ta san yana can tare da Najla amma koda taje sai ta samu Najla din bata nan watakila ta tafi sai shi kadai yana kwance yana bacci amma yayi rama ta fitar hankali,

"Ana sallama da kai a falon baki..."

Daga haka ta juya ta fita shikuma ya tashi ya saka rigar shi jallabiya ya fita, iya Alhaji nura kadai ya samu sai Imaan dake zaune amma ganin ya shigo yasa ta mike zata fita nan Alhaji nura ya dakatar da ita ta hanyar ce mata,

" A'a dawo ki zauna mana ai wannan zaman kema ya shafe ki....." mamaki abin ya bata saboda ta yaya za ace itama zaman ya shafe ta alhali bata daga cikin ƴaƴa ko kuma ahalin gidan, amma sai ta koma kawai ta zauna din zuciyar ta cike da tarin tambayoyi kala kala tana ta faman tambayar kanta to me kuma ya faru da zama ya hado har da ita? Ko dai wani abunne kuma ya sake faruwa aka ce harda ita? Zuciyar ta cike da wasi wasi har Alhaji Nura ya gama gaisawa da Anaam sannan cikin jimami da kuma Alhini ya zaro wata envelope daga cikin aljihunsa yace,
Chapter 12 · 0% Book details