Sashe 10
Zama Da Madaukin Kanwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda mommy ta tsara tafiyar tata hakance ta kasance daga Kasar chairo ta wuce ƙasa mai tsarki bayan gabatar da umarah ta fara shirye shiryen dawowa gida shi Anaam ya saki jiki ya bararraje yana ta sheke ayarsa son ransa yana yin abinda ya so kuma ya gadama kwatsam sai yaji wai mommy har ta sauka malam bala driver ya tafi airport ɗaukota, tashin su kenan daga bacci shi da Najla dan haka cikin sauri ya koma part dinsa yace ta fara hada kayanta mommy ta dawo, itama a tsorace take da mommy din saboda ta san bata son mu'amalarsu haka kuma bata son tarayyarsu shiyasa babu shiri ta tattara nata ya nata suka tafi ya mayar da ita Kaduna,
Lokacin da mommy ta dawo jikinta ya bata akwai wani abu amma kuma kowa dake gidan babu wanda ya gaya mata, bayan ta nutsu take tambayar Imaan yaushe rabon Anaam da gidan nan amma amsar da ta bata ta dan kwantar mata da hankali dan ce mata tayi dazun ya fita babu jimawa, ajiyar zuciya mommy ta sauke kafin ta ce,
"yana nan da halin nasa na rigima da fadace fadace ko?"
"A'a mommy.... Tunda kika tafi babu abinda ya faru....."
"maganar kawo min mutanen banza gida fa?"
Shuru Imaan tayi dan sai bata san amsar da yadace ta bawa mommy din ba shin ta fada mata gaskiya duk da yana kiran ta da munafuka ko kuma ta yi shuru abinta ta huta?
"mommy tun bayan da na sanar dake wannan kwanan da suka yi har yau dai bai sake kawo kowa ba...." ta shiryawa mommy ƙarya bayan a zahiri kusan kullum sai abokanansa sun zo da yan matansu nan zasu yi ta buga karta suna shan sigari da shisha ko kuma suyi ta lido da snooker saboda akwai wurin yin snooker din nan cikin part dinsa cikin falonsa,
"Allah ya shiryi Anaam yasa shi hanya madaidaiciya..."
"amin mommy...."
Tausayin mommy Imaan ta rinka ji saboda ganin yadda tayi fes da ita tayi ƙalau a dan wannan tafiyar da tayi saboda ta samu hutu da saukin matsalolin Anaam, a ranar da mommy ta dawo bayan ya kai Najla Kaduna ya dawo yayi hatsari a hanyarsa ta dawowa daga Kaduna,
"shikenan kuma mommy ta dawo zai cigaba da tayar mata da hankali..." shine abinda Imaan tace bayan ta samu labarin abinda ya faru dan ita mommy tuni ta fita a kidime sun tafi asibiti ita da malam Bala driver dan yana dab da shigowa Abuja abin ya faru, hankali a tashe su mommy suka je asibitin suka sameshi, duk da motar tashi taji jiki amma shi din tazo masa da sauki dan iya karaya ce kadai a hannu amma baya ga haka babu ko kwarzane a jikin sa, anan asibitin suka kwana saboda sai cikin dare aka yi masa gyaran karayar zuwa safiya suka koma gida amma zai rinka zuwa yana ganin Dr time to time,
Ita dai Imaan tun bayan da taji abinda ya faru ta fara tausayin mommy Allah ya dawo da ita kuma zata cigaba da ganin damuwa da bacin rai kala kala daga gareshi, amma duk da haka abinka da uwa lokacin da suka dawo part dinta suka taho dashi har cikin bedroom dinta ta saka masa pillow ya kwanta kan gadonta, breakfast ta umarci Imaan da ta hada ta kawo musu.
Yana kwance kan gadon mommy kamar mai yin bacci ita kuma mommy ta shiga toilet tana yin wanka Imaan ta shiga cikin dakin, bude idonsa yayi ya kalleta wanda ita dai take ganin sa tamkar harara dan duk lokacin da zai kalleta sai taga kamar harararta yake yi,
"sannu ya jiki?"
"Da sauki" ya fada can ciki ciki kamar yadda ya saba idan yan wulakancin nashi suna kusa,
"Allah ya kara sauki...."
Wannan Karon bai amsa ba ya mayar da idanuwansa ya rufe, ajiye kayan tayi ta juya ta fita dan bata da zabi illa hakan, tana fita mommy ta fito ita da kanta ta bashi breakfast din yaci ya sake kwanciya yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi. Tana falon baƙi tana gyarawa mommy ta shigo kuma da alama fita zata yi dan gata nan tayi shirinta tsab cikin wani koren leshi mai kyau da tsada wanda ya karbi jikinta mutuka ta sha babban mayafi shima kalar kore,
"Imaan zanje company muna da baki amma Insha Allah ba jimawa zanyi ba, Anaam yana cikin bedroom dina yana bacci dan Allah ki rinka zuwa ko akwai abinda zai bukata...."
"to shikenan mommy a dawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya...."
Fita mommy tayi ita kuma taci gaba da aikinta har sai da ta kammala sannan ta leka bedroom din mommy dan ganin halin da yake ciki, har lokacin baccinsa yake ta yi ba tare da wata damuwa ba koda yake ai dole yayi bacci saboda jiya bai samu bacci ba, sai wurin azahar sannan ya tashi, yana son yayi wanka amma kuma bai san ta yadda wankan zai yuyu ba saboda hannun da ya saba amfani dashi shine mai karayar shi kuma wannan baya iya komai dashi saboda rashin sabo, zaune ya tashi yana kokarin cire rigar dake jikinsa saboda ya sha iska jin an tayar da generator amma ita dinma ya kasa cire botiran dake gaban rigar tashi duk da har bakin sa yasa, shigowar Imaan ya katse shi daga abinda yake yi inda take dauke da abinci dan dama jira take ya tashi ta kawo masa, ajiye masa tayi a gaban gadon bayan ta jawo dan karamin bedside table, gani tayi yana kokarin cire rigar jikin shi amma da alama ya kasa, matsawa tayi duk da ta san baida bukatar taimakonta kamar yadda itama a dolen zata taimaka masa, hannunshi ya dauke daga gaban rigar ya kawar da kan shi gefe fuskarshi babu yabo babu fallasa, sai yau ne tayi masa kallo na tsanaki har ta gano dalilin da yasa mata ke manne masa suke like masa wato baƙi ne wanda ba wai can ba amma kuma yana da kyau karshen yadda zata iya kwatantawa tun daga fuskarshi har zuwa surar jikin shi gaba daya sakamakon motsa jiki da yake yi hakan ya bawa jikinsa damar zama na cikakken namiji, kyawawan manyan idanuwa da gira, dogon hanci, lips jajaye masu kyau da taushi da kuma kyalli duka ya mallaka sai dai amma baida kyawun hali wanda a wurin duk wani mai hankali kuma hali shine jari fiye da komai, yanda ya kawar da kan shi gefe itama haka ta kawar da nata kan har ta kammala cire masa botiran rigar tashi dan akwai farar vest wato sigiletin maza a ciki ya saka, sai da ta matsa daga gabansa sannan ya fara yunkurin cire rigar nan ta fita ta barshi tana tabe bakinta wanda sai take ji a ranta kamar harda hakkinta cikin wannan hatsarin da yayi saboda ya takurata ya kuma shiga hakkinta da yawa bata ɗiga aya akan wannan tunanin da take yi ba ta jiyo muryarsa ya fito yana kwala mata kira,kafin tazo har ya koma cikin bedroom din mommy, binsa tayi ciki nan ta ganshi tsaye,
"zuba min abincin nan...." ya fada yana kokarin zama gefen gadon mommy,
white rice and stew ne Sai farfesun kayan ciki nan ta zuba masa ta mika masa,
"ba zan iya cin abinci da hagu ba zauna ki bani....."
Sororo tayi tana kallon sa yayin da shi kuma bai ko kalleta ba sai ma bata rai da ya fara yi, ita kuma tunani ta fara yi ta yaya godai godai dashi zata zauna ta saka shi a gaba tana bashi abinci a baki, a wanne dalili? "to ai lalura ce..... Dan lokacin da yake lafiya bai taba cewa ki bashi ba" wani bangare na zuciyar ta ya sanar da ita kuma ita da kanta ta san shi dinma a dole zai bukaci hakan daga gareta dan baida yadda zai yi ne amma Anaam din da ta sani ba don lalura irin wannan ba da bata da wannan kimar ko darajar da zai zauna ta bashi abinci,
Kamar dazu yanzu dinma kawar da kai taga yayi a haka take bashi abincin yake ci kamar dole, ko rabi bai yi ba mommy ta shigo, karba tayi ta zauna kusa dashi ta cigaba da bashi tana bashi labarin abubuwan da suka faru a company da irin cigaban da ta tarar an a sake samu a dan wadannan kwanakin da bata nan, ita dai Imaan fita tayi ta basu wuri taje taci gaba da abinda yake gabanta har sai da taji mommy ta kirata tace taje part din Anaam ta dauko masa kayan da zai saka yanzu idan yayi wanka, da to ta amsa ta fita zuwa part din nasa, kai tsaye closet dinshi ta nufa saboda dama ba wai wannan ne karo na farko da ta fara zuwa ba, jar t shirt ta dauko masa mai gajeren hannu da blue din jeans sai turaruka guda biyu, knocking tayi mommy ta karbi kayan ta ajiye masa a gefen gado itama ta fita ta koma falo tana amsa waya. Da dabara yayi wankan ya shirya amma ya kasa saka wandon shi yadda ya kamata da riga dan haka ya kira mommy itace ta gyara masa sannan ya bi bayanta zuwa falo, Imaan dake zaune can gefe ganin yazo ya zauna ita kuma sai ta tashi tayi waje saboda bata zama inuwa daya tare dashi........... ✍🏻
TWO WRITERS EMPIRE ✍🏻✍🏻
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
*_Ummi Shatu_*👌🏻
[8/9, 10:32 AM] Baby Aysher: ©️Love story 2025
*ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA...!*
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
*9*