← Book details Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Gidan su A.A dake unguwar tambari estate suka nufa. Babban Gidane ya hadu iya haduwa tun daga get zakasan nera tayi kuka. dan ko a layin yafi ko wani gida kyau da tsaruwa. A haraban gidan motocin sukayi parking, fito da salma akayi wanda kanta yake lullube cikin mayafi aka nufi cikin gidan da ita.

Wani hadadden falo naga an shiga wanda ban taba ganin irinsa a k'asar mu ta NIGERIA ba. se dai kasashen turawa. falo ne dayaji kujeru ash da baki ga chanise carpet da labulaye duk arsh da baki. ga k'atuwar plasma da home tiatre se aiki sukeyi kai gaskiya falon ya hudu.

Daga kan da zanyi na hango wata hamshak'iyar mata daga ganinta jin dad'i da hutu sun samu zama a jikinta. Kyakykawa ce doguwa fara tana da d'an k'iba amma ba sosaiba. baza ta wuce 55years ba amma idan ka ganta zakayi zaton batafi 45years ba saboda yanayin hutu da take ciki. Hajiya Halimat me dala kenan uwargida a wajen Alh. Abdul razak me dala kuma mahaifiya Awajen A.A.

Tana zaune tare da k'awayenta se murmushi take zubawa. Tasowa tayi cikin takunta na manyan mata ta k'araso ta rungume salma daka kalleta zakasan tana cikin farin ciki."well come to our family my daughter" ta fada tana murmushi, sannan ta jata suka zauna akan daya daga cikin kujerun da suke falon. Duk mutanen wajen ba wanda bata burgesu ba. wanda suka santa kam basuyi mamaki ba dan sun santa macece me son mutane bata da girman kai ko kadan.

Su aunty hadiza waje suka nema suma suka zauna, bayan 'yan gaishe-gaishe suka damk'a musu amanar salma, suka ce sun kar6a da fatan Allah ya tayasu ruk'o.

Agurguje
Salma na hango an fito da ita daga wani daki tasha lufaya milk colour fuskarta tasha make-up, tayi kyau sosai. Haraban gidan suka nupa wanda aka k'awata su da kujeru saboda gudanar da walimah. Batare da bata lokaci ba malama juwairiyya ta fara gudanar da lecture bayan ta bude taro da addu'a. Tayi bayani akan hakkokin miji akan matar sa da kuma yanda mace zata tafiyar da rayuwar aurenta da dai sauran su.

Bayan ta kammala ne aka rarraba bags wanda suke dauke da hoton ango da amarya a ciki akwai hankacif,memo,key holder,calender da juice kala-kala wanda suma suna dauke ne da pics din ango da amarya. se take away wanda akasa rabin kaza,donnut da meat pie. Ba'a tashi daga waliman ba se 5:00pm.

Wani daki na musamman aka kai salma,wata budurwa naga ta shigo dakin wanda batafi 21years ba,kyakykyawa doguwa bata da jiki sosai black beauty sadiya Abubakar kenan (my namecy😜) wanda aka daukota tun daga sokoto domin tazo ta shirya salma zuwa wajen dinner.

Toilet ta shiga ta hada ruwan wanka wanda yasha turaruka masu kamshi,ta fito ta umurci salma da ta shiga tayi wanka ta dauro alwala saboda lokacin sallar magriba ta k'arato.Bayan salma ta fito ta shafa mai se sady ta dauko make-up kit dinta ta fara tsantsara ma salma kwalliya. Wanda ya dauke su tsawan awa daya da rabi.

MASHA ALLAH abinda ya fito daga bakina kenan lokacin danayi arba da fuskar salma.

A gaskiya me karatu zanso kaga salma a lokacin.Indai ba farin sani kayi mata ba zeyi wuya ka shedata. nima dan na lab'e a lungun gado ne shiyasa har na ganeta.😜 Azuciyata kuwa nace anya A.A zai gane salma kuwa shida ko gama saninta ma beyi ba.

muje zuwa

🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:35PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 14

Yau ya rage saura sati 1 biki gida ya fara cika da 'yan uwa na kusa da na nesa.

sallama akayi aka ce wai ana sallama da salma. Aunty hadiza ce ta cema yaron kace tana zuwa, da yake yanzu kusan kullum se tazo saboda hidiman biki.

salma kije ana sallama dake a waje aunty hadiza tace, tashi salma tayi ta dauki hijabinta tayi hanyar waje,kiranta aunty hadiza tayi, kina nufin haka zaki fita wai? ko kwalliya bakiyi ba bare ki fesa turare? maza jeki shafa ko hoda ce ki goga jan baki ki fesa turare.

tura baki salma tayi sannan ta koma daki ta danyi make up ta fesa turare ta fito. Har lokacin aunty hadiza tana tsaye a wajen data barta, to ko kefa ta fada tana murmushi da zaki fita kamar ba amarya ba,zakije wajen miji fuska farau-farau ba kwalliya.

ko kulata salma batayi ba ta fita ta barta tana ci gaba da maganar ta.

A jingine a jikin mota ta hango su, wannan karon su 2 suka zo, shida wani saurayi kamar shi black beauty dagani zeyi saukin kai dan fuskar shi cike take da murmushi. ba kamar A A ba daya hada rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa.

Tun da ta fito yake kallonta yana kare mata kallo, ba lefi tayi mishi kyau se dai fa shi kowacce mace bata burge shi inba matarsa humaira ba.

Sallamarta ne ya dawo dashi daga tunanin daya fada. kauda kai yayi se abokin sane ya amsa sallamar. Gaisawa sukayi sannan yace hajiya salma nasan baki sanni ba, sunana SALEEM nine babban abokin Abdul.

Munzo ne domin muji irin shirye-shiryen da kuke yi. seki fada mana event nawa zakiyi da yawan kudin dazai isheki se mu baki. cikin sanyin muryanta ta ce ba abinda zanyi kuma bana bukatar komai.tokai kaji abokina, ta yaya za'ace amarya bata bukatar komai? ai bazai yuwuba.

ko kallon shi A A beyi ba balle ya nuna yaji abinda yake fada. dan tsaki saleem yaja sannan ya maida kallon shi gun salma yace to mu ta bangaren mu akwai dinner da muka shirya bayan ankai amarya karfe 8:30pm. Ina fatan ba matsala?

Gyada mishi kai kawai tayi duk da a ranta bata so hakan ba, bude mota saleem yayi ya fito da wani leda tare da emvelop ga wannan kayan shi zaki sa a wajen dinner. wannan kuma ki rike a wajenki saboda hidiman biki duk da kince bazakiyi komai ba 500k ne ba yawa.

dan rusunawa salma tayi ta karba sannan tayi masa godiya. Murmushi saleem yayi mata dan ba karamin burgeshi tayi ba, bakomai amaryar mu ya fada sannan ya dubi A A ko akwai wani abin da ban fada ba? kauda kansa yayi cike da jinkai yace idan ka gama surutun zamu iya tafiya. ya fada tare da shigewa mota

Murmushi saleem yayi danshi ya saba da halin Abdul,mutum ne wanda baya son hayaniya se kayi magana goma be amsa maka daya ba. shiyasa baya damuwa da duk abinda zeyi masa saboda yasan halinsa in and out. Tun suna yara suke tare kasan cewar iyayen su aminan juna ne. ko sunyi fada a lokacin suke shiryawa

To amaryar mu, mu zamu tafi se munzo daukan ki nan da sati. godiya salma tayi masa tare da juyawa ta shiga gida suma sukaja motar su suka tafi.

salma tana shiga ta mikawa aunty hadiza ledan da kuma emvelop din, bude ledan tayi taga kayane a ciki. wani hadadden material ne purple colour da ratsin fari anyi masa dinkin doguwar riga. se farin takalmi hill da farin poss, se head purple da kuma sarka da dan kunne fashion purple da fari.

wannan kayan fa? aunty hadiza ta tambaya, bayani salma tayi mata. aikuwa kudinnan se dai a bude miki account a saka miki. bari na kaima innarki ta ajiye zuwa a gama biki se akai banki.

WAI WAYE A A ne???
ku biyo ni a next page domin muji cikekken tarihin A A me dala

🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:35PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 15

Ina jin dadin yawan comment dinku da nake gani, nagode sosai ALLah ya bar kauna.

WANENE AA ME DALA??

ABDUL-AZEEZ ABDUL-RAZAK ME DALA shine cikekken sunanshi, mahaifinsa Alh. Abdul-razak me kudine na gaske yana da kamfanin saida motoci har guda uku bayan haka kuma dan kasuwa ne sosai. Abdul saurayine meji da kansa ga kyau ga nera uwa uba ilimin boko da arabic.

yayi karatunsa har zuwa matakin masters akan business. Abdul mutum ne miskilin gaske, danshi mutum ne da baya son hayaniya. Idan kaga yanda mata suke binshi abin zai baka mamaki,amma ko kallo basu isheshi ba.

Shikadai ne da namiji agun iyayensa,shine first born sai kannen shi mata guda uku Hafsat,Amina da ummul khairi. Sun samu tarbiyya a gurin iyayen su, kasancewar su masu arziki hakan besa sun sangarta su ba.

Abdul sun hadu da matar sa humaira ne a wani super market,sunje shopping shida abokinsa Saleem. tunda ta ganshi ta rikice akansa amma shi ko kallo bata ishe shi ba. hakanne yasa tabi duk hanyar da tasan zata jawo hankalin shi gareta kasan cewarta mace me budadden ido dan gidansu 'yan boko ne ita kadaice 'ya awajen iyayenta. ko kadan iyayenta ba ruwansu da irin rayuwar da take yi dan ko zata kwana a wajene ba wanda zai tambayeta dalili. wannan ne ya bata damar sheke ayanta yanda take so. dan gidan malamai ba wanda bata sani ba, idan dai taga kayi mata yanzu zata kai sunanka gun malaminta a mallake mata zuciyar ka. Hakanne ta kasance lokacin da taga A A.

tunda taga alamun dan jin kaine taje ta sanar da malaminta akayi mata aiki a kansa. Aikuwa aiki yayi kyau dan a hakane ta samu har ta aure shi. iyayensa basuso auren ba kasancewar ta me karancin tarbiyya, amma ba yanda suka iya tunda ya dage akan yana sonta a haka, se dai kawai suka ci gaba dayi masa addu'a.

Bayan anyi auren ne ta fara fiddo da asalin halayyarta, ko sau 1 bata taba daga waya ta kira iyayen mijinta ba domin ta gaishe su,ballantana ta taka da kafarta taje har gida.

koda kannensa sunzo bata bari su ganshi,se dai tace musu bayanan. daga karshe ma zuwa tayi ta samu me gadi akan ko sunzo kar ya yadda ya barsu su shigo gidan, duk randa ya barsu to abakin aikinsa.
Chapter 5 · 0% Book details