← Book details Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 1 OF 12

Sashe 1

Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAAPP 08066360176

🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 1 and 2

Ina mika g0diya ta wa ALLAh (swa) daya bani ik0n rubuta wannan littafin. Sannan wannan littafin kageggen labari ne ban yi d0n cin zarafin wata k0 wani ba dan haka idan yayi dai dai da rayuwar ka/ki ayi hakuri. Na sadaukar da wannan littafinne ma Aunty na Aysha biciki (AysM) ALLAh ya kara basira da daukaka... Masoya zaku iya fadan ra'ay0yin ku ta wannan numbern 090649847980 . Nagode.

A fusace ya shig0 gidan yana faman kwalla mata kira kamar gidan zai tarwatse saboda tsabar ihun da yake yi, ke saude! Ke saude! Cikin hanzari ta fito daga daki tana amsa kiran da yake mata. Gani mallam ta fada tana karasowa ya kalleta cikin daure fuska sannan yace se yanxu kikaga damar amsawa? Cike da ladabi tace kayi hakuri mallam wallahi sallah nakeyi shiyasa. Dan ta6e baki yayi sannan yace ina salma take? Ki gaya mata zatayi bako anjuma kuma saura yazo taki fita wallahi ranta seya baci dan nagaji da ganinta a gabana ba miji.

Inna saude ta kalleshi sannan tace haba mallam aure ai lokaci ne idan lokacinta yayi ko tana s0 ko bata so xatayi ai... Cikin jin haushi ya katse ta ke saude na dade da sanin ke kike zugata to bari na fada miki a wannan karon na tsaida magana. Na riga nayima salma miji ke baki isa na canja maganata ba kuma ki ja mata kunne k0 tana s0 k0 bata s0 se anyi aurennan. Inna saude tayi kasa da muryanta tace dan Allah mallam kayi hakuri ni ban isa na zuga salma akan ta bijire ma umurninka ba sbd ni da ita duk a karkashin ik0nka muke, kuma insha Allahu salma bazata watsa maka kasa a ido ba kayi hakuri. Jin abinda saude tace ne yasa mallam amadi sassautawa sannan yace ai kene saude da wata irin magana ya zango ina miki maganar nayi mata miji amma kina cewa aure lokaci ne, ai lokacin yayi kenan tunda har na zabo mata mijin daya dace da ita. Gidan da zata je ta huta k0mai se anyi mata ba tare da tasha wuya va. Inna saude ta matso tana cewa mallam irin wannan k0dawa se kace wanda zata auri govenor

Murmushi mallam Amadi yayi saboda jin ta s0sa masa inda yake masa kaikayi, ai saude mijin da salma zata aura kamar g0venor yake a wajen mu dubi ciki gidannan k0 dan tiles babu balle aje kan abin sanyinnan A.c ake ce masa k0 me ai kuma kinga duk wanda yake da irin wannan a gidansa se dai mu kirasa da govenor a gidannan. Cikin mamaki inna saude take kallonsa k0da yake ba abin mamaki bane awajenta tunda tasan halin mijin nata.

🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 2.I dedicate this page 2 my l0vely sis maimuna dauda guda (ummi) Allah ya bar qauna... Zaku iya fadan ra'ayoyin ku ta wannan numbern 09064984798 ngd

Tunda tasan halin mijinnata mutum ne mara godiyan Allah, wanda k0mai ya samu baya isarshi, a kullum shidai hangen na wani yake yi. Murmushi tayi sannan tace wai ni mallam waye kake ta zuzutawa ne haka? har yanzu banji ka fada min sunan shi ba. ALH. ABDUL ME DALA ya fada yana zama akan taburman dake shinfide a tsakar gidan... Cikin fírgici inna ta dafe kirji badai Alh. Abdul dana sani ba? Dan murmushi yayi sannan yace shidin dai nake nupi. INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI'UN. Abinda inna saude take ta maimaitawa kenan. Yanxu malam ka rasa gidan da zaka kai yarinyar nan se wannan gidan? Gidan da kowa yasan ba gidan zama bane, amma saboda s0n abin duniya kake so ka maida 'yarka bazawara. Kai inma zawarcinne ai da sauki indai baza'a kassarawa mutum rayuwa ba.

Inna ta fada tana goge zufan da ke zubowa daga fuskarta wanda yake sauko mata tun lokacin da taji an ambaci sunan ALH. Abdul me dala. Duk kawaici irin na inna saude wanda ko wani irin hukunci mallam amadi zai yanke a gidan zeyi matukar wuya kaji tayi magana koda kuwa hukuncin beyi mata dadi ba. Amma yau sanadin jin sunan ALH. Abdul da tayi ta tanka. Wanda shi kansa mallam amadi saida yayi mamakin hakan. Shiru yayi yayi mata dan besan me zaice mata ba. Shidai yasan ya riga ya gama yanke hukunci kuma ba wanda ya isa ya canja masa ra'ayi

[1:34PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 3.

Cikin sanyin jiki inna saude ta zauna kusa dashi.sannan tace mallam wannan maganar fa abin dubawa ne don Allah kabar salma ta zabi wanda take so, har nawa salmar take? da za'a ce an gaji da zamanta ba miji. Kwata kwata fa bata fi 18yrs ba. Dan Allah kabar maganar hadata da ALH. Abdul dinnan. A hargitse ya dago yana mata wani mugun kallo, sannan yace ke saude wallahi fita daga cikin maganar nan idan har kina son mu shirya dake, nan gidana ne salma kuma 'yata ce inada iko da ita da da duk abinda yake cikin gidannan.
Ina da ikon aura mata duk wanda nake so. Ke koda kuturu naso ta aura dole tayi min biyayya balle cikekken mutum me tarin dukiya.

Kuma bari kiji billahillazi ko mallam dattine ya dawo duniya kinga dai shiya haifeni ko? To be isa ya hana na daurawa salma aure ba. Sake baki inna tayi tana kallon shi ba tare da ta'iya cewa k0mai ba. Jin maganar na shi har iyayen shi yake sawa aciki.

Arziki na bin mu kinamana bakin ciki to ta Allah ba taki ba. Ya fada yana miqewa daga kan taburmar da suke zaune. Ya saka takalman sa ya fice daga gidan yana
banbamin masifa.

Bin bayansa da kallo tayi kana tace mallam ina guje maka ranar nadama dan nasan tananan zuwa wallahi se kayi nadamar abinda kake shirin aikatawa. Mikewa tayi ta fara aikace-aikacenta d0n yamma tayi gashi bata gama abincin dare ba.
[1:34PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 4.matashiyar budurwa ce kyakkyawa doguwace amma ba sosai ba, fara ce kar jikin ta dan daidai kirar coca cola. tana da faffadan fuska me dauke da manyan idanu tare da madaidaicin hanci da faffadan baki,.

tana da beauty point a gepen kumatunta hagu da dama. haqoranta farare wanda suke dauke da siririn wushirya a tsakanin su , tana sanye da dogon hijab har kasa ruwan kasa hannun ta yana dauke da al-qur'ani me girma.!!!

da sallama ta shigo gidan tana cewa inna na dawo, inna saude dake kitchen tana tuka tuwo ta amsa mata sallamarta tana cewa salma kin dawo? cikin nutsuwa ta amsa mata da eh nadawo, sannan tace inna bari nazo na taimaka miki kafin a kira sallah.

A'a salma yi zamanki ki huta,keda yanxu kika dawo. ai harna gama daman tuwo ne ya rage ban tuka ba. To inna salma ta amsa tana cire hijab din makarantar hadda da take zuwa dashi,.sannan ta shige daki ta ajiye Al-qur'anin dake hanunta,ta fito ta nemi waje ta zauna tace inna har yanzu baba be dawo bane? inna saude ta amsa da cewa ya dawo ya sake fita ne, amma yanzu zaki ganshi ya shigo tunda magariba tayi.

Inna bata gama rufe baki ba mallam Amadi yayi sallama ya shigo gidan. sannu da zuwa baba cewar salma, yawwa sannu 'yar albarka. Da mamaki take kallon mahaifin nata rabon da taji irin haka a bakinsa har ta manta.

Da Sauri ta tashi ta debo masa ruwa a buta,domin yayi alwalan sallar magriba. sannan itama ta dauki buta tayi ta shiga daki domin tayi sallah itama.
[1:35PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Page 5

Bayan mallam Amadi ya dawo daga sallah, ya nemi waje ya zauna inna saude ta kawo masa abincin shi. Bayan ya gama cine ya dubeta yace ina fatan kin fadama salma sakon da na baki???
inna tace ban fada mata ba mallam, amma yanzu zan fada mata insha ALLAhu

Da harara ya bita dashi,sannan yace kira min ita nina fada mata tunda ke baza ki iya ba.kayi hakuri mallam yanzu zan fada mata.

Tsawa ya daka mata yana cewa ki kiramin ita nace, da hanzari inna ta tashi ta shige daki tana me kwalama salma kira.

Amsawa salma tayi sannan tace inna wani abu xan yi miki? girgiza kai tayi tace mahaifinki ne yake kiranki.

Gaban salma ne ya fadi ta shiga maimaita INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRAJI,UNï¼a cikin zuciyarta dan tasan idan taji kira daga wajen mahaifinta, tofa ranar da bakin ciki zata kwana

Inna ta juya ta fice daga dakin tana cewa ki fito yanxu karki bata lokaci. Da hanzari ta biyo bayan mahaifiyar nata,can gepe ta tsuguna cikin girmamawj tace baba gani.Ya dubeta yace dama ba wani magana bane maganar auren kine nagajr da ganinki a haka ba miji,saboda haka na zaba miki miji kuma anjumj zezo saura naji kin masa wani abu. Wallahi jikinki zai gaya miki, yanzu ki tashi kije ki shirya kafin yazo.

a hankali salma ta mike tana hada hanya ta nufi daki,jin irin hukuncin da mahaifinta ya yanke ba tare daya tuntubeta yaji ra'ayinta kona mahaifiyarta ba. tana shiga daki ta fashe da kuka 😭
tana me cewa ya ALLAh ina rokonka kasa hakan ya zamomin alkhairi a rayuwataðŸ™ðŸ™ðŸ™

kuyi hakuri da wannan.
[1:35PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
*ZAB'IN MAHAIFINA*
🌳🌳🌳🌳🌳

Writen by *SADIYA ALHASSAN(ummu Affan)*

Dedicated to *PRINCESS ESHAT AYSM*
_AYSHA BICHIKI_

Masoya makaranta novel dina ina jin dadin yanda kuke nuna kaunar littafina. Nagode sosai ALLAh ya bar kauna.

Page 6

WANENE MALLAM AMADI???

Mallam Amadi dan asalin garin Bauchi ne, a karamar hukumar Ningi. kasuwanci ne ya kawo mahaifinsa cikin garin bauchi

Mahaifinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado, su 2 ne a wajen iyanyen su. shi da kanwar sa hadiza wanda take aure a cikia anguwar nassarawa jahun.
Chapter 1 · 0% Book details