← Book details Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 11 OF 12

Sashe 11

Zabin Mahaifiyata Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

tananan zaune har yarinyar tagama ta fito, mik'ewa tayi tace"dauko kayanki muje na nuna miki yanda zaki zauna.

B.Q takaita dakunane guda 2 kowanne da toilet a ciki se falo a tsakiya, se k'aton kitchen a gefe da alama shine manda ake girki a ciki. daki daya blessing ne a ciki, d'ayan d'akin wanda ba kowa salma tace ta shiga, ta juya ta koma part d'inta.

Toilet ta shiga ta d'auro alwala tayi sallar azahar. ta dawo falo ta zauna ta kunna tashar arewa24, ta samu suna hasko film din dawo-dawo.

Tana zaune taji an turo k'ofarta an shigo ba neman izini, d'aga kai tayi dan taga waye me k'arfin halin shigo mata d'aki haka.

Blessing ta gani 'yar aikin humaira, cikin b'acin rai salma ta daka mata tsawa "Keï¼.. baki da hankali ne? da zaki shigo min d'aki ba neman izini, haka aka koya miki a gidanku?" Jikinta yana b'ari ta durk'usa tana bawa salma hakuri.

Fuska ba fara'a salma tace "me kikazo yimin a d'aki?" cikin girmamawa ta amsa hajia babba ce ta aiko ni nazo na karb'a mata abinci a wajenki.

shek'ek'e salma take kallonta tace kije kice mata ban girka da ita ba. cikin sauri ta mik'e ta fita

Bugo kofar akayi aka shigo, humaira ce cikin masifa ta fara magana " ke salma ina abincina?" ban girka dake ba salma ta fad'a. kutman uba..🙊 ina cikin gidannan kiyi abinci kice baki girka dani ba? to wallahi baki isa ba, da wani tsugudidin ne yasa kikace zaki dingayi da kanki?

kallonta salma tayi tace "ai da nace zan dingayi da kaina bance hardake zan dinga girkawa ba, wa mijina nace zan girka. Alfarma d'aya zan iya miki, shine zan dinga yi dake safe da dare, da rana kuma seki nemi abinda zakici. Hakan ma albarkacin mijina kikaci, dan haka karki sake zuwa kice na baki abinci danni ba 'yar aikinki bane.

Dubanta humaira takeyi cike da mamakinta,yarinya k'arama ta tsaya tana fad'a mata magana , wanda inda tana da k'anne tayi k'anwa ta 2 da ita, lalle ta samu waje da yawa tace " wallahi salma ina tausaya miki, ni humaira nayi alk'awarin sena LALATA (littafin sad-naf) miki rayuwa, se kinyi nadamar shiga gonata da kikayi.

Tab'e baki salma tayi tace " ni nafi k'arfinki wallahi, idan kina takama dabin malamai ne to ni kuma na rike addu'aðŸ™ðŸ™ kuma da yardan Allah ba abinda kika isa kiyi min.

Mu zuba ni dake aga wanda zeyi nasara,humaira ta fad'a kafin ta juya ta fita daga falon. tsaki salma tayi, taci gaba da kallonta.

Driver ya kai abinci office d'in A.A masinja yayi masa izinin shiga bayan yaje ya fad'a masa yayi bak'o, tura k'ofar yayi ya shiga da sallama.

Duban shi A.A yakeyi cikin mamakin ganinshi, yace lafiya kuwa mallam haladu? lapia lau Alh. k'arami(dayake haka suke fad'a masa) gaishe shi yayi kafin yace "daman hajiya karama ce tace na kawo maka wannan👉 . duban basket din A.A yayi yana yamutsa fuska kafin yace wacece kuma hajia karama?

Amaryanka nake nufi ranka ya dad'e. kallon basket d'in ya sakeyi cikin mamaki yace "gidan kaje"? eh ranka ya dad'e hajia ce ta aikeni nakai mata 'YAR AIKI. Gyada kai yayi ya nuna masa kan centre table yace ya ajiye a wajen.

5000k ya mik'a masa, karb'a drivern yayi yana zuba godiya kafin ya fece daga office d'in. basket d'in ya d'auko ya ciro cooler da jug d'in. Ya bud'e ya zuba abincin tare da had'in coslow, sannan ya fara ci.

yana ci yana lumshe ido rabon daya ci abinci me dadin wannan harya manta, ko abincin restaurant dayake aikawa asiyo masa ba yanda ya iya ne kawai, gidan hajiyar sa ne idan yaje yake cin abinci kamar wannan. to shikuma yanzu ba zuwa yakeyi sosai ba. dan ko yaje baya dad'ewa bare har yaci girkinta me dad'i.

sosai yaci abincin yasha zob'on, a ransa yana jinjina ma yarinyar dan komai nata dabanne, gaskiya yanzu yana farin ciki da ZAB'IN MAHAIFINSA. kiran masinja yayi ya bashi saurae abincin, zob'on kuma ya saka a fridge, zuwa anjuma zai sha dan yayi masa dad'i sosai.

🌳🌳UMMU AFFAN🌳🌳
[1:36PM, 2/7/2018] ‪+234 808 677 7945‬: 🌳🌳🌳🌳🌳
ZAB'IN MAHAIFINA
🌳🌳🌳🌳🌳

Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)

ðŸŒHAJOW ðŸ“ðŸŒ

ðŸŒðŸ‘©â€ðŸ‘§â€ðŸ‘§ðŸ‘©â€ðŸ‘§â€ðŸ‘§ðŸ‘©â€ðŸ‘§â€ðŸ‘§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS âœðŸ¾âœðŸ¾âœðŸ¾ðŸŒ

Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI

Page 24

Da daddare salma ta tuka tuwon shinkafa miyar egusi wanda yaji ganda, da jallop din taliya da kifi, ta hada da sauran zob'onta na cikin fridge. bata kai abincin dining ba saboda bata yarda da humaira ba. Me aikinta ta kira ta bata abincin su dana megadi.

Kwalliyarta tayi cikin riga da skert na jan leshi, babban falon taje ta zauna tana jiran dawowar A.A. tana zaune humaira ta fito waje ta nema ta zauna se zabga ma salma harara takeyi.

Da sallam ya shigo falon cikin husky voice d'insa, mik'ewa salma tayi tana amsa sallamar, k'arasawa tayi ta karbi briefcase d'in hannunshi, cikin yanga tayi mishi barka da dawowa.

d'akinta ta wuce taje ta ajiye briefcase d'in, ta hada masa ruwan wanka, ta d'auko masa jallabiyya da gajeren wando ta ajiye masa akan gado ta fito daga dakin.

A kusa da humaira ta same shi kome suke tattaunawa oho musu da alama dai rarrashinta yakeyi. Aranta tace kudai kuka sani jarababbu kawai🤣🤣🤣🤣, kuma insha Allahu duk sihirin da tayi maka seya karye in dai kana shan zob'on nan.

Cikin murmushi ta kalle shi tace na hada maka ruman manka. dubanta yayi shima murmushin dauke akan fuskar sa ya amsa mata, sannan ya tashi ya shiga d'akin. Mugun kallo humaira ta jefa mata tace "tsabar iya karuwanci ne harda had'a masa wani ruwan wanka?" murmushi salma tayi tace aiba lefi bane tunda wa mijina nayi, kuma kowa yasan ban taba yawan bin maza ba, bare a kirani da sunan karuwa tayi wucewarta d'aki. bin bayanta da kallo humaira tayi dan tasan magana ta fada mata, wato ita ce tayi yawan karuwancin lalle wannan shine in kasan nafad'a bakasan na mayarwa ba.

Atare suka fito yayi wankan shi se kamshi yake zubawa, ita kuma tana dauke da abinci akan tray, se da ta bari sun k'araso cikin falon sannan ta kalleshi tace " Akan dining zaka ci ko na ajiye akan carpet?

A k'ule humaira ta ce kin taba ganin munci abinci akan carpet?? murmushi salma tayi kafin tace aunty wai ai naga ya dawo daga aikine ya gaji bansani ba ko zai iya hawa kan dining d'in.

ki ajiye akan carpet d'in, inaga zaifi. ya fada yana zama akan kujera, ajiyewa salma tayi sannan ta zuba musu. Abincin suke ci ba wanda yake magana a cikin su, sosai yaci abincin dan ya manta rabon dayaci tuwo, dan shine best food d'insa amma humaira bata taba sawa anyi masa ba. Humaira ma taci taliyar sosai amma bata sha zob'on ba, exotic ta dauko a cikin fridge din falon.

Bayan sun gama salma ta tattara kayan takai kitchen, ta sake wanka tasa kayan bacci tayi kwanciyarta. Ganin salma bata dawo bane yasa A.A yima humaira se da safe, ya ce mata bacci yakeji dan ya gaji da yawa, be jira jin abinda zata ce ba yayi shigewar sa part din salma, ya barta a zaune ta rasa ma abinda ya dace tayi.🙉

Yana shiga dakin ya cire jallabiyar ya saka kayan bacci, kwanciya yayi ya jawota jikinsa yayi musu addu'a.

yauma haka suka tashi cikin dare sukayi sallah,da karatun alqurani. da asuba bayan sunyi sallah, ganin da salma tayi fuskar sa a sake yasa ta dauko hisnul muslim ta mik'a masa tace ya karanta azkar d'in. beyi musu ba ya karb'a ya fara karantawa.

bayan ya gama ya dubeta yace " please idan akwai saura tuwon nan kiyi min dumamensa" Amsawa tayi sannan ta gaishe shi, ta tashi ta had'a masa ruwan wanka.

A gurguje ta hada breakfast tayi wanka ta shirya. Bayan da suka gama karyawa ta d'auki briefcase d'in, har bakin mota ta raka shi. Basket d'in jiya ya ciro mata, tayi masa fatan alkhairi, har ya tayar da motan ya lek'o yace "kina da waya kuwa?" Kallon shi takeyi cike da mamakin canjawar shi. kafin ta girgiza kai, bece komai ba yaja motar sa ya fita bayan me gadi ya bud'e masa get.

Da rana tayi jallop din cous-cous wanda yasha kayan lambu da hanta, tayi had'in coslow, ta had'a zob'onta kamar yanda tayi jiya, tunani takeyi yau wazata samu yakai masa? sega jamila me aikinta ta shigo "aunty ga drivern gidan hajia yazo"

fitowa tayi bayan sun gaisa yake ce mata " hajia ce ta aikoni akan zan dinga zuwa ina kaiwa Alh. karami abinci, saboda jiya dana koma take tambayata ya akayi na dad'e shine nayi mata bayani"

Godiya salma tayi ta d'auko abincin ta kawo masa,ta mika masa bak'in leda wanda ta saka turmin atamfa da shadda se turaruka masu tsada, tace ya kaima hajia. Duk da tasan suna da kudin da zasu siya wanda yafi wannan amma ihsani yana da dad'i.

Aikuma hajia halimat taji dadin kyautar dan har Abdul takira take fad'a masa, sosai yayi farin ciki k'imarta ya sake daduwa a idanunsa (mata mu kula yin kyauta ma 'yan uwan miji yana dada miki kima a idanun mijinki, koda su d'in basa kaunar ki to karki ce baza kiyi musu komai ba kiyi musu gwargwadon iyawan ki ALLAh yasa mu dace)

Da daddare da A.A zai dawo ya siyo ma salma waya ki'ran iphone 7. sosai salma tayi farin ciki,tayi masa godia sannan tace ya bata numbern hajia tana son zasu dinga gaisawa, yaji dad'i kuwa ganin yanda take nuna tana son iyayen sa.

Atak'aice haka suka cinye kwana 7 ba abinda ya tab'a shiga tsakanin su na auratayya, sannan kullum se sun tashi cikin dare sunyi nafila da karatun alqur'ani da safe ta bashi littafi yayi azkar ga kuma zob'o da take hada masa da ganyen magarya da ayoyin shifa dan karya sihiri.

Acikin kwana 7 dinnan kusan duk wani sihiri dake jikinsa ya karye, har tunani yakeyi ta yanda ya auri humaira.
Chapter 11 · 0% Book details