← Book details Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 13

Sashe 4

Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman waleed ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJI NE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE*🥗

*Ayya wai ina kuka shige ne Auntyqueen mermue da sis Billy ladan sis Meelat ahk ina tanemanku*😔Duk inda kuke Allah yasa daku da alkhairi.

*Wato na lura kufin son Abul fa ita Rukky bata da Team sai shi bari naga Abul da Rukky waye yafi Fans saura ku nuna son kai*🤕 luv oll😍
idan kuka ba abul zuciya nikuma na zugata takawo wani guy....😜

1⃣3⃣🌹1⃣4⃣

" A kwai mafita d'aya shine bari na duba wani abu akansu" nanma zane yayi ya goge yasake ya goge wani irin zufane yake karyo masa kama wanda ake watsa masa ruwa kallonta yayi cike da karya yace " a gaskiya Yaro nan bakaramin son yarinyar yake ba gaahi har Uwarsa ta amince haka kuma suna tsaye akan wanna alamarin abinda ya dace shine akan yarinyar zamuyi aikin duk da itama bata wasa da ibada sai dai a duk lokacin da take cikin matsanancin bacin rai bata saurin ambato Allah da wuri don haka zamu tura mata wanda zaisa mata k'iyayyar yaron sosai a rainta yanda zata tsane shi amma shima ba wani dogun aikin zayi ba sabida duk rananar da ya kusanceta karfina maganir zai ragu don haka dole kikula kisan yanda zaki jata ajikinki har tasake dake sai ki hanata yarda da shi kinuna rashin fahimta yasa baki kula amma yanzu kome ya wuce."

shiru tayi tace " anya me buzun kura nasan halinta tuntana Yarinya nake k'inta zata yarda dani kuwa "
tsawa ya buga mata yace " duk abinda kika ga dama kiyi 6ace min da gani kafin nasa a juya miki kanki baya ga wannan hayakine kinayi aljanin k'iyayyar zai baiyana aikin hayakin amma ku lura da lokacin da take cikin da 6acin rai kome kashinsa zaiyi amfani fita min da gani "

jikinta har wani rawa yake sabida tsoran wani banza.

🌹🌹🌹

Bayan ta gama labaran cikin harshin turanci karfin tara na safe d'akin rawotanni ta shiga tasami kawarta Zulfa'u sau d'aya ta kalleta sannan ta kauda kai tayi ta zauna shiru yabiyo baya Zulfa kasa hakuri tayi dole ta katse shiru tace "Rukky magana na gaskiya shine babu yanda za'ayi kisami miji a wata biyu kacal sabida baki san halinsa ba shima baisan naki ba ina ganin kiyi hakuri da Abul mana inda bake koshi wani cikinku yafad'a Abul bai kai talatin ba wallahi bawanda zai sani tunda har yafito ya fad'i miki yana sonki kawai ki amince sabida kinsan halinsa gaba da baya."

cike da masifa ta kalle Zulfa tace " haba dai yaron danayi masa hidima tun yana karamin kice na yarda na amince da shi akan yana sona habawa wallahi da sake duk wani sirrina duk saiya bude har nayi rayuwar aure dashi kai kai mun kwanta gado d'aya sanna nakira shi da Uban Yarana tab badani ba wallahi gwara najira subani kowani irin mutum amma banda sa'ar Yaseer "

dariya Zulfa take kyalkyalewa har tana dukan tebirin tace " wayon cikina Rukky Alhassan zakiyi abin kunya ko na ga haka shiyasa duk lokacin da yazo nan jikinki har wani rawa yake sabida tsoransa amma ba damuwa wata rana kece zakiyi haukansonshi Narantsen da Allah sarki"

bata sake kulata Zulfa ba sabida ta lura zata kara mata wani ciwon kaine.

🌹🌹🌹
Da dare bayan dawowar Alhj Attahir suna hirar yake fad'a mata irin nasaran da suka samu xuwan Abul wajen sayard da motocin ba karamin riba suka samu ba fatan alkhairi Umma ta masa sannan tace " Alhj Abul fa aure yake nema a cikin unguwar nan"

shiru yayi da jin abin dariya can ya sa dariya yace" yaunshe ka haife shi da zayi tunanin aure ? kuma wacce yarinyan ce haka da ta6ata lokacinta akansa ?"

haushin maganar Umma taji tace " ba shikenan ba amma yakamata kasan halin da yake ciki shine gaskiya domin ko azumin da yake ai da yakare kanshi yake amma ba damuwa."

Murmushi yayi kafin yace " wallahi Abeeda ina son yayi nima nasan me yasa yake azumin amma wacece Yarinyar "

"Rukayya ce yar gidan Alhj Hassan ce daga ita yarinyar har mahaifiyar ta sunki yarda sabida suna gudun abindan mutane zasu ce " abinda umma tace kenan,

farin cikine ya kama shi yace" wa Adamu naso haka ashe Abul shine mijin toh gobe da asubahi zama Alhj Alhasan magana shikenan inyaso ita yarinyar kwaji da ita

🌹🌹🌹

Inna kiranan Sa'idu yayansu Rukaiyya tayi ta fad'a masa yanda sukayi da Abul yace zaizo su maganar bata waya bace.

gashi sauran kwana hud'u wahadin yacika duk ta d'imance kaman wacce akace wahadin mutuwar tace.

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀

Mmn Waleed ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJI NE
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY_

*REAL ME DAMBU CE🥗*

_Y'AN UWANA MARUBUTA NAGODE ABISA ADDU'OIN DA FATAN ALKHAIRIN DA KUKE MIN INA ALFAHARI DAKU_

*Wanna shafin bana kowa bane nakune sadaukawar*

*_DAMA TA FANS_*

*_MISS _ MARRIAM NOVEL GROUP_*

*_NASIBI WRITER'S ROOM_*

*_MUMMY RABI_*

*_AUNTY BINTA BABANGIDA_*

*_MY RIGIMATION_*😜

*_MAMAN SADEEQ_*
KALPANA💅

*_MOMIN NASRIN_*😍

*_MMN AMAL,MY SHEMA,ADDAN JELATA,MMN NOOR,MMN'AL'AMIN,NEENA,_*
Da wanda basu ji sunan ba inayinsun sosai😍

Mmn meenat Allah yaba yarona lafiya🤧

*Deeja Waziri tare da Bie bie dee ina tayaku murna k'anmala buks dinku lafiya Allah yabaku ikon fara sabi lafiya*🤝🏼

*Naki daban ne Aunty maijidda musa* Ana tare🤝🏼

🎁H.A.W.🎁

1⃣5⃣ 🌹1⃣6⃣

Bayan Inna ta gama waya da Sa'idu sai takira Yaseer wanda yake service a ondo ta fad'a masa ay shikan kai tsaye ya amince dariya yayi kafin yace " Inna wallahi billahi azim Abul khairi shi yafi dacewa da Didi sabida nasan halinsa ciki da waje banda Didi banta6a jin ya kira wata mace a gabana ba yankance shi in Allah zai bashi mace ya bashi mace kamila kama Didi kullum maganarsa kenan tun muna scndry har muka rabu ya tafi gana duk wani saurayin da yazo wajenta shi yake koransa lokacin da na tambayi shi meyasa yake koran mata Samaruka cemin yayi wallahi baisani ba amma da zarran ta ganta da wasu maza ranshi ke 6aci duk hutun da zai koma Inna wallahi sai yayi kuka sabida Didi Inna Abul nasonta son da wallahi baki bazaiya furutawa ba amma kitunani akan haka duk zuwansa tsarabanta yafi nakowa amma duk yanda kukayi shine mai kyau "

wani farin cikine ya rufe Inna tace "ba damuwa bari naji me Y'ayanku zaice ."

Da wannan sukayi sallama

dan haka yanke hukumcin fad'a ma Babansu da ya dawo ta fad'a masa shima dariya yayi yace " toh shi kuma wato sunna zai d'abaka ko Allah yasa mudace amma fa tayi mashi girma ina shi ina Uwar d'akinsa banda namiji toh Allah ya tabbatar "

"Amin" Inna tace,

🌹🌹🌹

"karfe biyu da rabi na dare mafarkin da yasaba akanta y'au ma shi yayi dole ya tashi yayi wanka ya d'auro alwala sannan ya tada sallah nafila raka'a biyu yayi sanna ya d'auki alqur'an yqfara karatu ya dade yana karatu kafin ya rufe ya fara kwararo addu'a akan Sahibarsa Allah ya dai daita al'amarinsu nanma ya dade kafi ya tashi ya kwanta.

Da asubahi ma saura kad'an ya makara sai da Abbansa ya tada shi bayan an idar da salla ne duk suka fito shikan gida ta tawo Abbansa ne ya tsaya da su Baban Rukayya bayansu gaisa ne da yake dukkansu Baban Rukayya da Kanensa Abban Abul yace " gani dai a gabanku amma narasa me zance muku bansa ya zaku d'auki abinda zan fad'a ba "

shiru yayi

Babansu Rukayya yasan kwanan zance amma yafi son yaji daga bakin Alhj Attahir

duk sun kagu da son jin meke tafe dashi Baba Yakubu ne yace " Alhj karka damu ka fad'a mana kawai "

ajiyar zuciya yayi kafin yace " daman Yahya ne yake niman izinin neman auren Rukayya "

duk mamaki ya rufe su Baba Hameed ne yayi karfin halin cewa " Alhj kansa me kace kuwa "

"ehh dagaske nake fa ba da wasa ba saidai ko baza ku bashine " yace,

Baba Tanimu yace " a'a ba haka bane kawai muna gudun magana ne amma tunda shine yake son mun bashi ita Allah ya tabbatar"

Baban Rukayya baice kome ba sai murmushi da yayi.

Baba Baseeru yace " Yayan baka ce kome ba sai fama murmushi kake "

dariya yayi kafin yace " me zance tunda shi Yahya duk Yan mata unguwar nan basuyi masa sai tsohuwar y'arku " sai kuma yarike baki alamun yayi
kato6ara.

Dariya suka saka dukkansu 6ata rai Abban Abul yayi yace " bana son haka fa Alhj hassan y'artawa ce tsohuwa bakai ba takwara na fad'a maka "

dariya sukayi masa haka suka rabu cike da raha da farin ciki sai tattaunawa suke har suka shiga gida lokacin shida da arba'in da biyar dai dai itama tafito kenan tana da labarun karfe bakwai sai sauri take a dai dai zauren cikin gida suka had'u tsugunawa tayi kasa ta gaishe su , duk suka amsa Baba Hamisu yace " mamana muna sa idonki fa gobe inbaki samun ba toh munyi miki miji "

a razane ta d'ago kai sai kuma ta mayar kasa tace " bani da zabi sai naku "

Baba Tanimu yace " jeki Allah yayi miki albarka a dawo lafiya"

"amin " tace,

sukuma suka shiga gida kowa ya kama gabansa zuwa aiki.

🌹🌹🌹

A wajen aikin ma dakyar tayi aiki domin bata da kuzari har tashi daga aikin me nape ya kawo ta tana sauka tabiya kud'i zata shiga ashe shima yana kan motarsa durowa yayi yasa kananun kaya sajinsa da y'ar gemun wanda suke had'i da juna sunsha gyara fuskansa tayi wani fass da shi cikin takun kasaita ya shiga zauren yayin da ita kuma take tafiya cikin nutsuwa har tashigo zauren kamshin turarensa ya shaka sai da ta lumshe idanun ta kafin ta bud'e akasan shima ita yake kallo yace " Preety barka da dawo nasan kin gaji da yanzu kina da miji ai dasai yayi miki wanka ya baki abincin da ya dafa da hannusa ko "ya d'aga mata gira.

Tsaki ta ja bata san lokacin da bakinta tace " d'an iska Yaro kawa....."😳

Mmn Waleed ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJI NE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_
Chapter 4 · 0% Book details