← Book details Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman Waleed ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJINE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE🥗*

*🏹 HIKIMA ASSO WRITER'S🏹*

*Farin cikinku shine namu*🤝🏼

*Maman sadeeq nagode da addu'arki Allah yaraya mana sadeeq Kalpana*💅

_Reader ana tare_🤝🏼

5⃣🌹6⃣

Fitowa tayi daga d'akinta tazo waje Inna a kitcher shiru tayi taki magana kamshin turarenta Inna taji ta d'ago murmushi tayi sannan tace " masha Allah gashin nan kikai mata kice tabawa bak'on ghana maza kije "

kwallane suka cika mata idanun amma haka ta boye su domin sam bata son wani abu ya had'ata da gidansu Abul sabida yanda take ganin ya koma d'an air dole.

Haka ta d'auka tafi daga gidansu sunan yanda ta barsu haka ta wuce tabarsu suna halin nasu wato gulma da habaice banza tayi dasu abinda ke damunta yafi karfin surutunsu.

tafiya takeyi amma duk ilarin jikinta rawa yake ba ita takeyi ba haka Allah yayi ta ba wani tafiya tayi ba domin makotarsune.

Tana zuwa sai datayi knσckíng kafin megadin yabud'e mata yana washe bakinsa yace " a'a malama Rakiya kece haka kaii gaskiya kinyi kyau fa sai kace daga turai "

wani kallon banza tayi masa domin bawai yana da kamun kai bane shi yasa bata kula shi cikin gidan ta wuce abinta shima bin bayanta yayi da kallo yana lashi baki aransa yana aiyana yanda kyan jikin Didi domin koshi akace an bashi ita toh ba karya mutum zai huta sosai.

murd'a hannun kafor shiga cikin gidan tayi da salllama tashiga.

Yana kwance akan doguwar kujeran da ya kawata falon ga wani Cinema tv dake fama aikin tunda tashigo yaji wani kasala ta rufa masa wanda dole yasa ya Lumshe kyawawa idanuwarsa kafin

ya amsa mata da "Wa'alaikum salam "

tashi yayi ya zauna kallonta ya tsaya yanayi tunda ta kalle shi sau d'aya bata sake ba shima kallonta yake sosai duk tawani sake halin ina son ya mata magana amma ta tsare gida dole ya fara abinda dole za sata magana jan yaji ya fara can kasan makoshi yace " Didi Umma kike nema tana d'akinta "

wani hararar da ta maka masa yasa gimtsi dariya da ya taso masa tashi yayi yazo gabanta murmushi yayi yana jin dadi yanda take 6ata fuskanta k'ura mata ido yayi.

A hasale tace ’’ me haka bana son rashin kunya Yaro karamin sai iskan tunbaka tafasa ba har kana shirin konewa mitsssw" taja tsaki.

Ranshi 6aci yayi shi ba zaginsa da tayine ya bashi haushi ba ce mishi datayi yaro shine ya bashi hausho yaji zafin maganarta

don haka ya bude bakin yace " Didi kinmanta Yaro ma namiji ne wallahi abinda yaro zayi ko d'an shekara arba'in bazayi iyaba kuma kika cigaba da cemin yaro toh wallahi da kafarki zaki gudu daga yau nabar sake kulaki "

farin cikine ya rufata har Umma tafito ta gaisheta sannan ta bata aikan Inna sanna ya mata sallama tafito daga gidan yana d'akinsa yake lekota ta wíndσw har tabar gidan.

🌹🌹🌹
hankalinta kwance tarabu da k'aya daga wajen aikinta sai gida sai kuma islamiyya datake zuwa tare da Inna kusan sati uku kenan da dawowar Abul amma ya yaki shigowa gidan sabida abinda Didi tayi masa da dare yayi niyyar shiga gidan ana fita sallan Ishahi yashirya cikin kananun kaya yashiga gidan tun kafin yakai kofar zauren farko yaji kamshin turarenta doh haka idanun yacigaba da bazawa can ya hangota jikin wani mota tana jingine ajikin motar tsaki yayi sanna yayi kwafa.

Yace " don Allah dube shi dawani rusheshin cikinsa kama tukunyar giya "

karshe basa shiga yayi sabida bacin rai sai masifa yake tayi shi kad'ai kasa hakuri yayi ya koma yayi musu sallam dukkansu kallon Alhj yayi ya e " Babana bakasan kana nema kan nema bane ai har an karbi sadakin wani wallahi dagaske kuma Yayanane "

shiru mutumin yayi yace " kayi hakuri sai anjima" yaja motarsa yayi gaba tsananin yanda ranta ya6aci gefensa tabi ta shige bin bayanta yayi yace " Didi kiyi hakur,,,"
tas ta kife shi da mari tace " kai wani irin yaro ne haka da fitina me na maka haka me zafi "

mamaki da tsorone suka dabaibaye shi jan hannunta yayi har cikin zaure kafin ya had'ata da bangon yace " ni yaro ne na mutu akan Sonki shine sanadi indai maza dubu zasu zo nikuma zan kore su Wallahi Ina raye ne sabida sonki kuma zan mutu da sonki karki sake cemin yaro daga Yau kuma ni zan shiga neman aurenki hmmm sai kinyi kukan jini a hannuna wanda bata san me sonta ba duk sauran jikinki suke hari nikuma kenake Kauna"

Maman waleed ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJI NE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*HIKIMA ASSO WRITER'S*

*REAL ME DAMBU CE*🥗

7⃣🌹8⃣

Mutuwar tsaye Rukaiyya tayi sabida abinda yafito bakin Abul tsoro da mamakinsa ne ya kamata.

cewa tayi nashiga uku ni Rukaiyyatu wanna abun kunyar dame yayi kama ace Abul khairi shine ke sona ay wanna maganar tana fita toh wallahi ko fita sai tafi karfina wasu zafafan hawaye ne yake zuba daga idanunta daga karshe tarushe da kuka zama tayi a wajen tayi me isarta dole tatashi ta koma cikin gida d'akinta tashige ko wajen Inna bata shiga ba don haka bawanda yasan meke faruwa tunda ita ba gwanar magana bace.

Koda Abul yakoma gida yanda yashiga ciki a hargitse yasa Umma ta kalleshi huci kawai yake sai kace wani maciji shiru tayi data ga bayi da niyyar magana ita takatse shiru tace" auta lafiya kashigo min haka me yafaru baka shiga gidansu Rukaiyyan bane ?"
sai da yagama hucinsa kafin ya bud'e baki yayi magana yace " Umma wai har yanzu ni Yaro ne ?"
shiru tayi na wani lokaci tana murmushi sanna tace " eh toh a wajena da Abbanku kai yaro ne amma me yasa kamin wanna tambayan "
tashi yayi yana dariyar mugunta yace " ba kome Ummana"

" Kai kasani kashigo kama wani k'ububuwa sanna kace ba kome ooohon ka "Umma tace ,

🌹🌹🌹

Tun daga ranar basu sake had'uwa ba sabida yana bin Abbansu wajen sayar da motocin kullum yana busy babu lokaci gashi garin damina in y'au ba'ayi ruwa ba to gobe za'ayi rana a tsaka ya fara azumin domin yana cikin wani yanayi dole ya fara alhamis da litinin idan yana azumin da wuri yake dawowa gida don haka y'au monday yana yin azumin.

Kuma ya tashi da son shan kunun gyad'an Inna da wuri ya dawo gida a falo yasami Umma sai da suka gaisa kallon shi tayi tace " wai ni Babana azumin me kakeyi ne haka kusan sati guda kenan kana azumi meke damunka ? "

y'ar sajinsa yashafa yana murmushi yace " my Umma ay azumin nafilla nakeyi ko babu kyau ne na daina "

"A'a bazan hana ka samun lada ba amma idan kana da damuwa ka fad'a mana mu iyaye ne masu adalci kaji ko " Ummansa tace masa ,

yace " babu kome Ummana ina son shan kunun Innarmuce dashi zanyi bud'a baki "

hararsa tayi kafin tace " kaniyarka mata tana fama da aiki zakaje kasata wani damuwa bari nasa Tabawa taka kawai "

" A 'a wallahi nata nake son " da sauri ya bar falon yana dariya

garin yayi duhu alamun ruwa za'a zuba sauri yayi yashiga gidan yana addu'a Allah yasa kar ruwan nan ya hana Inna masa kunun domin tana da Athma bata shiga ruwa kome tayi dole tabar shi sai an gama shi yasa Babansu Rukaiyya yayi mata wani kincin a kofar shiga falonta tawaje kenan.

yana shiga ana fara yayafi da gudu yashigo baranda yana haki zaro ido Inna tayi tace "a cikin wanna had'arin kafito baka tsoran murane ya kamaka "

yar dariya yayi kafin ya durkusa har kasa yace " Inna ina wuni ya damina ya hakuri damu "

murmushi tayi sanna tace " don baka son na maka magana shine kayi saurin gaishe ni ko toh lafiya hakuri dole muyi daku damina kuma alhamdu lillah lokacinsa sai y'au kashigo mana "

sosakai yayi yana dariya yace " Inna ina bin Abbanmu wajen sayar da motocinsa ne shi yasa Inna kunun gyad'a nake so ina azumine don Allah zansamu Inna "

dariya tayi sanna tace " toh kashiga falo ka zauna insha Allahu kafin biyar da rabi zan gama "

yace " toh Inna nagode sosai " falo yashiga ya zauna yana duba abu a wayarsa.

Inna kuwa ta window kicin takira Deeja y'ar Baba Basiru da yake Mamansu suna shiri sosai da Inna kuma Rukaiyya y'ar d'akin Hajjon ce shiyasa duk matan gida suke jin haushinsu.

Inna tace " kizo amma kid'auki lema fa karki jike "

tace " toh "

gyad'an Inna tad'ebi rabin mudu tazuba masa ruwan zafi tabarshi yayi kama min biyar lokacin har Deeja ta zo faran shinkafa ta wanke ta jika sai da sukayi min biyar din sanna taba Deeja ta wanke gyad'an tq hada da shinkafa waje d'aya tace " kai gidan Shamsiya a nik'a miki yanzu kika kawo min" tana fita Inna ra fere dankalin turawa sai data dafa kafi tayi grate dinda a abin kankare kubewa sanna ta d'auko kwai guda goma ta fasa akai maggi,curry,thyma,gishiri,albasa,attarubu,duk ta zuba lokaci d'aya saida ta had'ashi sosai sanna takula a laida tasake mai dashi kam wuta tana cikin haka Deeja ta dawo da markad'an kunu Inna ta zuba ruwa ita kuma deeja ta tacce sanna Inna ta nuna mata yanda zata na juyawa har yayi k'auri aikin sosai sukayi har suka samu abinda Inna ta kula ya nuna saukewa tayi sai da yayi sanyi kafin Inna ta juye a tire tana masa yanka *awara* Deeja kasa hakuri tayi tace " Inna me sunan wanna "

dariya Inna tayi tace " awaran dankaline kenan yanzu zan masa y'ar miyarsa " wanna karo karas, kabeji,green pєpє,green beef, albasa,sai attarubu, wanke su tay kafi tayi chufin dinsu dukka tazuba a cikin farayi fan tasa y'ar mqn turking dinta da maggi da gishiri taci gaba da suyawa Deeja na kula da awaran dankalin.

Da sauri Rukaiyya tashigo da sallqma leka su Inna tayi Inna tace " maza kije kicire kayan sanyin nan "

"toh " kawai tace ,
Chapter 2 · 0% Book details