← Book details Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 13

Sashe 10

Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tashi yayi ya d'auko mata da cup tatsiyaya a cikin cup tabashi yashanye tasake bashi yashanye a karo na uku ne ya girgiza kai alamun ya isa kenan.

Zuba musu idanun yayi yamarasa ta ina zaifara cikin sanyin muryarsa yace " Inna me narasa a tare dani wanda Rukayya bata son? shin Inna laifine don na so Rukayya? Inna laifine Yaro kamana ya aure Rukayya ko sunna da nayine laifin ! "

tun baice ga abinda tamasa ba jikin Inna yayi sanyin tace " duk abinda kalissafu duk babu hujja a cikin da mace zata ce baka kai ba, kana da mutunci sanin yakamata uwa uba kai nagartacce So da ka nuna wa Rukayya mu karufawa asiri ba ita ba bansan me tayi ba amma don karka saketa bansan me zancewa mutane ba,"
karshe maganar muryarta na rawa kaman zatayi kuka.

"Banta6a tunanin saketa ba amma nazo wajenkine a matsayin Uwa kibani shawara akan me yadace nayi Inna bansan duk kiyayyan da take min zata iya zubar min da jinina ba sai y'au ashe cikine da ita taje aka mata allura tazubar min da shi ....,,, sunkuyar dakai yayi sannan yace gaba da magana bana son kowa yasa haka har Ummana domin tana jin abinda tayi zata tsaneta wanda haka zai shafi zamqnmu da ita shawaranki kawai nake nema "

hawaye ne ke zuba a idanun Inna tarasa me za masa tace.

Sa'idu cike ta bakin cikin yace " kasako y'ar iska kafin nan kamata shegen duka "

Abul yace " bazata ji haushi ba sai ma farin ciki kusake shawara "

Hameeda da tagama cika fam tace " toh kasake aure kawai mana "
yace "Momin Yusra Rukayya nake so bana jin zan so wata bayan ita indai tana raye bani ba kara aure "

zuba masa ido Yaseer yayi kafin yaja gwauron numfashi yace " bazaka saketa ba bazaka kara aure ba toh kayi nesa da ita matukar kana kusa da ita ranka kara 6aci zatayi kaduba maganata da kyau."

Dukkansu ya basu tausayi Inna tace " tashi kakai ni wajenta "

"toh "yace , sannan yatashi hijab Inna ta d'auka suka fita zuwa asibiti a cikin mota Inna tace " kace baza kayi duk abinda suka lissafu ba amma kayi hakuri kuyi nesa da ita zaka ji saukin abun naji Yaseer yace zaku tafi karatu da ita kaje kawai kabarata anan kayi hakuri .

Shiru yayi duk da tamasa laifi bajin za'iya nesa daga gare shiyasan irin son da yake mata amma tunda Inna tace yatafi dole yatafi yabarta ko zuciyarsa tayi sanyin.

Har suka isa hakuri Inna take bashi.

Nunawa Inna yayi d'akin don bazai shiga da sallama Inna tashi dakyar ta amsa sallamar ganin yanda fuskan Inna ya sauya sai da gabanta yafad'i tsoro ya kamata har gabanta Inna ta karasa.

Sai da Inna takare ta kallon sannan tace " banta6a tunanin zaki iya zubar da cikin ba kai ko shege ne wallahi bana tunani haka ballata d'an sunna hmmm uban wa yabaki wannan mugun shawaran toh wallahi kinemin wata Uwar bani ba na yafe ki tunda kuma na rantsi da Allah sai nasa shi yakara aure kije Allah zai bashi wacce tafiki kome "

tana gama maganar takad'a kai tafita cike da takaice kuka Rukayya tasake tace " Allah ya isa tsakanina dake Inna kulu kinraba ni da kowa har mijina da iyayena."

bayan fitar Inna gida Abul ya kawo ta sannan yaje ya fad'awa Umma taji ba dadi sannan tace " kana da fitana ba mamaki kaine kaja haka tafaru yanzu waye a wajenta "

yace " babu kawo ita d'aya ce kawai "

"tashi muje ka kaini " kayanta ta d'eba kala hud'u sannan suka tafi sunje sunsamu har wannan lokacin kuka take.

Hakuri Umma tabata shi kuwa ko kallon bata ishe shi ba.

🌹🌹🌹
Cikin satin Abul yashirya tafiyansa yake fir Umma ta hana ayi mata wankin cikin kwananta shida aka sallame ta gidan Umma ta dawo har wannan lokacin Abul baya shiga hidimarta.

Bakaramin azabtuwa yake ba da rashin ta daga ita har shi duk sunfita hayancinsu idan taji muryarsa takan rasa nutsuwar idan bai zoba kuwa har Umma ta ganewa bata cikin nutsuwarta idan ta ga haka sai Umma takira shi .

Ana shi bangaren yana haka ne dan ya hukuntata
🌹🌹🌹
tsayon sati ba labarin Inna kulu duk inda ake tunanin tana nan anje babu ita babu labarin.....

Mnn waleed ce

☔☔☔☔☔☔

*YARO MA NAMIJI NE*

💦💦💦💦💦💦

_🌹Love story🌹_

*Real me dambu ce*

Hikima Asso Writer's

Kuyi hakuri wanca shafin nayi kuskure nmb

3⃣8⃣🌹3⃣9⃣

Dakyar akasamu labarin tana Akt Baba Tijjani yace baruwan sa domin bai aiketa ba dakyar Baban Rukky da sauran Y'an uwan suka shawo kansa yaje dubata har lokacin bata san wake kanta ba.

🌹🌹🌹

Shirya shiryen tafiyan Abul ya matso domin saura kwana biyu ya tafi duk abin duniya ya dame shi kaman yace Rukky tashirya sutafi amma sai ya share.

Itama tashiga wani hali tarasa me ke damunta ga Inna da y'an uwanta suna fushi da ita duk yanda taso su had'u da Abul bata samu halin haka ba.

Ranar tafiyarsa da safe yashigo cikin gidan wasu kaya yakawo mata a cikin kwali anyi 🎁 yashiga d'akin yasamu tayi zurfi cikin tunani sai da yayi gyaran murya kafin tasan yazo tashi tayi tsaye tana kallonsa duk da zamansu babu tarairaya amma tana cikin kwanciyar hankalin kafin su sami wannan matsalar.

Cikin nutsuwa yace " gashi har da Atm card dina a cikin a kwai abubuwa a ciki nazo na fad'a miki ne zan tafi ghana naso muje tare amma yanzu haka baxai yuba.,,,,,,,,shiru yayu sannan yaci gaba da maganarsa kafi haka ta faru na fad'a miki a kwai albishir da zan miki gashin nan a ciki kiduba natafi da Sonki bansani ba ko zandawo da Sonki dan nasan nikad'a nake haukana "

yana gama fada haka yajuya da zafita da gudu tazo ta rungume shi ta baya tana kuka sosai shima zuciyarsa ce ta hau bugawa sosai zare hannunta yayi daga jikinsa sannan yayi murmushi......!

Yace " me nakuka baki sona ko...."

girgiza kaitayi tace " plss dn't lve alone i cn't lfe with yhu plss 4give my sin....don Allah Abul khairi "

karfin buguwar zuciyarsa takaru fiyye da yanda yake girgiza kai yayi yace " u with live alone Rukky yhu don't luv me yhu dnt be carfully wth my hrt but am still mad crazy bcos of yur luv am srry ilove yhu "

juya tafizgo rigarsa d'aga kafafunta ta karasa tsayi ta had'a bakinsu waje guda rike akansa tayi da hannunta biyu tana masa wasu hot kiss wanda shikansa saida ya da d'a rungume ta ya had'a kugunsa da nata jikin kofar d'akin ya had'a ta dashi karshe kasa tsayiwa sukayi suka zube kan gado wasu arnar salon yashiga nuna mata wanda itakanta batasan Yaro kaman shi yana da haddarsu ba can kaman wanda aka tsikara tashi yayi zai barta sake jawo shi tayi tana kallonsa tashi tayi ta zauna tasa hannunta cikin rigarsa tana shafa kirjinsa tana wasa da gashin kirjinsa janye hannunta yayi sannan yatashi ya tafi kuka tasaka sosai tana danasani.

Ashe romeo kan yabar Yaseer a cikin motarsa dama ya sallame Umma shiga

motar yayi Yaseer sai tsaki yake ja shi kuwa sai murmushi yake zabgawa indan ya tuna moment dinsa da ita na yanzu sai yaji kaman ya fasa tafiyar ma

haushi ya gama rufe yaseer yace " kaii d'an iska me nasani a gqba kana murmushi "

dariya yayi sannan yace " kasan mata da miji bame shiga tsakaninsu don haka wallahi kaman na fasa yawa a kwai passtport a wajenta duk lokacin da tashirya kasata a jirgi kawai sai ka fad'a min "

haka suka isa airport din.

🌹🌹🌹

Bayan tafiyarsa kwalin ta bud'e takardu passport ta gani sai key mota da wani d'an karamin akwati me masifar kyau sai wani farin takarda .

d'auka tayi gabanta ba fad'uwa har idanunta sun fara kawo ruwa domin a tunaninta Sakinta yayi.

Bud'ewa tayi ta fara gani y'ar short not ne yayi mata karantawa tafara kaman haka:

_Amincin Allah da Rahamansa su tabbata a gareki ya ma'abociyar kyau Bansan Ya zan fad'a miki ba amma ko take zan kwatanta miki Nafara sonki ne daga rnr da nazo basamu ana miki gorin miji bansan shine so ba sai da na tafi karatu a nan nazama mahaukaci akansonki na zama kurma ni makaho ne akan sonki a lokacin dana san da haka na kudiri a niyyar duk wanda yazo wajenki nine zan kore shi kuma sai akayi dace haka ta faru bab kore su dan kome ba sai don ina sonki Wallahi har na aureki banso nayi amfani da karfi akanki ba bayan haka banso nasaka miki magani a duk abin shanki ba nayi haka ne sabida hakkina a she kuskure na aikata banga laifinki ba don kin zubar da cikin nan ba domin idan nayi al'akari da mace tana bukatar kulawa da tarairaya amma baki samu a wajena ba kuyi hakuri ga passport duk lokacin da kika shirya ina jiranki domin nashirya ya mana sabuwar Rayuwa ga key da wannan sarkan kyautar nan takasa domin kinbani abu me daraja wanda yafi wayanan daraja da tsada kofa na abude take I LOVE YOU RUKAYYATU MA'ARUFA_

Urs

Yahya Attahir Adam

I miss yhu

kuka tafashe da shi tace " Honey iluv yhu am srry "

dai dai zai shiga jirgi kenan murmushi yayi yace " me too iluv yhu babe am srry too "

tace ".kayafe min laifina "

shafa kansa yayi yace " Allah ya yafe mana baki d'aya "

"Ina sonka sosai za tawo gareka very soon"

yace" da nafi kowa sa'a a duniyar nan da nanuna miki So zallah babu algus a cikinta "

wannan musayar kalaman babu waya zuciyarsu ce a had'e da juna.

Sorry da late dayi

Mmn waleed ce

☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NA MIJI NE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹Love story🌹_

*Real me dambu ce*🥗

Hikima Asso Writer's

_Yayi da nakansance da *Kishiyata Jahadina* Haka *Abu Zarri* za shigo rayuwata ba zato ba tsamani karshin *Sharrin cikin gida* yazo kafin nan sai na fuskanci *Kalubalen Rayuwa* domin dole na had'u da *Alexander* a lokacin zan tantace *So ko Sha'awa*_
Chapter 10 · 0% Book details