← Book details Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 13

Sashe 1

Yaro Ma Namiji Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YAROMA NAMIJINE*
💦💦💦💦💦💦

🌹 _LOVE STORY_🌹

*REAL ME DAMBUCE*

بسم اللة الرحمن الرحيم

*Kaman yanda nagama Asanadin bakin iyaye Allah kabani ikon gama su Lafiya Abinda na fad'a dai dai kabamu ladan inda nayi kuskure Allah kayafe mana*

MY AMNOUR ALLAH YABAWA ME GIDA LAFIYA

*MASOYA MAGOYA BAYA MASU WA ME DAMBU FATAN ALKHAIRI TOH GANI NAN NADAWO DAGA NIYYATA NA SABUWAR SHEKARA ZAN FARA KUKENKU YAYI YAWA BANA SON GANI DAMUWARKU YAROMA NAMIJINE YACE YANA BEGENKU*😘💞💋

*YAN UWAN MARUBUTA DA MAKARANTA NAGODE DA SUPPORTER DINKU*❤

_Sadaukarwa_
ga Maman 4, Asmaty,Momin nasreen, Ummu noor, Maman hashmeer,Aunty baraka, Addan jelata, my Shema'u, Nafi dotan Mmn4,Batul Jattko,Mrs Aliyu dangin sa, Mmn farida Faccala,Mmn meent mijin kwaila, Mmn sadeeq Dashen Allah lazy writer😎
Littafin nakune da fatan zaku karbe shi hannu bibiyu

*WALLAHI HAR ABADA BAZAN MANTA DAKU BA*
AMNOUR
NEENA_COOL
DR RUKKY MAI TALIYA
QUEEN MERMUE
ACTION BABY
AUNTY HALIMA KANGIWA
SHATU RAFI'A
AUNTY RAHAMA NALELE
QUEEN AYUSHA ILYASU
HAWWE
AUNTY FAUZAH CE
AYSHAT A MOH'D
REAL KHADY
Queen Beba
*Kashhh wallahi bansan yawwa kuba*
Me dambu tana gaishi ku🙋🏿‍♂

_________________

🎁N.A.W🎁
_Farin cikinku shine namu_🤝🏼

1⃣🌹2⃣

Ranta a jagule yake tun jiya da Umma ta fad'a mata Abul khairi yana tasowa daga kasar ghana zaizo hutun karshin shekara wani bakin cikine ya rufeta domin tana cikin zaman lafiya yana dawowa tashiga damuwa kenan domin duk Samarikanta duk ya koresu wanca hutun da yazo batasan me yake nufi da ita tarasa me ta tsare masa haka Yaro karami yasata a gaba gawani iskanci da yatsira shine yanda yake wasu abubuwa a gabanta kaman wanda yake gaban budurwansa ,duk wannan tunani tayi shine lokaci da suka iso unguwarsu domin tana cikin Keke napene don ta dawo daga aikine.

Suna isowa kofar gidansu ta hango shi yana zaune akan motar abokinsa wanda suke rashin kunyarsu tare.

Dkatar da me napen tayi yana isawa tafito tabashi kud'insa rashin canjane ya basu matsala.

Daga can Abokinsa yata6a shi " kai Abul khairi ga sugar Mommynka ta dawo fa..."
" Ameer dagaske ina take.."

"ke kauce gata a kofar gidansu suna neman chanji.."
sauka yayi a motar tana tafiya kana ganinsa kasan yakai cikaken namiji Yaro me kimanin shekara ashirin da hud'u d'an gatan Yaron da iyayensa suke alfahari ga ilimin addini gana boko,

cikin takun kasaita ya isa wajensu "Assalamun alaikum.."

me nape ne ya amsa masa da " wa'alaikum salam.."

"malam jeka da kud'i zan biyata "

cike da mamaki me nape ya kalleta " hajiya kina jin Yayanki yace natafi da kud'inki"

raita a 6aci ta kalle me nape " ay bashi ya baka ba don haka kabani canjina "

wani murmushi Abul khairi yayi domin ya fad'i haka ne don ya zolayeta kuma yayi nasaran haka dubu d'aya ya zaro " malam bata nata gashi Allah ya bada sa'a"

bakin ciki ya hanata ma karben kud'inta shine ya karbe me nape ya tafi abinsa cikin zauren na biyu ya same ta yasha gabanta.

"Wai menayi ne haka dakika tsane ni haka y'au fa na dawo kamata yayi ki manta da kome tunda yawuce abinda ya faru tun baya kike ajiyewa a ranki ba kyau yana sa mutum tsofa.."

wani kallon banza tayi masa a madadin yaji haushi sai ya wani lumshe idanunsa masu d'ankaren kyau ga girma wani iska yaja a bakinsa kafin ya fara tsotsan bakinsa,

tana ganin haka ta girgiza kai " bani hanya na wuce ko na mare ka.." matsawa yayi yana kallonta daga sama har kasa,

himar din da tasa irin me kama jikine gashi duk yabi jikinta ya kama wannan Coca cola shif dinta yafita rass dasu albarkattun kirjinta sunan yanda suke wani murmushi yayi sanna yafara magana da haka

" Didi Rukaiyya na zata zanzo na samu wani ya d'auke minke amma ba damuwa wqnnan karo da karfina nazo..."
yafadin haka ya bata hanya ta wuce bin bayan yayi da kallo yanda take tafiya sai da tsigar jikinsa ya tashi harta gashin jikinsa sai da suka mike tsaye "Didina kenan kina wuta ina binki da soyayya "

yana fita yasame Ameer yana jiransa " kaga ni kwanciya zai shiga nayi sai anjima kenan "

" ba damuwa ango tsohuwa "
da haka kowa ya kama gaban.
🌹🌹🌹
Rukaiyya tana tashiga matan tasamu gidan da suke tsakar gida suka hawu jefa mata habaici Inna kulu ce fara sauran suka amsa mata yaransu suka saka dariya bata ko d'ago ta kallo su ba tashiga kofarsu tasamu Innata tana soya masar shinkafa " sannu Inna ya aiki "

murmushi Inna tayi " Uwat ay ke yakamata na tambaya ya aiki "

dariya tayi domin kullum haka sukeyi ita da Innarsu " aiki sai godiyar Allah kome yana kyau "

" aha masha Allah jeki huta nasa kind'ebu rana sai kace ba damina ba " inji Inna ,

"yawwa Inna wanka ma zaiyi yanzu "

daga waje Inna Kulu fara magana " ay dole Yarinya tarik'a tana neman abokin hutu babu dole akare da bin abonkan aikin ana gurjan sauran abinda suka rage ko ba haka"
" haka ne Inna Kulu "
duk suka fashi da dariya

Maman waleen ce
[21/12, 14:59] Hassan Atk: ☔☔☔☔☔☔
*YARO MA NAMIJI NE*
💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE*

*Nagode da addu'arku had'i da fatan alkhairi*😘

😆😆😆😆😆😆
Yasin zaku sani yin abin kunya wato kuna kishi 👉🏽M4 ko toh ku shareta Ina yinku sosai🤝🏼

Aunty maijidda Musa😘
&
Oganniya😍
Shafin nakune😘

*Madeena marubuciyar Rayuwar taslim na gode da irin kulawar da kika nuna min*💞

_Wallahi bansan yawarku ba Amma Yar manga tana miki sakon godiyar Allah ya had'a fuskokinmu da Alkhairi_Am real Love you Fans❤😍😘

3⃣🌹4⃣

Kukane ya kwace mata sosai meta nema tarasa a rayuwarta abu d'aya kawai tarasa wanda ta danganta shi da lokacine kawai.

Dariya taba sai dayi sosai kafin Innarsu tace " har yanzu bazaki daina kuka akan matan iyayenki ba ko ? toh kisa aranki kome lokacine aure na Allah ne bana mutum ba kuma da suke ce miki karuwa kinga na damu ko Babanki ya damu toh kisaki kome kikama Allah "

girgiza kaitayi sannan Innarsu tace " maza kiyi kito kikaiwa Hajiya umma masarta "

yanda kukasan aka kwad'a mata guduma haka taji maganar Innan kunkuni tafara tace "ni gaskiya zankira miki takwara tsohun kwano yakai miki "d'an kanin Babansu ne sunansa Sa 'idu shine suke kira da tsohon kwano amma sunan Kakansune

tsare gida Inna tayi sanna tace " ke zaki kai Dodon da yake gidan yacinyeki yar nema kawai tashi kibar min nan"

🌹🌹🌹
Gidan zaure shine sunan gidansu Rukaiyya amma mutane sunfu kiran gidan da sunqn gidan farare sabida gadon me gidan wato Alhj Sa'idu Jatau kena. da sukayi na farin fatansa shi din mutumin gombe ne kasuwanci ya kawo shi garin Kano daga bayan yaje ya d'auko matarsa Malama Rukaiyya yaransu takwas bakwai maza mace d'aya,

kuma ita babbarsu sai yan biyu Babansu Rukaiyya ke amma abokin haihuwarsa ya koma saishi *Alhassan* yana aikin gwanati a ma'aikan ilimi shi matarsa d'aya ce
yara hud'u mata biyu maza biyu

sai
*Baba Tijjani*,
yana da mata biyu da yara tara
yana kasuwan a kasuwan sabon gari

sai

*Baba Tanimu*,yana koyarwa wani scndry har yakai matakin vice din principal
shima matansa biyu yara goma mata shida maza hud'u

sai
*Baba Hamisu*,
yana aikin nepa yana da mata uku ya goma shabiyu maza biyar ma bakwai.

sai
*Baba Yakubu*, yana tukin babbar mota yana da mata hud'u yaransa goma sha hud'u kuma an auran da biyar daga cikin yaransa mata domin mazansa shidane sauran duk matane

sai
*Baba hamidu*, kayan miya yake sayarwa shima matansa biyune ya biyar yake dasu sabida yaransa suna mutuwane kafinsu girma

*Baba Basiru*, yana aikin koyarwa Buk ne kuma shine autansu yaransa ukune matarsa d'aya.

D'akinsu Rukaiyya itace ta biyu akwai yayanta namijin sunansa Sa'idu shima sai ita,sai Hameeda tana aure a nasarawa g.r.a Sa'idu yana da mata da yara uku maza biyu mace d'aya.

Hameeda yaranta biyu duk mazane.

sai d'an autansu Yaseer abokin Abul khairine domin lokaci d'aya aka haifesu,

Rukaiyya a kano tayi primary skull scndry kuma a azare tayi sabida Innarsu y'ar azare ce data gama shine Babansu yanema mata B.u.k da taimakon Baba Basiru sunso ta karanci *medicine* amma tace ita *mass com* shi takeso don haka suka barta da abinda take so shekara biyar kenan da ta gama amma babu miji saidai kuma tana aikin da gidan radio freedom ne a shashin labarai
A yanzu haka duk sa'aninta na gidansu duk sunyi aure har kanenta da domin duk shekara ake aura da yara mata da maza don haka gidan a had'i yake da sukurnen amma yayansu Rukaiyya baya cikin gidan yana , janbulo ana Baba yayi masa gida shi da Yaseer.

🌹🌹🌹
Abul khairi asalin sunansa Yahya ne d'an ga Alhj Attahir Adam babba d'an kasuwane yana shigo da motocine yaransa uku akwai Yayansu Abul khairi Adam sojar ruwane sai Hafixa itace sa'ar Hameeda sai Abul khairi karatu addini dana zamani duk sun kafa yaransu aka sai godiya Wannan shekara Abul khairi da Yaseer suka gama jami'a tun Abul yana shekara nabiyu a jami'a ya fad'a tarkon son abokiyarsa uwar d'akinsa kuma Didinsa domin shi yasa mata Didi ita tayi renonsa tun kafin yayi wani wayo amma yanzu an wayi gari sun koma wuta da ruwa wance zuwansa hutu duk wanda yazo wajenta shi yake zuwa yakore su, akan idonta yasa koran mata Samaruka akan wani Alhaji ne suka daina shiri domin har wajen aikinsau yabi shi yayi masa kashidi

shi kuma Alhaji yakirata ya fad'a mata tundaga ranar suka 6ata shine har yanzu basa shiri abinda yake sake had'a su shine yanda duk lokacin da suka had'u zai soma jan yaji ya tsotsar baki tayi rayuwar jami'a ta ga mutane da yawa amma yanayin Abul yana bata tsoro da mamaki taya yaron da yake da ilimin addini haka amma yanzu ya koma d'an iskan dole

🌹🌹🌹
wanka tashiga tayi da sauri sauri sabida yamma tayi tana fitowa a gurguje tayi shafe shafe sannan tasa doguwar riga baki mayafinsa tasaka rass tafito har wani kama suke da Amisha pate har jikin sosai kama da d'an rashin tsayin wato duntancin sai dai Rukaiyya baka ce amma me kyauce👌🏻
Chapter 1 · 0% Book details