← Book details Yanbiyun Macizai Part 1 Complete Hausa Novel. Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Yanbiyun Macizai Part 1 Complete Hausa Novel. · about 5 min read

P.E.W.A
Home of Perfect Writer's together we stand
ESSENTIAL WRITER'S
Pen
is mightier than
the sword
_______________________________
_______________
BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me
via: 09167472935
GARGADI
KAR A KUSKURA A CANZAMUN WANI ABU NA LITAFFIN NAN, TA KOWACE SIGA BAN AMINCE AYI AMFANI DASHIBA, KUHUTA LAFIYA
DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.
kowace adu
an da yazo bakinta tashiga karanto wa wani irin kara tasake jin alamar kamar wani abu kululu a karkashinta, dasauri tamikar da kafafuwanta tareda daga katuwan rigarta sama, a hankali tadaga gugunta sama nan da nan saiga kan jaririyar ya tafito
.. kasa kasa ta dinga karanto adu
a tana mai runtse idanunta ta wani sake dogon nishi a take jaririyan tafado
..sosai takeyin adu
a, tareda kara sakin nishi nan take wata jaririyar tabiyo baya babu bata lokaci
. a hankali tashiga sauke nufashin wahala jada baya tayi sanan taja rigarta tarufe
. Idanunta ne yashiga juya mata tashiga ganin ko ina biyu biyu
. Sakamakon jinninda yabile mata gyara kwanciyarta tayi dakyar a hankali tashiga lumshe idanunta kasa kasa tashiga ambaton sunan allah
lokaci daya tasake bude idanunta
.kwayar idanunta da yiyi fari sol yashiga kafewa a hankali a hankali
..lub yarufe daga nan rai yayi halinsa, allahu aqbar
zaune take a kan kujera irinta sarauta tadan kishingide a jikin kujeran, a yayinda bayi sunkai su goma wadanda suke zagayeda ita suna maiyimata hidima
...uku na zaune a gabanta
. Biyu na gyara mata fruits a yayinda daya nadaga gefe tana mika mata fruits din ita kuma tana karba tanaci a hankali
kallo daya zakayi musu ka fahimci ko wannensu a tsorace suke basa son suyi wani abu waishi kuskure bale har ace za
ayi musu hukunci dan haka suke taka tsantsan da ita
daga gefenta bayi uku ne a tsaye masu yi mata fifita
. Ana cikin haka ne saiga wata tashigo ciki dasaurinta tareda zubewa a gaban matar tana maicewa
takawarki lafiya magajiya kuma gimbiya a gurin sarki mai adallci allah yaja datsawon kwananki gaba
.gaba dayan bayin suka amsa da amen, jakadiya tacigaba da Magana tace ranki shi dade labari mai dadi dakuma gardi nazo miki dashi
.daga mata hannun tayi alamar ta dakata
juyawa tayi bangaren bayin dake yimata hidima
.da hanun tayi musu nuni dazusu iya tafiya dasauri duk suka mimike tareda barin gurin a hankali tadawo da hankalinta gurin jakadiya
.. cikin izzah tace aha inajinki
sasauta murya jakadiya tayi a hankali tace ranki shi dade komai yatafi yanda muka tsara yanzu nan muka gama maganar da sule yakuma fadamun komai yakankama yanzun haka, gimbiya aleesha dasauri gimbiya zalliha tace dakata
. kirata da sunananta aleesha, banason nakarajin gimbiya daga bakin kowace baiwa tayi kwafa
. dasauri jakadiya tace allah ya huce zuciyar sarauniyar sarki
.a hankali tace a akiyaye jakadiya tace inshallah sanan tacigaba da yanzun haka gimb saikuma tace aleesha tana lahira
Sanan koda ace sarik zai zagaya illahirin garin gembun mambila bazai taba samun gawanta ba, wani irin dariyane yasubuce ma gimbiya zaliha lokaci daya kuma tasake komawa ta hade
. Tace ina fatan babu wanda yaji wanan maganar kuma babu wanda yaga lokacinda suka bita a daren jiyanko
. Dasauri jakadiya tace babu ranki shi dade kafinma sushiga bangarenta saida na tabatarda sariki yabaro bangaren tukun na nakuma tabatarda babu mahalukin da yake numfashi a duniyan nan kowa yayi nisa acikin barcinsa sanan nayi musu jagora izuwa bangarenda take
ina kuma daga tsaye tafito dagudu tayi hanyar yama. Kinkuma san wannan hanya mai hatsarine bare kuma uwa uba dajin mambila
Gimbiya zaliya tawani sake murmushin jindadi a hankali tace jakadiya aikinki nakyau dan haka kyautarki ta dabance
kije zan aiko miki da tukuyicikinki akawo miki
..washe baki jakadiya tashigayi tareda murnan yau ta faranta ran uwar gijiyarta wato gimbiya zaliha. Tashiga fadin allah yabar mana ke gimbiya sarautar mata farar mace alkamban mata uwa a gurin magajin sarki
. Daga mata hannun tayi sanan tayi mata nuni da hanun alamar zaki iya tafiya. Dasauri jakadiya tamike dan barin waje . gimbiya zaliha tasake cewa dakata tacigaba dacewa idan kinje kikirawo min sarkin gida kice ,masa ina son ganinsa yanzu yanzu nan
. Cikin rawan jiki jakadiya tace
Angama ranki shi dade
.allah yaja daranki tajuya tatafi jiki na bari
niko mihz bareemah nace ajuri zuwa rafi wata rana tulu zaifashe allah dai yasa mudace idan muka dace mudafe kar yayan shugu su kwace
FADAR SARKI
Manya manya mallaman fadane suke a zazaune kusa da kujerar alfarma wace sarki yake a yayinda gaba dayansu basu a cikin nutsuwarsu saboda batar amarya kuma matar sarki wato gimbiya aleesha wace aka nemeta aka rasa tundaga daren jiya zuwa safiyar yau
sosai suke cikin tashin hankali gaba daya mutanen garin gembun mambila
..abun yadaure musu kai yana kuma basu mammaki kowa sai fadan albarkacin bakinsa yakeyi
..dogaraine kuda hudu biyu a gefen sarki daya kuma yana rike da bullalar dorina irinta dukan rakumi nan murdadiya mai taurin gaske
a hankali sarki ya dan daga kansa da idanunsa wanda suka rine sukayi ja saboda tashin hankalinda yake ciki yakali gawan bayiwanda aka kasha a daren jiya, a yashe a gabansa an lulubeta da farar kyanle wanda jinni duk yabata wanan kyanlen gakuma sauran bayin wadanda suke daki daya da ita kowace hankalinta a tashe dukaninsu a durdurkushe
cikin razanar dasu dansuji tsoro sufadin gaskiya daya daga jikin dogari guda daya yace dasu kuntabata bakusan lokacinda tafita daga dakinba
.dasauri dukansu suka hada bakin wajen cewa a a a a wlh bamu saniba saboda lkc dukaninmu munyi nesa acikin bacci
. A hankali sarki yace akaisu a rufesu tukuna har sai an gano gaskiyar lamarin ama banda horo a kuma tabatar da ana basu abincci akai akai. Angama ranka shi dade
.nan aka kwashesu sai gidan kulle
.. niko nace allah sarki bayin allah basujiba basu ganiba
DAJIN MAMBILA
[11/23, 1:49 PM] +234 916 056 1643: https://chat.whatsapp.com/IODG6CVfyVb9m3vQrw0vq6
YANBIYUN MACIZAI
The Twins Snake
By
MIHZ. BAREEMAH
Daga alkalamin
mihz bareemah
Dedicated to essential group members thank you for the support you people give to me
FREE PAGE 4
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
Chapter 2 · 0% Book details