← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 12

Sashe 8

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kicin kicin Jiddah tayi da rai "ke wace babyn Figgo? To wallahi bazanje ba ke kije dama kece acici"

Ta k'arasa magana tana wani daga bombom sama sannan ta fice daga class din.

"Abdallah wai kai kuwa lafiyar ka kuwa? Kana fama da olcer sannan kace kullum sai kayi azumi? Wlh tun wuri ka samawa kanka lafiya"

Sarai ya gane abinda Ummi take nufi amma shi dai a nasa lissafin azumin shine samun lafiyarsa da kuma maslaha agare shi.

"Wai ni yanzu da nake wannan jiran gawan shanun shin wai Jiddah zata karbeni a matsayin miji? kuma abokin rayuwar ta? Kuma zata soni kamar yadda nake son ta?"... ......

Duk wannan tambayoyin da bashida amsar su yayima kanshi kafin daga bisani karar wayan shi ya katse shi.........

Khairaty ✍🏻
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*Yaa Sheikh*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*U. K. Y. for real*😘

*Dedicated to Mmn khairy*🤝🏻

*65to70*

Wayar tashi ya d'auka sunan da ya gani ne yasa shi dai daita nutsuwar shi, school authorities ya kane rubuce kan Wayar tashi don haka baiyi wata wata ba ya d'auka.......

Cikin gaggawa ake neman yaa Sheikh yaje Madina saboda za ayi musu exam wanda daga wannan exam d'inne idan mutun yaci za'a bashi ayki da acormadation, (muhalli) da kuma yarjejeniyar albashin da za ake bawa mutun idan ya amin ce.

Bayan ya sha ruwa ne suna zaune da su ummy da Abdul majid kasancewar sun dawo yake shaidawa Umme abunda yake faruwa....

Ba karamin dad'i Umme taji ba dajin wannan labarin saboda ko ba kamai tasan zasu huta idan Abdallah ya samu aykin nan saboda Abdallah akwai taimako da kuma tausayi ita dai fatan ta Allah yasa su dace ya samu yaci exam din.

"To Abdallah yanzu tafita kama ka keban? "

"Wlhy kuwa Ummy nah"

"To Allah yasa adace saika kira Abii ka fad'amai, zuwa yaushe ne to suke bukatar kuje?"

Ta karashe zancen nata da tambayar shi.

"Ummy sati biyu ne"

"Ok to Allah ya taima ka"

"Amin"

"Ku... tunda kuma dawo ma kuwa kunyi muraja'a? Ko kuma tun da kun zama yan boko shikenan kunyi bye bye da islamiyya?"

Abdul malik ne ya danyi k'arfin halin magana yana sosa k'eya"aa yaya wlh ni inayi saidai ko Abdul majid"
Da sauri Abdul majid ya katse shi "kai Karfa ka had'ani da ya Abdallah wlh yaya nima inayi, yanzu ay girma yazo munsan dad'in abun, idan da badon Allah yasa munada na addinin ba ay da bamu kai haka a A. B. U ba tuni zasu bugo mu.

Murmushi yaa Sheikh yayi yana cewa "gara da kuka gane hakan ay"

Sun d'an taba hira kad'an kafin daga bisani Yaa Sheikh yayi musu sallahma zai wuce masallaci sallan isha daganan kuma zai tsaya Saboda akwai matasan da yake wa karatu bayan sallan ishan don haka yace wa ummy saida safe sukuma su Abdallah ya jamusu kunne karsu makara a jam'i.

"wayyo Allah na Nana wlh da gaske k'asan cikina ciwo yake min"

"Ke dalla nace miki marar kice take ciwo bawai k'asan ciki ba"

"To naji mara ta tana min ciwo"

Wata uwar shewa Nana tayi ta d'ora da gud'a "ayiiriiriiii su Jiddah za'a balaga a balallage "

"Kinga bana son iskanci fa Nana wannan wani irin magana ne kike? Ni banason iskanci"

"A'a kinga ikon Allah Jiddah kefa kikace kina ciwon mara kuma ciwon mara ay na mai period ne ita kuma mai period ay baliga ce "

Wata uwar harara Jiddah ta watsawa Nana "ke kika san wannan kinga tafiya ta"

Ta mik'e tana tafiya amma kirjin nan a sama

"Babyn figo maida k'irjin mana, idan kika koma gida kina irin wannan tafiyar ay sai mai jallabiya ya cinye ki d'anya da wannan shegen kallon da yake miki"

Ko juyowa Jiddah batai ba bare ta bata amsa....

Yau saura kwana uku yaa Sheikh yatafi kuma gobe ya yanke shawaran dubo Jiddah don bazai iya tafiya bai ganta ba, acewar shi wai idan ya tafi bai ganta ba bazai iya tab'uka komai ba don haka gara yaje yaga beby love d'inshi.

Fita yayi yayowa Jiddah shopping kaca-kaca na yan makaranta sannan yaje ya gayawa Ummy ko tana da sak'o gurin Jiddah idan tana dashi to ya zama cikin shiri don gobe zaije dubota sannan yaje ya gayawa Mamy ma.

Ita dai Ummy bata so wannan zuwan da zaiwa Jiddah ba saboda tana tsoron kar yaje ya gano abinda zai sa ya kasa yin abun arzik'i a exam din nashi.

Hhhhhhh tofa wannan shine kowa da nashi tunanin. Waye mai gaskiya Ummy ko Yaa Sheikh? 🤔🤔🤔

Thank you Yaa Sheikh fans aylobiyu furnai furnai😂🤣😂😘

Khairaty ✍🏻😍❣
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Yaa Sheikh*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*ina godiya masoyana aringa hakuri da spelling mistakes please 😍*_

*U. K. Y. For real*😍

*Dedicated to Mmn khairy*🤝🏻

*70to75*

Tsaye yake gaban mirror Yana feshe jikin shi da turare kamshi kawai ke tashi akowace kusurwa na d'akin kamar anyi b'arin turare.

Sanye yake cikin wata gezna( shadda) light blue tayi matuk'ar amsarshi abunka da farin fata, dark blue din takarmi sauciki yasa da agogo da hula duk dark blue ne yayi kyau sosai.

Cikin Sauri yake komai don k'arfe 3:00 na rana kuma yana so duk inda 4:00 yake ya zama yana kusa da Jiddah.

Abdul majid ne ya shigo d'akin yana cewa "Yaya na gama wanke motan Abii din, yaya wai Abii din dawowa zaiyi ne? "

Ko kallon sa Yaa Sheikh baiyi ba ya bashi amsa da "a'a ni zan fita da ita, sannan idan ka gama surutun naka ka d'auki wad'ancen ladojin ka samin a boat "

Ya k'arasa maganar yana nufar cikin gida ya sami Ummy ya shaida mata ya gama shiryawa zai tafi.

"Hmmm Abdallah kenan yanzu duk wannan shirin na Jiddah ne?"

Shidai Yaa Sheikh sosa kai kawai yayi yana murmushi baice komai ba.

"To Allah ya kiyaye, sannan ga kantu nan na soya mata ka kaimata kasan mutuniyar taka a wajen kwad'ayi tafi kauri"

karb'ar kantun yayi yana murmushi yana sak'a abubuwa iri-iri a ransa.

"To Ummy ta gode bari naje gurin Mamy dagacen zan wuce"

Itama Mamy duk kayan kwad'ayi ta had'a mata takuma bada sak'on a gaishe mata da ita.

***********

"Don Allah Nana kiyi sauri ki gama inada assignment ke kuma kin tsaya iyayi"

"kai ni karki cinyeni, mu tafi".

Jiddah Sanye take cikin doguwar riga ta morris blue ta matseta ta sama ta kasa kuma ta bud'e ga yanmatanci ya fara bayyana, wani d'an k'aramin farin hijab ne iya wuya, ba wani kwalliya taiba amma tayi matuk'ar yin kyau.

4:00 acikin school d'in su Jiddah tayiwa Yaa Sheikh , bai tsaya ko ina ba sai admin block yabi duk wani procedure da visitors suke bi don haka aka tura messeger ya kira Jiddah Usman.

Yaa Sheikh komawa yayi cikin moto yana jira yaga ta ina Jiddah zata b'ullo sai wani gyara zaman hula yake yana daidaita kafad'a😂lol.

Sanda Jiddah taji wai anzo mata tasan ba kowa bane illa Yah Abdallahn ta don haka ko takan Nana bata biba ta nufi inda visitors ke tsayawa,... ay kowa tana zuwa ta hango moto din Abii an faka ta can k'asan wata bishya aykuwa su Jiddah harda wani sake gyara tafiya irin Yaa Sheikh yasan fa tazo boarding school ta Kara wayewa.

Tacikin mirror ya hangota tana takowa ko'ina na jikin ta yana motsawa tamkar cikakkiyar budurwa.

" Yaaa salam.... What? It's Jiddah? I can't believe it "

Kafin ya gama mamakin nasa har ta k'araso dai-dai saitin Window d'in mai zaman banza, itama Allah Allah take taga shin Yah Abdallahn ne kokuwa.

Ido biyu sukai da Yaa Sheikh wanda ya kafeta da ido ko k'iftawa ya kasa yanajin wani abu na bin jikinshi kamar kiyashi yaa Sheikh bai k'ara shiga wani haliba sai da yaga Jiddah na wani irin tsallen murna gami da shagwa'ba,

"Laah aykuwa shine wayyo dad'i"

Sa hannu tayi ta bud'e kofar tun kafin yayi mata izini, ta fad'a cikin moto din batare da ta kalli halin da Yaa Sheikh yake ciki ba ta kaimai wani wawan hug, suman zaune yayi lokaci d'aya kuma numfashin shi yana kokarin d'aukewa.

"Kai amma naji dad'i yaya Abdallah nah yasu ummy? "

Duk tana rungume dashi take jera mai wannan tambayar.

Da kyar ya iya zame jikin shi daga nata sannan yace "Jiddah duk wannan murnan na ganina ne? to ki tsaya mu gaisa mana"da kyar ya ke maganar kamar zai shid'e.

"Ok Yah Abdallah nah ya kake? "

"Lafiya klau Jiddah ya karatu? "

"Lafiya lau yaya"

"Ummy da Mamy suna gaisheki"

"Ina amsawa, Allah sarki Ummy nah, me tabaka ka kawomin? "

"Abun dad'i"

"Yeee! To nagode yaya"

Shidai Yaa Sheikh kawai kallon Jiddah yake a ranshi kuma yana mamakin yadda akai ta canza gaba d'aya kamar ba ita ba. D'an saisaita kanshi tayi ya wayance da cewa

"To yanzu dai ki bani labari kafin lokaci ya kure minti goma suka bani na ganki"

"Ok tom kasan me Yah Abdallah?"

"Aa Jiddah saikin fad'a"

Shagwa'be fuska tai kamar zatai kuka sannan ta fara magana "kaga ranan nan ne naita ciwon k'asan ciki naita kuka"ta k'arasa maganar tana shigewa jikin shi.

Bubbuga bayanta yashiga yi yana bata hak'uri.
"Meyasa to bakije clinic ba?"

"Naje sun bani magani amma bai daina ba"

"har yanzu? " ya tambayeta

"Aa banda yanzu"

"To idan ya kuma kiyi addua zai daina amma karki kuma yin kuka, ko kinaso nima nayi? "

Mak'e kafad'a tayi sannan tace "banaso"

"Yawwa Jiddah good girl, kinsan me nakeso dake? "
"A'a "

"So nake Kimin addua jibi zan koma madina zamuyi exam, sannan Kimin alkawari zaki ringa karatu sosai"

Ya kafeta da ido yana sauraron amsar ta, itama shi take kallo idon ta cike da kwalla.

"Yah Abdallah tafiya zakayi, idan katafi sai Yaushe? "

"Ohh no! Don't cry my jiddo ba dad'ewa zanyi bafa kafin ki dawo ma Insha Allah na dawo Kedai Kimin addua"

Yana maganar ne yana goge mata hawaye.

"Nayima alkawari zan ringa karatu sosai sannan zanyima addua Allah ya bada sa'a"

"Amin jiddo nah, kinga har kocacin ya cika ki tafi class idan kun kama evening prep saiki je ki karbi sak'onki "
Chapter 8 · 0% Book details