← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 12

Sashe 3

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta koma Borno ita da yaran ta, da al'kawarin duk sanda ta samu lokaci zata Ke kawo musu ziyara, tana kuka haka suka rabu tana kewar mijin ta,tana mai addu'ar Allah ya ji'kan mijin ta.

Bayan tadawo Borno ne ta koma family house d'in su kasan cewar ita din ma marainiya ce haka dai take zaune gidan, yau da dad'i gobe babu,mutun d'aya ne take gani taji dad'i wato 'kanin ta Abdallah shine ya ke 'kwantar mata da hankali.

gidan daga daga 'kannan baban ta Sai matan su hakadai take zaune, saboda babban burinta bai wuce taga yaranta sun sami ilimin addini da na boko ba.

Alhamdulillahi burin hajiya laila yana cika, ta tsaya tsayin daka wajan ganin yaranta sun samu ilimi, don kuwa sun sauke al kur'ani,kasan cewar su yara masu haza'ka, inda Gaddafi yake aji shida a primary shi kuma Usman yana aji biyar, yanzu kuma abunda yake damunta bai wuce rashin auren 'kanin na taba wato Abdallah.

To kana taka Allah na tashi 'kwatsam Sai ciwan ajali ya riski Hajiya Laila,tace ga garin Ku Abdalla 'kaninta yayi kuka haka su Gaddafi shida Usman.

Dan haka Abdallah ba shiri ya fara Neman aure saboda yasan wahala su Gaddafi zasu sha idan ya barsu a family house d'in nasu, ammafa ranshi ba dad'i yaso yayar tashi taga auran nashi.

Ba'a d'au lokaci ba yasamu yarinya Yar manyan mutane,mai tarbiyya itama shuwa ce , mai suna khadija ,bayan sun dai daita ne aka yi aure.

Bayan auran da wata biyu ya d'auko Gaddafi da Usman suka dawo gabansa inda yaci gaba da d'aukar d'awainiyar su na makaranta da kuma tarbiyyar su, kuma itama Khadija bata da matsala tana kula dasu tsakani da Allah.

Bayan wani lokaci itama Khadija wadda ayanzu su Gaddafi suke kira da hajiya kamar yadda suke kiran Hajiyarsu kafin ta rasu, ta haihu ta samu 'yarta mace kyakkyawa da ita,inda taci sunan Hajiya wato Laila.

Haka suka cigaba da zama cikin so da 'kaunar juna, su Gaddafi suna son Laila shiyasa ma itama Khadija keson su.

Kwance tashi ba wuya don Gaddafi da Usman sun gama karatun su,itama Laila ta girma tana secondary.

Gaddafi da Usman sun fara kasuwanci suna saro kaya a kano suna kawowa Borno kuma ba laifi Suna samun alheri, da hakane har suka sami uban gida.

Kasuwanci su ya bunk'asa inda suka daina kawo kaya Borno Sai dai su siyar a kano, idan suka zo kano basa komawa Baron Sai 'karshen sati.

A hakane har Allah ya ha'da Gaddafi da Aysha wato ummee, Gaddafi yazo ya sami baffan sa Abdallah da batun aure, baffa Abdallah yaji dad'i yakuma bashi shawaran ya Gina gida a can kano saboda yawo a moton yayi yawa gara su zauna guri d'aya.

Haka kuwa akayi, gadan gadan suka fara gini a kano a unguwar gandun albasa, gida biyu suka gina, d'aya na Gaddafi d'aya na Usman duk da dai shi ba auran ne a gabansa ba.

Aka daura auran Gaddafi da Aysha duk lokacin da suka samu dama kuma suna zuwa Borno.

haka har Aysha ta haihu ta sami namiji aykuwa Gaddafi yasa ma yaro sunan baffan sa Abdallah, yaro kyakkyawa dashi ga shiga rai, Sai yafito sak kyawawan Sudan d'innan hanci har baka, baffah Abdallah yaji dad'i matu'ka,awannan lokacine kuma baffa ya takurawa Usman sai ya fito da mata, da Usman yaji baffan nashi ya matsa masa ne yafito ya fad'a mai gaskiya shifa Laila yakeso, ay kuwa wannan abu ya yiwa baffa dad'i' haka hajiya ma don tasan Usman zai ri'ke mata tilon 'Yarta ta don daga kan Lailan bata kuma haihuwa ba.

Ba 'bata lokaci akayi aure aka kawo wa Usman amaryarsa Laila.

Aysha taji dad'i sosai saboda acewarta ta samu 'Yar uwa, ayko tasamu d'in don Laila bata da matsala kullum Abdallah yana hannunta saboda mai sunan baban tane kuma gashi kyakkyawa.

Bayan Abdallah yayi shekara Tara ne aka yi mai 'kani Abdul majid, Abdallah yanazuwa makaranta kuma yana da ko kari, yana da shekara Taran ne ya haddace alkur'ani .

Itadai lailah shuru Allah bai kawo haihuwaba amma itada Usman sunata addu'a suma Allah ya basu.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Aysha wato Ummee ta kuma haihuwa shima na miji aka samai suna Abdul malik.

Bayan wasu 'yan lokaci Allah ya amshi addu'ar Usman da Laila inda su ma Allah ya basu 'yarsu mace Inda taci suna Jidda yarinya kyakkywa son kowa 'kin Wanda ya rasa fara tas da ita kana ganinta kaga jinin Shuwa ga kyau ga gashi.

Jidda tana da shekara uku Allah ya yiwa Usman rasuwa, kai wannan rasuwa ta gigita su musamnan Laila wato mamy da kuma Abii,haka shima baffa da hajiya ,Abdallah shima yaji mutuwarnan sosai ita kuwa Jidda bata da wayo don haka bata San ma me a keyi bama.

Bayan Mamy ta gama takaba baffa yace "ta koma gida" amma Sam Abii yaki Yar da a cewarsa ay ko ba matar Usman bace ita ba ay ita k'anwar sa ce shi mai iya rike tane kuma Dama tana 'Yar sana'ar ta gashi sun saba kawai ta zauna idan Allah ya fito mata da miji tai auran ta, haka baffa ya ha'kura ya kyale ta.

*Cigaban Labari*
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*YAA SHEIKH*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U.K.Y. for real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to mmn khaery*🤝🏻

2⃣0⃣to2⃣5⃣

Haka suka 'karasa makaranta Yana d'auke da ita a kafa'da, ya kai ta har cikin makarantar tasu sannan yace,

"Saura kuma idan antashi ki tsaya a hanya kina wasa"

"Nima bazan tsaya wasa ba ay yau Abii zai dawo zai kawo mana kayan dadi ko?"

Yace mata "eh kiyi karatu da yawa"

Ya juya ya fice daka makarantar.

Bai tsaya ko inaba sai gidansu Bilal.

Bilal abokin Yaa Sheikh ne tun suna yara haka kuma tare suke karatu saida su kazo university ne Yaa Sheikh ya tafi sokoto shi kuma Bilal Yana kano, shima Bilal yanzu haka bai samu ayki ba kuma shima malami ne a Sahsib islamiyya.

Yaa sheikh Yana zuwa ya tarar da Bilal a 'kofar gida Yana duba wani littafi, ya 'karasa shima ya zauna sannan suka yi musabaha fuskar Bilal dauke da murmushi, amma fa ta Yaa Sheikh cike take da damuwa kuma Bilal ya fahinci hakan sai dai baiyi magana ba, don yasan ko yayi ma ba lallai ne ya gaya mai abin da yake damun shi ba saboda Yaa Sheikh mutum ne mai zurfin ciki.

Zama Yaa Sheikh yayi suka cigaba da duba littafin suna muhawara irin ta masu imilin addini a tsakanin su,daga bisani suka koma hirar su ta abokai, anan ne Bilal ya takura akan lallai sai Yaa Sheikh ya fad'a masa abun da yake damun sa.

Yaa Sheikh ya d'ago fuskan shi d'auke da damuwa yace,

"Bilal"

Sai da Bilal ya d'ago ya kalle shi zuwa lokacin fuskan shi har ya sauya kala, kana iya karanta damuwar da Ke d'auke a fuskar tashi.

Yace "Jiddah itace damuwa ta Bilal, bani da wata damuwa da ya wuce Jidda"

Bilal ya sake kallon abokin nashi kuma Yana mamakin abin da yake cewa, taya zai ce wai Jidda ce damuwar shi, Jidda karamar yarinya? to kodai wani Abune ya sami Jiddan ?

Duk Bilal ne ya kewa kanshi wannan tambayar sai dai yasan Yaa Sheikh ne zai iya bashi amsa, don haka yace,

"Abdallah me yasami Jiddan kodai ba Jiddan Ku kake nufi ba?"

"Ita nake nufi Bilal, Jidda yarinya CE karama sai dai ina jin wani babban al amari game da ita, kuma nima na kasa tantance mai hakan yake nufi,idan naga Jidda nakan rasa hankali na, ina shiga wani yanayi aduk lokacin da nake tare da ita, ni mutum ne mai son shagwab'a ita kuma Jidda ba abun da ya zame mata jiki kamar shagwab'a,Bilal akwai abubuwa da dama da nake ji game da Jidda, kuma banaso Ummee ta fuskanci halin da nake ciki".

Ya d'ora da cewa " nidai nasan ba wata mace da nake jin hakan game da ita, hasali ma ni mata basa gaba na, why sai Jidda? Why?"

"Allah kaga zuciya ta, Allah kayi al'kawarin baza ka jarabci bawan ka da abin da yafi 'karfin shi ba ya Allah ina rokon ka da ka dubeni da idon rahma"

Bilal da yai kasa'ke yana kallon abokin nasa da tausayin sa da ya cika mai zuciya kuma yana mai mamakin wannan lamari, saboda yasan abokin nasa ba mai damuwa da mata bane hasalima ko mace ce tace tana sonsa to daga ranar tsana ta shiga tsakanin sa da wadda tace tana son nasa.

Bilal ya nisa yace "Abdallah kar kasa damuwa a ranka kacigaba da addu'a nima zan tayaka,sai dai ina tunanin kawai fa son Jidda kake"

"Nima ina zargin hakan, amma ay Jidda ba tsara ta bace taya zan fara son ta? Yarinyar da ko kanta bata sani ba, ya Allah gani gare ka"

"Kardai kasa damuwa a ran ka komai zai zo dasau'ki da yardar Allah kai dai kayi addu'a, kuma da kake cewa baka son Ummee tasan halin da kake ciki idan bata sani ba waye kake dashi da zai tayaka addu'a? kadai San addu'ar iyaye akan 'ya'yansu daurewa zakai ka fad'mata"

"Hakane amma gaskiya Bilal ko zan gayawa Ummee ba yanzu ba zan dai cigaba da daddu'ar"

Bilal yace "to shikenan nima zan tayaka "

Yaa Sheikh ya mika wa Bilal hannu suka yi musabaha yace "to bari na k'arasa gida yau Abii zai dawo sai mun had'u a islamiyya"

"OK to shikenan nima zan shigo nayiwa Abii sannun da zuwa"

Haka suka rabu Bilal yana tausayawa abokin sa, shima Yaa Sheikh yana tausayawa kan sa.

Yana shiga gida ya tarar da Ummee ta gyara gida ko ina fes fes itama tayi wankan ta tana jiran shigowar mai gidan ta.

Ya shiga yana murmushi yana yaba yadda Ummeen shi keda kokari tana da tsafta ga son ado, ya k'arasa kusa da ita yana mata sannun da gida tace,
"Yawwa sannu Abdallah, kakai min yarinyar tawa ko, amma dai ka tsaya wani gun don ka dad'e?"

Ta jera mishi tambayar.

"Eh Ummena natsaya a gurinbBilal ne"

Ta sake cewa " 'Yar tawa kuma fa?"

"Na kai ta"
Chapter 3 · 0% Book details