← Book details Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 12

Sashe 4

Yaa Sheikh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya bata amsa a ta'kaice don baya so Ummee ta gano wani Abu, saboda shi ko maganan jiddan tana sa shi tuna nin ta.

Tsayu war mota a 'kofar gidan sune ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, Umme tace

"Abdallah wannan kamar Abii ko?"

"Bari na duba "

Ay kuwa shi ne, Abdallah ya 'karasa wajen baban nashi yana cewa,
"Abii sannun da zuwa ka sha hanya"

"Wallahi kuma babana shiga da wannan sauran kuma ka barsu a but din idan su Abdul majid sun dawo saisu shigarwa Mamy"

(Shima Mamyn yake CE mata tunda dai sunan mahaifiyar sa gare ta.)

Abdallah yace "toh Abii" yana mai daukan kayan da Abii din ya nuna masa.

Ummee da murna ta tari mijin ta,Abdallah ya kuma gaushe da Abii, ya tashi yana cewa "Umme bari na Dan watsa ruwa na kwanta kafin azahar"

"To Abdallah"
Itama ta fad'a tana kokarin tashiga d'akin Abii ta ha'da mai ruwan wanka "

Karfe 12:15 Jidda tashigo tana murna don taga Motan Abii a kofar gida tana cewa,

"yeee Abii ya dawo"

tai hanyar dakin Abii da gudu ta fad'a dakin, aiko tana ganin sa ta fad'a jikin sa, shima da murna yace

" 'Yar gidan Abii kin dawo, ya makaranta kina dai karatun ko, ko kina nan kina kukan ki na banza?"

Ya jera mata tambaya saboda ya San mai hali baya fasa halinsa.

"Abii banayi kuma ina karatu,Abii ka kawo min tsaraba"?

" na kawo miki Jidda na idan bankawo miki ba Wa zan kawowa?"

Aiko ta washe baki tace "yawwa Abii na, na gode, sai anjima zaka bani?"

"Eh zan bawa Umme ta ajiye miki yanzu kije ki gaishe da Mamy kuma kice nima Ina gaishe ta,

" Abii to ina Umme?"

Yace"tana d'akin ta"

"To idan ta zo kace na dawo kuma kabata tsaraba ta' ta ajeye min"

Tana gama fad'a tafice da niyyar zuwa wajan Mamyn ta, sai dai tana zuwa wajen 'kofar d'akin Yaa sheikh ta shige d'akin, tana shiga ta ganshi yana bacci, yayi d'ai'dai ya kunna fankar 'kasa tana ta hurashi.
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*YAA SHEIKH*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*BY:U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to Mmn kheiry*

_masoya na bansan irin godiyar da zan muku ba wlh nima Ina sonku na gode da kula warku kuma wadanda sukai min adduar samun nasara a exam dina to alhamdulillahi nasamu nagode sosai da sosai_

*my ANFA ilobiyu Lodi Lodi wooo*😅😘

*25 to30*

Jiddah Tana shiga d'akin tai wajen madubi turarukan shi ta fara feshe jikin ta dasu

"Ay wallahi sai na fesa kowanne nima naita kamshi kamar Ya Abdallah na"

Nan dai taita fasawa sannan ta koma yimai bincike ta hargitsa komai zuwa wannan lokacin ta gaji tulus dama ta gamo rashin jinta a makaran, gefen shi ta kwanta itama sai bacci,

Wani abu yaji ajikin shi kamar ruwa ruwa sannan yaji kamar wani yazo ya kwanta abayan shi,

ay kuwa da sauri yafarka juyawar da zaiyi yaga Jiddah kwance cikin fitsari sharkaf tai musu don shima ajiken yake kawai kallon ta yake yama rasa mezai ce,

ita kuwa sharar baccin ta take ko ajikin ta, tsaki yayi kawai ya yunkura zai tashi kenan ay kuwa baiyi aune ba kawai yaji Jiddah ta cafko shi tana magagin bacci,

wata galabai tacciyar 'Kara ya saki yana kiran

"ya ilahi"

Ya jima kafin ya tattaro karfinsa,

janye hannun ta yayi daga jikin nashi yana tunanin wai yaushe ma ta shigo d'akin nashi har ta kwanta kusa dashi?

sai alokacin yaga iri ayka aykan da taimasa gaba d'aya ta hargitsa d'akin, juyawa yayi yasake kallon ta tananan tana sharar baccin ta wani 'kaya taccen murmushi ne ya kubucemai ya furta

*"inda rai da rabo"*

ko me ya tuna oho,

sannan ya tashi ya sake wasu kayan ya fita daga dakin,

Yana fita ya tarar da Ummyn su tana alwala

"Yanzu nake cewa Abdul malik yazo ya tasoka kafin karasa jam'i"

"Wlh na tashi Ummy wannan yarinyar taki ce wai ta rasa inda zata kwanta sai d'aki na kawai sai farkawa nayi nagan ta, gashi tamin fitsarin kwance"

Dagowa Ummy tai tana tambayar sa "fitsari dai, akan katifar kuma? "

"A wlh Ummy" yafada fiskan shi cike da takaici shi sai yanzu ma abin yake batamai rai,
"To ay shikenan Kayi alwala kar ashiga sallan"

"To Ummy na, Abii fa ko ya tafi masalkacin?"

"Eh " Ummy ta fada tana shiga dakin ta shima ya sheikh alwala yayi ya tafi masallaci ko takan Jiddah bai biba,

Ita kuwa Jiddah ya sheikh yana fita ta farka ganin abin da taine kunya ta hanata fita saboda tasan indai su Abdul majid sunji abinda tai tashiga uku,

tanajin fitarsu masallaci tai maza ta sulale tai gidan mamyn ta, tana shiga ta tarar mamy ta tada sallah, tasamu guri tarakube tana jiran mamyn ta idar,

Mamy tana idarwa Bayan tayi addua ta kalli Jiddah dasai muzurai take tace "meya jika miki kaya? "

"Fitsarin kwance nayi"
Tabata amsa tana dukar da kai,

"Fitsarin kwance Jiddah a Ina kikai? "

"A dakin ya Abdallah "

Mamy ta sake jefa mata tambaya "a kasa ko a Ina? "

"A katifa"

Tafada tana turo baki na borin kunya.

*5 years*

Kuyi hakuri da wannan fans ba yawa😍😍😍
[21/04, 10:00 a.m.] Shooly: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*YAA SHEIKH*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*U. K. Y. For real*😘

🌈 *kainuwa writers asso*✍🏻

*Dedicated to mmn kheiry*

*30to35*

*5 years*

Shekaru biyar da suka shud'e abubuwa da dama sun faru, ansamu nasarori da dama.

A halin yanzu Jiddah ta gama primary school sannan ana cuku-cukun sama mata secondary.

Jiddah idan kagan ta a wannan lokacin bazakace yarinya Yar shekara goma sha biyu bace, Jiddah doguwa ce fara siririya Mai cikakken diri da kyawun zati, wani abun burgewa game da Jiddah shine Jiddah irin yarannan ne masu shegen iyayi ga tsafta ga son iyawa a 'bangaren karatu Jiddah nada kaifin 'kwa'kwalwa afannin Arabic da kuma boko idan Jiddah Tana magana Sai kayi mamaki saboda tsabar iyayi kai a ta'kaice Jiddah tana da d'aukar hankali.

A 'bangaran Yaa Sheikh kuwa a halin yanzu Yaa Sheikh cikakken mutum ne kyakkyawa, to dama abinka da jinin sudanawa dole Ya Sheikh ya kasance Mai jan Hankali,

Ya Sheikh yanada sura Mai d'aukar hankali ga nutsuwa abinka da malaman sunna ba hayaniya.

Shekaru biyar da suka wakana Ya Sheikh ya samu scholarship na zuwa 'kasar Madina, sakamakon musaba'ka da akayi ta 'kasa ba'ki d'aya inda ya samu nasarar lashe gasar kowa yayi farin ciki da hakan,

Ya tafi k'asar Madina inda ya cigaba da karatun masters d'in shi ahalin yanzu ya kammala.

Sai dai sun nuna buk'atar su akan Ya Sheikh da ya zauna don yayi musu Ayki a kasar tasu wato Madina koda ba
na din din din ba kuma Yaa Sheikh ya amince da bukatar su, Sai dai ya basu nashi uzirin cewa yanason zuwa gida nawani d'an lokaci sannan yadawo ya kar'bi aikin, suma kuma sun amin ce.

Babban burin Ya Sheikh yanzu bai wuce yaje yaga abin k'aunar saba kuma sanyin idaniyar sa wato Jiddah, don ba abinda ya sauya game da abin da Ya Sheikh ya keji akan Jiddah, don daga Ummy har Mamy sun gane Ya Sheikh yana tsananin 'kaunar Jiddah, Sai dai ita Jiddah bata sani ba.

Ummy tasha yiwa Ya Sheikh magana akan ya nemar wa kanshi mafita ya samu wata cikakkiyar budurwa ya aura don ya yiwa Jiddah girma, Jiddah baza ta iya dashi ba amma kullum tazo Mai da zancen Sai ya hau yi mata magiya don Allah Ummy na kibar wannan maganar kafin Jiddah taji itama tace nayi mata girman.

Ummy dai jinshi kawai take kuma tana mamakin yadda Abdallan nata yake mugun son Jiddah wanda ta lura ko gurin da yake Jiddah tazo Sai yanayin sa ya canja, to inaga an kaimai ita gidan sa a matsayin mata.

Mamy har yanzu Allah bai kawo mata miji ba tana zaune dai tana 'yan sana'oin ta kuma rashin auran bai dame ta ba saboda ba abunda tarasa yadda Ya Sheikh zai yima Ummyn shi ayke haka yake yiwa Mamy ma sannan Abii ma duk abunda ya kawo Sai an kai mata, tana zaune cikin kwanciyar hankali,
Sannan koda ta gane ala'kar Ya Sheikh da Jiddah abun ya mata dadi sosai, sai dai Tana tunanin Anya Jiddah tana son Abdallah kuwa?

Abdul Malik da Abdul Majid suna Sokoto suna karatunsu na degree wanda shima Ya Sheikh ne ya dauki nauyin Kara tun nasu.

Kai Sai dai muce Alhamdulilah amma dai kam an samu ci gaba.

"Nidai Mamy Allah boding nakeso kinga Nana ma can za a kaita ba Sai akaimu tare ba? "

"Oh wato ita Nanan ce ta cemiki boding za a kaita shine zakizo ki sani a gaba ko? To ni kifita a idona na rufe kina jina ko tun wuri ki cire zancen boding d'innan ma a ranki Jiddah kinsan Abii ba yarda zaiyi ba."

Jiddah bata sake cewa komai ba saboda tasan Ya Sheikh ya kusa dawowa kuma tasan zai yarda kuma yana yarda shi kenan,

"To shikenan Mamy bari naje na gaishe da Ummy Da Abii kafin ya fita."

Mamy tace "toh ki ce ina gaishe da Abii kuma kicewa Ummyn taku nima Zan shigo anjima."

Tana fita tafad'a gidan Ummyn bayan ta gaishe su tai sauri tafita tana cewa "Ummy na tafi..... na baro Mamy tana Ayki "

"To Jiddah na kice mata Sai ta shigo din"

Jiddah tana fita tai gidan su Nana aminiyar ta,
Nana tana ganin ta ta hau murna don a tunanin ta Jiddah tazo gaya mata an yarda itama za akaita boding d'in.

"Ke Mamyn ta yarda ko? "
Nana ta tambaye ta

"Wlh bata yarda ba Nana amma dai kinga Ya Sheikh ya kusa dawowa idan ya yarda shikenan."

"Ya Sheikh ubanki ne shi da zakice Sai ya yarda? "

Wani mugun kallo Jiddah watsawa Nana kana tace "idan shi ba ubana bane ai yaya nane shi ko kuma idan bai yarda ba uban wane zai biya kud'in makarantar? Ko babanku zai biya min?" ta k'arasa maganar tanawa Nana kallon up and down

"Kefa baki da M wlh yanzu me ne nasako Baban mu a ciki? "
Chapter 4 · 0% Book details